Farfesoshi daga kasashen Turkiyya da Serbia na aiki domin kirkirar wata na’ura da za ta rinka gargadi kan harin nukiliya.
Na’urar dai za ta mayar da hankali ne wurin bayar da tsaro ga iyakokin kasashen NATO.
Tuni dai kungiyar NATO ta yi maraba da wannan aikin wanda Jam’iar Bolu Abant Izzet Baysal ta Turkiyya ta assasa da kuma Jami’ar Serbia ta Nis.
An soma aikin ne watanni uku da suka gabata, kamar yadda Jami’ar Bolu Abant Izzet Baysal ta bayyana.
Ercan Yilmaz, wanda farfesa ne ta bangaren falsafa a jami’ar ta Turkiyya, shi ne ke jagorantar kirkiro bangaren na’urar da ke zaburarwa da zarar wani abu ya kusance ta.
Sai kuma daga bangaren Jami’ar ta Serbia suna aiki ne wajen samar da kwakwalwar tantance bayanai da kuma manhajar da za ta yi daidai da na’urar.
Yilmaz ya shaida wa Anadolu cewa na’urar za ta kasance kamar jirgi mara matuki wanda zai rinka duba iyakoki yadda ya kamata. “Mun fitar da tsarinmu. Mun kuma kammala fitar da samfarinmu.
Za mu kammala samar da bangaren da ke zaburar da na’ura [sensor] nan da watanni takwas. Dayan bangaren kuma sun soma aiki kan batun kayan wuta,” in ji Yilmaz.
“Za a mayar da na’urar jirgi mara matuki. Jirgin zai rinka shawagi kan iyakokin kasashen NATO. Idan akwai wani shirin nukiliya, zai gano shi,” in ji shi.