Hukumomi sun ce za a ci gaba da daukar matakan inganta suna da murya da kamanni don gudun damfara. Hoto: Reuters Archive

Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya (MIT) ta gano wani mutum da ya yi amfani da kirkirarriyar basira AI, wajen kwaikwayon muryar Shugaba Recep Tayyip Erdogan don ya yaudari wasu zababbun kamfanoni da kuma manyan jami'an gwamnati.

MIT ta gano cewa dan damfarar ya yi amfani ne da manhajarkirkirarriyar basira don yin irin muryar Shugaba Erdogan tare da kiran wayoyin wasu 'yan kasuwar wasu fitattun kasashen waje fiye da 10.

Ba tare da bata lokaci ba aka kama mutumin tare da mika shi ga hukumomin tsaro, godiya ga kokarin bajinta da sassan tsaron intanet na hukumar MIT, a cewar majiyoyin tsaro.

Jami'ai sun jaddada bukatar da ake da ita ga mazauna kasar da su ci gaba da yin taka tsantsan a irin wannan yanayi da ake kokarin yin kutse da aikata laifukan intanet, sun kuma ce za a ci gaba da daukar matakan inganta suna da murya da kamanni don gudun damfara.

TRT World