Dakarun Turkiyya sun kaddamar da samamen da suka yi wa suna Operation Claw-Lock a watan Afrilun da ya gabata a maboyar 'yan ta'adda na PKK a lardin Metina, Zap, da Avasin-Basyan  da ke arewacin Iraki, kusa da kan iyaka da Turkiyya. / Hoto: AA Archive

Sojojin Turkiyya sun "kawar" da manyan 'yan ta'adda biyu na kungiyar PKK a arewacin Iraki, a cewar majiyoyin tsaro.

An kai harin ne a wani samame da aka gudanar ranar Litinin wanda aka yi wa suna Operation Claw-Lock zone kuma an kwato tarin makamai, ciki har da bindiga biyu samfurin M-16, da alburusai 180 masu girman 5.56mm, da na'urar harbo makamai ta RPG-7, da tabarau da ake amfani da shi da daddare da kuma na'urar daukar hoto.

Hukumomi a Turkiyya suna amfani da kalmar “kawarwa” idan dan ta'adda ya mika wuya ko aka kashe shi ko kuma aka kama shi.

Ankara ta sha daukar matakin kai hare-hare kan 'yan ta'adda a arewacin Iraki da zummar bankado su daga maboyarsu musamman wadanda ke kitsa kai hare-hare Turkiyya.

A shekaru fiye da 35 da ta shafe tana kai hare-hare a Turkiyya, kungiyar PKK – wadda kasashen Turkiyya, Amurka da Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin ta 'yan ta'adda – ta kashe fiye da mutum 40,000, ciki har da mata da kananan yara da ma jarirai.

AA