Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi kakkausar suka ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na shawarar raba Falasdinawa da matsugunansu na Gaza, inda ya kira hakan "abin da ba za a amince da shi ba".
"Tattauna wannan batu ma kuskure ne," in ji Fidan a ranar Laraba, yana mai sake jaddada matsayin Turkiyya na kalubalantar duk wani yunkuri na raba jama'ar Gaza da kasarsu.
A ranar Talata Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya ce Amuka "Za ta karbe" Gaza, jim kadan bayan bayar da shawarar a sauya wa Falasinawa wajen zama na dindindin a wani waje da ba Gaza ba.
"Amurka za ta karbe iko da Zirin Gaza, kuma za mu yi aiki da hakan mu ma," ya fadi haka a wajen taron manema labarai da Firaministan Ira'ila Benjamin Netanyahu.
Game da Syria, Fidan ya jaddada cewa Sham ba ta da shirin koma wa tsarin tarayya ko bayar da 'yanci ga wani yanki, yana mai cewar gwamnatin Syria ta kudiri aniyar kare martabar iyakokinta.
Ya kara da cewa "Matsayar Shugaban Kasar Syria al Sharaa kan kungiyar ta'adda ta PKK/YPG a bayyane take karara kuma ta dace da bukatun tsaro na Turkiyya."
Fidan ya kuma yi tsokaci cewar Syria ta yi alkawarin kora ko kakkabe dukkan 'yan ta'addar PKK da suka shiga kasar daga sauran kasashe domin tsare hadin kan kasar.
Ya kuma sanar da shirin hada kai tsakanin Turkiyya, Iraki, SYria da Jordan don karfafa hadin kai a yaki da 'yan ta\addar Daesh.