Kalama Shugaba Erdogan na zuwa ne kwana guda bayan da wani dan kasar iraki ya kona Kur'ani a gaban wani masallaci ranar sallah a birnin Stockholm na Sweden. / Photo: AA

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce kasarsa ba za ta taba lamuntar tunzuri da barazana ba, kwana guda bayan da aka kona Alkur'ani mai tsarki a Sweden.

"Za mu koya wa Kasashen Yamma masu izgilanci cewa cin mutuncin Musulmai ba 'yancin fadin albarkacin baki ba ne," Erdogan ya shaida wa mambobin Jam'iyyarsa ta AK a wani sakon bidiyo a ranar Alhamis.

"Turkiya za ta ci gaba da mayar da martani ta hanya mai karfi har sai mun yaki kungiyoyin ta’addanci da na makiyan Musulunci da karfinmu," ya kara da cewa.

"Da wadanda suka aikata laifin (Kona Alkur’ani)da masu daukar hakan a matsayin ‘yancin fadin albarkacin baki da kuma masu kawar da kai tamkar ba su ga ana yi ba, duk ba za su cimma burikansu ba," in ji shugaban kasar.

Karuwar matsalar

Wan dan kasar iraki ne ya kona Alkur'ani mai tsarki a gaban wani masallaci a birnin Stockholm na kasar Sweden a ranar Sallah..

Sannan ranar 12 ga watan Yunin da muke ciki ma wata kotu a Sweden ta daukaka kara kan neman a sauya hukunci wata karamar kotu na dage haramcin kona Kur'ani, inda ta yanke cewa 'yan sanda ba su da hurumin hana gangamin kona Kur'anin har sau a farkon shekarar nan.

A watan Fabrairu, 'yan sanda sun ki ba da izinin kona Kur'ani da aka yi har sau biyu, inda suke ba da hujja da batun tsaro, bayan da wani dan kasar Denmark mai tsaurin ra'ayi Rasmus Paludan ya koma Kur'ani a kofar ofishin jakadancin Turkiyya a birnin Stockholm a watan Janairu.

Daga baya, wasu mutum biyu da suka yi kokarin daukar matakin mayar da martani a wajen ofisoshin jakadancin Iraki da Turkiyya a Stockholm sun daukaka kara kan matakin.

A watan Afrilu, Kotun Stockholm ta sauya matakin, inda ta yanke cewa barazanar tsaron ba ta da yawan da za ta hana yin gangamin.

TRT World