Turkiyya ta dade tana kira ga bangarorin biyu da su samar da kasashe biyu da kowacce ke da 'yancin gashin kanta, yana mai jaddada cewa hakan ne kawai zai samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Gabas ta Tsakiya / Hoto: AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi gargadin cewa hare-haren da Israi'la take kai wa Gaza na "rashin kan-gado da ba su da hujja" tamkar kisan kiyashi ne da za su iya jawo mata ƙyama daga ƙasashen duniya.

"Hare-haren rashin kan gado kuma marasa tushe da Isra'ila take kai wa Gaza zai iya jawo mata rashin daraja a idanun duniya,” a cewar Erdogan ranar Laraba a yayin da yake jawabi ga taron jam'iyyar Justice and Development (AK) a babban birnin kasar Ankara.

"Ruwan bama-bamai a wuraren da fararen-hula suke zaune, da kashe fararen-hula da gangan da hana motocin kai agaji shiga yankin da ma toshe duk wata hanya da za a taimaka wa mutane na nuna cewa Isra'ila 'yar ta'adda ce ba kasa ba ce," in ji Erdogan.

Ya ƙara da cewa: “ka da Israi'la ta manta cewa idan ta riƙa halaye irin na kungiyoyin ('yan ta'adda), to kallon da za a riƙa yi mata kenan.”

Erdogan ya ce Turkiyya ta yi amannar cewa babu wata hujja da za ta sa a rika kai hari kan fararen-hula.

"Rikicin da ake bin kowace hanya ta rashin kunya wajen aiwatar da shi kisan kiyashi ne ba yaƙi ba," in ji shugaban Turkiyya.

Dakarun Isra'ila sun ƙaddamar da hare-hare a Gaza don yi martani kan kutsen da ƙungiyar Hamas ta yi a yankinta.

An soma rikicin ne ranar Asabar lokacin da Hamas ta kaddamar da harin ba-zata da ta kira Operation Al Aqsa Flood a Isra'ila, nda ta harba dubban rokoki da yin kutse ta sama da kasa da ruwa cikin kasar, domin abin da ta kira ramuwar gayya kan mamayar da Isra'ila ta yi wa Masallacin Kudus a Gabashin Birnin Kudus da kuma ci gaba da gine-ginen da 'yan kama-wuri-zauna na kasar suke yi a Gaza.

Nan da nan dakarun Isra'ila suka mayar da martani wajen kai hare-haren da suka kira Operation Swords of Iron a kan Hamas inda suka rika luguden wuta a Gaza.

Kazalika Isra'ila ta katse ruwa da wutar lantarki a Gaza, lamarin da ya kara jefa yankin cikin bala'i wanda aka tsananta tun 2007.

'A shirye Turkiyya take ta shiga tsakani'

Erdogan ya ce ko a fagen yaki akwai wasu ka'idodji na da'a da suka kamata a kiyaye.

"Muna Allah wadai da kisan fararen-hula a Isra'ila. Kazalika ba za mu taba amincewa da kisan kiyashi a Gaza ba ta hanyar yi musu luguden wuta," in ji shi.

Shugaban kasar ya yi kira ga kasashen duniya su sanya baki domin ganin an kawo karshen rikicin.

"Muna Allah wadai da tunzurawar da masu ruwa da tsaki na yankin suke yi, wadanda, mai makon su kashe wutar rikicin, su ne suke izata. Muna kira ga Amurka da Turai da sauran su dauki matsaya bisa adalci da dattako da jinkai kan bangarorin biyu.

"Ya kamata a guji daukar matakin da zai gallaza wa dukkan Falasdinawa, irin su hana su agajin jinkai," in ji Erdogan, yana mai sukar matakin da Isra'ila ta dauka a wannan makon.

TRT World