Dangane da batun Gaza, Fidan ya bayyana cewa sun kuma tattauna kan buƙatar tsagaita wuta a Gaza.  / Hoto: Gaza

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya bayyana cewa, babban abin da Turkiyya ta sa a gaba a Syria shi ne tabbatar da kwanciyar hankali da hana mamayar kungiyoyin da ake ganin 'yan ta'adda ne bayan hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad.

Ya bayyana haka ne a yayin da yake magana tare da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken bayan ganawarsu a Ankara, inda Fidan ya bayyana cewa, rawar da Turkiyya da Amurka ke takawa kan makomar Siriya na daga cikin batutuwan da suka tattauna.

"A sabon halin da ake ciki a Syria, mun tattauna kan abin da za a iya yi don jin dadin al'ummar Siriya, hadin kan kasar, mutunci, hadin kai, da 'yancin kai, mun kuma yi magana game da rawar da Turkiyya, Amurka, da masu ruwa da tsaki na yankin suka taka, da kuma yadda za a yi amfani da su a cikin kasar, da kuma yadda za mu hada kai don magance wadannan matsalolin,” inji shi.

"Mun tattauna kan cewa hana ta'addanci a Syria da kuma tabbatar da cewa Daesh da PKK ba su mamaye wurin ba na daga cikin abubuwan da muka sa a gaba. Mun yi magana sosai game da abin da za mu iya yi game da waɗannan batutuwa, abin da ke damun mu, da kuma waɗanne hanyoyin haɗin gwiwa ya kamata su kasance, ”in ji Fidan.

Dangane da Gaza, Fidan ya bayyana cewa, sun kuma yi magana kan bukatar tsagaita bude wuta a yankin, yana mai cewa, “Mun amince da gaggawar cim ma yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Amurka da Turkiyya tare da sauran kawayenta na aiki tukuru don ganin an tsagaita bude wuta a yankin. Sai dai abin takaic shi ne, ana ci gaba da tashin hankali. Har yanzu Isra'ila na kashe fararen hula. Mun tattauna matakan da za mu bi don dakatar da hakan cikin gaggawa.”

Fidan ya kuma bayyana cewa, a ganawarsa da Blinken, wanda ya kai ziyara Turkiyya a karo na karshe a lokacin mulkinsa, sun tattauna kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, musamman a fannin tsaro.

TRT World