Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sanar da sunayen mambobin majalisar zartarwarsa a ranar Asabar, bayan lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 28 ga Mayu, wanda ke nuni da ci-gaba da mulkinsa tare da kafa gwamnati ta 67 a Jamhuriyar Turkiyya.
Mafi yawan manyan mukaman ministocin – harkokin waje da harkokin cikin gida da tsaro da kudi – an bai wa kwararru da ake girmamawa saboda kwarewar da suke da ita a fannoninsu.
Sabon ministan harkokin waje Hakan Fidan, abokin sirrin Erdogan ne da ya jagoranci Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya tun daga 2010, inda ya dinga taka rawa a al’amuran siyasa daban-daban – daga kawar da yunkurin juyin mulkin 16 ga Yuli zuwa yakar ‘yan ta’adda a areeasin Siriya da Iraki.
Fidan wanda aka haifa a Ankara, ya karanta alakar kasa da kasa a jami’a, ya yi aikin soji a Turkiyya a matsayin karamin ma’aikaci a tsakanin 1986 zuwa 2001, kuma an san shi da iliminsa kan tsaron kasa da kasa d siyasar yankin Eurosia.
Mehmet Simsek, tsohon jami’an sha’anin kudi a gwamnatin Erdogan tsakanin 2009-2018, shi ne zai jagoranci ma’aikatar kudi da baitulmali, wadda ke kula da manufofin tattalin arzikin Turkiyya.
A baya ma Simsek ya yi aiki tare da manyan hukumomin kudi na duniya da suka hada da Merrill Lynch.
Sabon ministan harkokin cikin gida shi ne Ali Yerlikaya, tsohon gwamnan Istanbul ne, kuma kwararren ma’aikacin ne.
Ya yi aiki a matakai daban-daban a cikin gida – daga Gaziantep na kudu maso-gabashin Turkiyya da ke iyaka da Siriya, zuwa Tekirdag, garin da ke iyaka da Girka a yammacin Turkiyya, sannan Agri da ke gabashin kasar.
Sauyi da ci-gaba
Baya ga ministan lafiya Fahrettin Koca da na raya al’adu da yawon bude ido Mehmet Nuri Ersoy da za su ci gaba da rike mukamansu, kujerun ministoci 15 daga 17 sun samu sabbin mazauna, kamar yadda aka gani a sanarwar ta ranar Asabar.
Da ma ana tsammanin samun sauyin saboda yadda wasu ministocin suka zama ‘yan majalisar dokoki karkashin jam’iyyar AKP.
Sun hada da: ministan harkokin waje Mevlut Cavusoglu, ministan harkokin cikin gida Suleyman Soylu, Ministan tsaro Hulusi Akar da ministan kudi da baiyulmali Nurettin Nabati.
Jam’iyyar Erdogan da kawancen al’umma ba su tsayar da mutanen da ake sa ran nada wa ministoci takarar majalisar dokoki ba a zaben. Saboda za a bukaci su bar kujerar majalisa sannan su zama ministoci.
A zaben na watan Mayu, babu wani da zai yarda ya yi asarar kujerar majalisa saboda yin murabus.
Amma wannan kunshin majalisar ministoci ba ya nufin Erdogan ya yi kutse kan manufofinsa na cikin gida da waje, in ji Cagri Erhan farfesa kan alakar kasa da kasa a jami’ar Altinbas.
Erhan ya shaida wa TRT Wrold cewa Erdogan ya jagoranci Turkiyya shekara 20 da suka gabata kamar direba.
Duk da a wasu lokutan an samu sauyin manufofi a jagorancinsa saboda sauyawar siyasa, amma kuma manufa mai kyau ta jagoranci ta Erdogan ba ta sauya ba.
Erhan ya ce ”Erdogan ya samar da majalisar ministoci da ta wakilci dukkan kabilun Turkiyya.
Waye Hakan Fidan
Duk da sauye-sauye, manyan masu taka rawa a siyasa irin su Fidan sun dade ba a jin duriyarsu, amma kuma aiyukansu na sauya al’amura, inji Erhan.
Erhan ya kara da cewa “Duk da cewa Fidan ya dade yana rike da mukamin shugaban Leken Siri na Erdogan, yana kuma taka rawa wajen dabbaka manufofin Turkiyya a kasahen waje. A saboda haka ba bako ba ne a ma’aikatar harkokin waje.
Wannan na nufin nada Fidan a matsayin ministan harkokin waje zai samar da cigaba a ayyukan da ake yi.
Shugaban kasar ya nada ministocin da za su dabbaka manufofinsa.
A watan Afrilu, Fidan ya raka Akar zuwa Moscow don ganawa da takwarorinsa na Siriya, Rasha da Iran da manufar samar da tsari na siyasa na hadin gwiwa, da zai fuskanci Tsakiyar Asiya da Afirka.
Fidan da ya yi karatu a jami’ar Maryland, ya kuma yi karatun sama da digirgir a alakar kasa da kasa, kuma a baya ya koyar a jami’o’in Hacettepe da Bilkent.
Erhan ya bayyana cewa zaman sa ministan harkokin wajen Turkiyya na nuni da cigaba mai ma’ana wajen dabbaka manufofin harkokin wajen kasar.
Simsek na nufin babban sauyi
Baya ga manufofin kasashen waje, ana sa ran samun wasu sauye-sauye a fannin tattalin arziki karkashin Simsek.
A ‘yan shekarun nan, hauhawar farashi a Turkiyya ya tashi sosai, kuma Lira na ci gaba da karyewa, dala na tashi.
Bayan nada shi a matsayin ministan baitulmali da kudi a karshen makon nan, Simsek na da ra’ayin rikau da zai iya kawo gyara a tattalin arzikin Turkiyya.
Kafin zaben 2018, Simsek ya yi aiki a gwamnatocin Erdogan a matakai daban-daban da suka hada da mataimakin firaminista da ministan kudi.
“Gaskiya, tabbatar manufofi, aiki da ka’idojin kasa da kasa ne za su zama jigon cimma manufarmu ta inganta walwala,” in ji Simsek yayin karbar ragamar ma’aikatar daga Nurettin Nebati, tsohon ministan kudi da baitulmali.
Alamun da Simsek ya bayar na kawo sauyi a sha’anin kudin Turkiyya ya yadu a kasuwannin duniya.
A sanarwar ranar Asabar, Goldman Sachs, daya daga cikin manyan kamfanunnukan zuba jari na duniya ya sanar da abokan huldarsa cewa manufofin kudi a Turkiyya za su sauya zuwa tsarin da duniya ke tafiya a kai a karkashin Simsek.
Simsek ya kuma ce “Sakko da hauhawar da farashi ya yi zuwa lamba 1 na daga manufofinmu na gajeren zango….sannan za a gaggauta habaka tattalin arziki da zai rage gibin da kasar mu ke samu,” in ji SImsek.
Ya karkare da cewa “Za mu bayar da fifiko ga samar da daidito a sha’anin kudade.”