10:44 GMT — Shugaban Turkiyya, Tayyip Erdogan ya ce ya yi imanin cewa shugaban Rasha, Vladimir Putin yana son cigaban yarjejeniyar da ta bayar da dama a fita da hatsi daga Ukraine ta tekun Bahar Aswad, bayan gwamnati a Moscow ta ce za ta dakatar da shirin.
Yayin da yake magana da 'yan jarida, shugaba Erdogan ya ce zai tattauna kan shirin, da kuma fitar da takin Rasha, tare da shugaba Putin idan suka hadu a ido-da-ido a taron da ake fatan za su yi a watan Agusta.
Amma kuma ya nunar da cewa akwai yiwuwar su tattauna da shugaban Rasha ta wayar tarho, ba tare da jiran taron su na watan Agusta ba.
Shugaba ErdoA koda yaushe, Turkiyya tana ba da muhimmanci ga cigaba da yarjejeniyar ta Jigilar Hatsia ta Bahar Aswad, kuma kasar ta karfafa yunkurinta na diflomasiyya don cimma hakan.
08:56 GMT — Rasha ta 'dakatar' da yarjejniyar Bahar Aswad kan Jigilar Hatsi
Gwamnatin Rasha ta ce yajejeniyar hatsin Ukraine ta zo karshe a zahiri, awanni kafin wa'adinta ya kare, kuma Rasha za ta koma aiki da yarjejeniyar mai muhimmanci, matukar aka cimma shrudan da ta gindaya.
"Yarjejeniyar Bahar Aswad ta kawo karshe a zahiri," a cewar kakakin gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov.
"Yarjejeniyar hatsin ta daina aiki. Da zarar an cika sharudan bangaren Rasha (na yarjejeniyar), Rasha za ta dawo aiki da yarjejeniyar nan-take."
A wani bangaren, Rasha ta sanar da Turkiyya, da ukraine, da Majalisar Dinkin Duniya a hukumance, cewa ba za ta tsawaita yarjejniyar ba, a cewar kamfanin dillancin labarai na kasar, RIA, inda suka ambato mai magana da yawun Ma'aikatar Kasashen Waje, Maria Zakharova.
0716 GMT — Rasha ta ce Ukraine ce ta kai harin gadar Cremea
Kasar ta Ukraine ta kai hari kan gadar Crimean a tsakar daren jiya ta amfani da jirgin ruwa mara matuki, wanda, a cewar kwamitin Rashi mai yaki da ta'addanci, kamar yadda gidan jaridan kasa ya ruwaito.