Za a samu zaman lafiya mai dorewa a Gabas ta Tsakiya ne kawai idan aka warware rikicin Falasdinawa da Isra'ila, in ji Shugaba  Recep Tayyip Erdogan. /Hoto: AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ranar Lahadi ya ce bai kamata a ci gaba da yin jinkiri wurin samar da kasar Falasdinawa mai cin gashin kanta wadda ke da hedikwata a Gabashin Birnin Kudus kamar yadda take a shekarar 1967 ba.

“Za a samu zaman lafiya mai dorewa a Gabas ta Tsakiya ne kawai idan aka warware rikicin Falasdinawa da Isra'ila,” in ji Erdogan a yayin da yake bude Cocin Kiristoci na gargajiya ta Mor Ephrem Syriac Orthodox Church a Yesilkoy da ke birnin Istanbul. Ita ce coci ta farko da aka gina a zamanin Jamhuriyar Turkiyya.

Shugaba Erdogan ya ce shirye Turkiyya take ta taka rawa wajen kawo karshen rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinawa da rage tayar da jijiyar wuya a yankinsu.

“Batun Falasdinawa shi ne silar matsalar da ake fama da ita a yankinmu. Yankin ba zai samu zaman lafiya ba sai an samar musu kasa mai zaman kanta,” a cewar shugaban kasar Turkiyya.

Erdogan ya jaddada cewa ya kamata a guji duk wani yunkuri na kara rura wutar rikici a yankin domin kuwa zai haddasa “kara zubar da jini.”

Ya ce Turkiyya tana matsa kaimi wajen ganin an bi hanyoyin diflomasiyya wajen samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

Kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta kaddamar da hari mai suna Operation Al-Aqsa Flood ranar Asabar domin yin martani kan kutsen da Isra'ila ta yi a Masallacin Kudus da kuma 'yan kama-wuri-zauna da ke kwace wuraren Falasdinawa. Ta harba dubban rokoki sannan ya yi garkuwa da 'yan Isra'ila masu dimbin yawa.

Nan da nan Isra'ila ta yi martani a wani hari da ta kaddamar mai taken Operation Swords of Iron a kan Hamas, inda ta rika luguden wuta a Zirin Gaza.

Kawo yanzu daruruwan mutane sun mutu daga bangarorin biyu, kuma ana ci gaba da fafatawa.

AA