Shugaba Erdogan ya caccaki kungiyoyin watsa labaran duniya kan yadda suka yi watsi da kisan gillar da ake yi wa 'yan jarida a Zirin Gaza. / Photo: AA

A taron TRT World Forum na shekara-shekara, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya caccaki kafafen yada labarai na Yammacin Duniya da masu rajin kare hakkin 'yan jarida kan ƙin cewa komai a kisan 'yan jarida da ake yi a Gaza suna fakewa da kafa hujja da Hamas.

Shugaba Erdogan ya caccaki kungiyoyin watsa labaran duniya kan yadda suka yi watsi da kisan gillar da ake yi wa 'yan jarida a Zirin Gaza, inda ya bayyana Isra'ila a matsayin wadda ta yi rashin nasara a yaƙin da ake ci gaba da yi a yankin na Falasdinawa.

"Isra'ila tana kashe mata da yara ƙanana a Gaza har ma da 'yan jarida da ke kokarin gudanar da ayyuka a cikin mawuyacin hali," in ji Erdogan, a wajen ƙaddamar da babban taro karo na bakwai da aka gudanar a Istanbul a ranakun 8 da 9 ga watan Disamba.

"Sama da 'yan jarida 70 aka kashe a Gaza. Ina manyan kafafen watsa labaran duniya suke? Me ya sa ba sa ba da kanun labarai kan 'yan jaridun da aka kashe?" Shugaban na Turkiyya ya ce.

"Kowace rana ana kashe dan jarida, amma duk da haka ba mu ji wata magana daga cibiyoyin da suka shafe shekaru suna ɓaɓatun neman 'yancin 'yan jarida ba."

Taron yana gudana ne a Otel din Hilton Bomonti a birnin Istanbul, inda aka gudanar da jawabai masu sha'awa da fatan kawo sauyi.

Taken taron shi ne Haɓaka Tare: Nauyi da Ayyuka, da Matakai, ana shirya taron ne a matsayin wani wake na tattauna batutuwan da suka fi daukar hankali a duniya a yau.

Yawancin mahalarta taron a yau daliban jami'a ne. Hayat Bikana Beydi, mai shekaru 22, daga Habasha, tana karantar kimiyyar siyasa da huldar kasa da kasa a Jami'ar Istanbul.

"Maganar gaskiya ina farin cikin kasancewa a nan," Beydi ya fada kafin a fara taron da ƙarfe 1120 na safe agogon GMT. Wannan ita ce shekara ta hudu da ɗalibin Habashan ke halartar taron.

"Eh, saboda a nan mutane suna zuwa suna ba da labarin abubuwan da suka faru, muna son koyi da su saboda mutanen da suka zo nan sun fi mu ƙwarewa. Don haka mun koyi abubuwa da yawa a wurinsu."

"A cikin zuciyata ba ni da taƙamaiman wanda na fi so a cikin masu gabatar da jawabi, amma ina sa ran dukkansu za su kasance masu kyau," Beydi, wacce ta fara jin labarin taron daga shirin bayar da tallafin karatu a jami'a ta fada, ta ƙara da cewa taron ya kuma shafi karatunta.

Ta ƙara da cewa, "Saboda masana sun zo suna ba da labarin abubuwan da suka faru, kuma [a matsayinmu na dalibai], muna son a yi koyi da su saboda mutanen da suka zo nan suna da ƙwarewa sosai don raba."

Zahra Ismail Hussein, mai shekaru 23 daga Somaliya, tana da ra'ayi iri daya, inda ta ce jin yadda ƙawayenta ke magana kan abubuwan da suka faru a baya ya sa ta samu halartar wannan shekarar. "Ina ɗokin ganin na halarta na ga yadda abin yake, kuma ina fatan koyon ilimi daga masu jawabi," in ji Hussein.

Darakta Janar na TRT Mehmet Zahid Sobaji ya bude taron da jawabi, inda ya ce Falasdin za ta zama a kan gaba wajen tattauna wa a taron. Ya kara da cewa duniya na kallon yadda 'yan adam ke mutuwa a Gaza.

‘Yada labaran karya – barazana ga zaman lafiyar siyasa’

Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun, da ya fara bayani, ya bayyana fatan taron zai samar da mafita ga matsalolin duniya.

Ya kara da cewa yada labarai da bayanan karya barazana ne ga ingantacciyar siyasa da dimokuradiyyar kasashe, inda ya yi Karin haske da cewa Isra’ila ba ta isa ta yi wuru-wuru wajen janye ra’ayin duniya ba.

A yayin da yakin da Isra’ila ke yi a Gaza ya shiga rana ta 63, mazauna Gaza, tare da na sauran yankunan da ake rikici, har da na Ukraine na daga batutunwa da taron ya mayar da hankali a kai.

Yara kanana shida da ke wakiltar yankunan da ake rikici sun mika wa Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan mubudin shekaru dari na Turkiyya.

Bayanin shugaban kasar ne babban abun da kowa ke jiran saurara a wajen taron, ciki har da dalibar Indonesia, mai shekara 22 da ke halartar taron a karon farko.

Jiran Zuwan Shugaban Kasa

“Wani babban bakon da nake sauraran zuwan sa shi ne shugaba Erdogan. Hakan ne ya sanya ni zuwa nan, don nag a shugaban kasa. Ina tunanin yana da hikima da karfin fada a ji, wannan zangonsa na uku a matsayin shugaban kasa, ko? A ra’ayina, yana gudanar da jagoranci mai kyau,” in ji Qhiftia.

Dalibar shaianin gudanar da kasuwanci ‘yar shekara 22 ta kara da cewa manufar taron, ‘yan jaridu da manyan masu jawabi ne suka ja hankalina na cike fom din neman halartar taron TRT World Forum. “A yau, akwai batun da ya shafi yakin da ake yi a Gaza, ina sauraren halartar wannan zama.”

A jawabinsa, shugaba Erdogan ya kalubalance kafafan yada labarai na Yammacin duniya kan yadda suke bayar da labaran ‘yan jaridar da aka kasha a Gaza, yana cewa Isra’ila na aikata kisan gilla ga ‘yan jaridar da ke bayar da rahotanni na gaskiya. Kafafan yada labaran Turkiyya na kokarin zama muryoyin wadanda ake zalunta.

Sama da masu jawabi 150 da suka hada da malaman jami’a, ‘yan siyasa, kwararrun binciken siyasa, ‘yan jarida da suaran su ne daga sassan duniya daban-daban sun hadu a Istanbul don bayyana kwarewarsu ga baki mahalarta. Ya zuwa yanzu, taron ya hada baki 8,500 da masu gabatar da jawabi 651.

Manyan batutuwan da aka tattauna a kai sun hada da tsaron kasa da kasa, makamashi, sauyin yanayi, tattalin arziki, fasahar kere-kere da yada labarai d ama siyasa.

TRT World