A wani shirin hadin gwiwa na fitar da hatsi da hannun MDD, Erdogan ya ce Turkiyya za ta cimma mafitar da kowa ke tsammani a dan kankanin lokaci.  / Hoto: AA

Akwai bukatar dawo da batun yarjejeniyar fitar da hatsi ta Tekun Bahar Aswad tare da magance matsalolin da tun farko suka jawo dakatar da yarjejeniyar, in ji Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, bayan kammala ganawar da aka dade ana jiran faruwarta tsakaninsa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin.

A ranar Litinin ne shugabannin biyu suka tattauna kan batutuwan da ke faruwa a yankinsu da kuma na duniya baki daya, da ma batutuwan diflomasiyya. Dawo da batun yarjejeniyar hatsi ta Tekun Bahar Aswad ta bara da ta taimaka wajen dakile matsalar abinci da aka fuskanta a duniya ce ta mamaye ganawar tasu.

"Mun yi amannar cewa ya kamata a ci gaba da magana kan shirin, ta hanyar gyara duk wasu matsaloli da suka jawo cikas," Erdogan ya shaida wa taron manema labarai da ya yi da Putin a yayin ziyararsa ta kwana daya zuwa birnin Sochi na Rasha.

Da ake tabbatar da muhimmancin cika bukatun fitar da hatsin da kuma taki da ya kamata Rasha ta yi, Turkiyya ta ce babu wani zabin da ya wuce tabbatar da shirin.

"Zabukan da ake so su maye gurbin yarjejeniyar hatsin ba za su iya samar da yanayi mai dorewa da tsaro da kuma tsarin hadin kai na dindindin tsakanin bangarorin biyu ba, babu kamar shirin yarjejeniyar hatsi ta Bahar Aswad," in ji Erdogan.

Yarjejeniyar ta taka "muhimmiyar rawa" a wajen magance matsalar abinci ta duniya, Erdogan ya fada, yana mai cewa shirin tamkar bututun numfashi ne ga wadanda suke cikin tsananin bukata kamar a Afirka.

A shirye ake a yi abin da dace

A shirye Ankara take ta yi abin da ya dace don aika hatsi zuwa wasu kasashen Afirka da ke fama da talauci, in ji Erdogan, yana mai cewa Turkiyya da Rasha sun amince da hakan.

"Putin ya ce, 'Mun kammala tsare-tsaren aika tan miliyan daya na hatsi zuwa kasashe matalauta' mu kuma mun ce, 'Mu, a matsayinmu na Turkiyya, mun dauki nauyin yin duk aikin da aka dora mana," ya ce.

Ukraine na bukatar ta tausasa yadda take gudanar da al'amura don ta hada hannu da Rasha wajen daukar mataki a yayin da ake ci gaba da yakin, Erdogan ya jaddada, yana mai cewa: "A baya mun karbi bakuncin tattaunawar sasanci tsakanin bangarorin. A shirye muke mu yi abin da ya kamata, kamar ko yaushe, a kan wannan batun.

Kan batun hada kai wajen tsara fitar da hatsi da ake shiryawa da Majalisar Dinkin Duniya, Erdogan ya ce Turkiyya za ta samar da wata mafita da za ta cimma dukkan abubuwan da ake sa rai cikin dan kankanin lokaci."

A watan Yulin da ya gabata, Rasha ta dakatar da sa hannunta a yarjejeniyar da Turkiyya ta samar ta dawo da aikin fitar da hatsi daga tasoshin jiragen ruwa uku na Tekun Bahar Aswad na Ukraine, wadda aka dakatar bayan yakin Ukraine da aka fara a watan Fabrairun 2022.

Moscow ta yi korafin cewa Kasashen Yamma sun gaza yin wajibcinsu a kan fitar da hatsin Rasha, kuma hatsin da ake fitarwa daga Ukraine bai kai yawan da kasashen duniya ke bukata ba. Ta ce takunkuman da aka saka a kan biyan kudade da tsare-tsare da inshora sun yi matukar tasiri wajen hana fitar da hatsin.

A shirye Ankara take don ci gaba da aikinta don cimma zaman lafiya mai dorewa da ci gaban yankin, kuma tana ta kokarin samar da mafita ta diflomasiyya don dawo da yarjejeniyar ta watan Yulin 2022.

Turkiyya tana kuma ci gaba da yin kira ga Kiev da Moscow don kawo karshen yakin da ake yi ta hanyar sasantawa.

Hadin kai mai

A ranar Litinin ne Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin ya ce ana ci gaba da samun hadin kai tsakanin Turkiyya da Rasha a kan batutuwa da dama, kuma shi da Erdogan suna tattauna muhimman abubuwa don samar da hadin kai tsakanin kasashen nasu.

“Ana samun nasara a hadin kai kan bangarori da dama tsakanin Rasha da Turkiyya, wanda ya ta'allaka a kan akidun kyakkyawar makwabtaka da hadin gwiwa da amfanar juna,” Putin ya shaida wa taron manema labarai da ya yi da Erdogan.

“Mun yi musayar ra'ayi a kan batutuwa kamar na yanki da duniya baki daya," Putin ya ce, inda ya kara da: "Babu shakka, tattaunawar yau za ta yi amfani wajen inganta hadin gwiwar Rasha da Turkiyya a dukkan bangarori."

Putin ya ci gaba da bayyana cewa shi da Erdogan sun lura da ci gaba da ake samu na habakar kasuwanci da tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa yawan kasuwancinsu ya karu da kashi 86 cikin 100 inda aka yi kasuwancin dala biliyan 62 a karshen shekarar 2022, daga baya kuma ya sake karuwa da wani kashi hudun a wata shidan farko na wannan shekarar.​​​​​​​​​​​​​​

AA