A 2013, Turkiyya ta kasance kasa ta farko daga cikin kasashen da suka ayyana kungiyar Daesh a matsayin kungiyar ta'addanci./ Hoto:AA

Tun daga shekarar 2015 Turkiyya ta yi nasarar ‘kawar’ da 'yan ta’adda fiye da 37,800 a cewar Ministan Tsaron kasar Hulusi Akar.

"Tun daga ranar 24 ga watanYuli na 2015, an kawar da 'yan ta'adda 37,860," in ji Akar a ranar Lahadi a wajen wani taro da aka gudanar a Istanbul game da rikicin Siriya da yaki da ta'addanci.

Kazalika an kawar da karin 'yan ta'adda shida a ayyukan soji da aka gudanar a yankin arewacin Siriya, a cewar Akar.

Mahukunta a Turkiyya na amfani da kalmar “kawarwa” wajen nuna yadda ‘yan ta’addan da ake magana a kansu suka mika wuya, ko aka kashe su, ko kuma ana tsare da su.

A takaice dai Akar bai bayyana sunan ko wace kungiyar ta'addanci ba, sai dai Turkiyya na ci gaba da kai hare-hare kan kungiyoyin ta'addanci irin su Daesh da PKK.

Yaki da ayyukan ta'addanci

Tun daga shekarar 2016, Ankara ta kaddamar da wasu shirye-shiryen ayyukan yaki da ta'addanci guda uku a kan iyakarta da arewacin Siriya wadanda suka hada da ‘Euprates shield’ a 2016 da ‘Olive Branch’ a 2018 da kuma ‘peace Spring’ a 2019, a wani mataki na dakile hanyoyin kafa ayyukan 'yan ta’adda da kuma samar da zaman lafiya a tsakanin mazauna yankin.

A sama da shekaru 35 da ta kwashe tana yaki da ayyukan ta'addanci a kan Turkiyya, kungiyar PKK da Turkiyya da Amurka da kasashen Tarayyar Turai suka sanya ta a cikin jerin sunayen kungiyoyin 'yan ta'adda sakamokon dora mata alhakin mutuwar mutane sama da 40,000 ciki har da mata da yara da kuma jarirai, Kungiyar YPG ita ce reshenta da ke Siriya.

A shekarar 2013, Turkiyya ta zama daya daga cikin kasashe na farko da suka ayyana Daesh a matsayin kungiyar ta'addanci.

Tun daga lokacin ne 'yan ta'addar ke yawan kai wa kasar hare-hare, da ya kai kashe mutane sama da 300 tare da jikkata daruruwan mutane a hare-haren kunar bakin wake da suka kai kusan sau 10 da harin bama-bamai sau bakwai da kuma hare-hare da makamai sau hudu.

A martanin da ta mayar, Turkiyya ta kaddamar da ayyukan yaki da ta'addanci a cikin gida da waje domin hana duk wasu hare-hare da ake kai mata.

TRT World