Jirigin sama-jannatin Turkiyya wanda ke dauke da wadanda zsu je aikin Axiom Mission 3 (Ax-3), daga ciki har da dan Turkiyya na farko da ya fara zuwa sararin samaniya wato Alper Gezeravci, sun isa Tashar Sararin Samaniya ta duniya.
Sun sauka a tashar da misalin karfe 1042 agogon GMT, wato 1342 agogon Turkiyya a ranar Asabar, kusan sa'o'i 37 bayan da suka bar tashar tafiya sararin samaniya ta Kennedy Space Center da ke Florida a Amurka a ranar 18 ga watan Janairu.
A halin yanzu 'yan sama-jannatin za su tafi kai tsaye su soma aiki, inda za su yi ayyukan da kasarsu ta tura su na binciken kimiyya. Gezeravci zai gudanar da binciken kimiyya 13 wadanda malaman kimiyya na Turkiyya suka shirya da kuma cibiyoyin bincike.
A wani taron manema labarai kafin jirgin sama-jannatin ya tashi, dan Turkiyyan ya ce zai kai wasu abubuwa na ban mamaki daga Turkiyya zuwa tashar sararin samaniyar a matsayin wata alama karamcin kasar.
Ya kuma tafi da abubuwan tunawa da balaguron tarihi, da suka hada da hotunan iyali, kayayyaki da ke wakiltar al'adunsa na makiyaya na Turkiyya da tutar Turkiyya.