Jami'an na Turkiyya sun kai samamen a sansanonin 'yan ta'addan YPG/PKK. Hoto/AA

Jami’an tattara bayanan sirri na Turkiyya sun “kawar da” ‘yan ta’addan PKK/KCK-PYD/YPG 11 a arewacin Syria, kusa da iyakar Turkiyya, kamar yadda majiyoyin tsaro suka tabbatar.

A ranar Lahadi, Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya (MIT) ta kai samame a yankin Manbij, kamar yadda majiyar wadda ta bukaci a sakaya sunanta ta bayyana.

MIT, wadda ke yawan sa ido kan maboyar ‘yan ta’adda a Manbij, ta gudanar da leken asiri mai kwari inda daga baya ta ci gaba da aiki tare da dakarun Turkiyya.

Ta lalata wani sansani mallakar kungiyoyin ta’addanci na YPG/PKK tare da kawar da ‘yan ta’dda 11, kamar yadda majiyoyin suka tabbatar.

Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai sun ayyana PKK a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda – kuma ta jawo mutuwar sama da mutum 40,000 ciki har da mata da kananan yara.

Kungiyar YPG abokiyar tarayyar PKK ce ta Syria.

AA