Ministan Harkokin Wajen Turkyya Hakan Fidan ya yi tur da kona Alkur'ani mai tsarki da aka yi a kasar Sweden a ranar Sallar Layya, yana mai cewa ba za a lamunci hakan ba.
"Ba za mu lamunci aikata irin wadannan ayyuka na yaki da Musulunci ba da sunan 'yancin fadin albarkacin baki," kamar yadda Fidan ya fada a wata sanarwa da aka wallafa a shafukan sada zumunta.
"Dauke kai da nuna kamar ba a ga abin da ke faruwa ba tambkar aikata laifin ne," in ji Fidan.
A hannu guda kuma, mai magana da yawun Jam'iyyar AK mai mulki a Turkiyya Omer Celik, a wata sanarwa ya ce: "Muna Allah-wadai da hukumomin Sweden kan bayar da izinin kona Alkur'ani a gaban wani masallaci a ranar Sallar Idi."
"Muna yin tur da kakkausar murya kan matsayar Kotun Kolin Sweden na kare kalaman kiyayya.
"Duk wani salo na raini laifi ne ga bil adama. Za mu ci gaba da yaki da wadannan la'anannun ayyuka da karfinmu ta duk hanyar da ta dace a siyasance ko a shari'ance," in ji Celik.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan da 'yan sandan Sweden suka bayar da izinin kona Kur'ani a gaban wani masallaci.
'Yan sanda sun ce dalilan da aka bayar a rubuce na barazanar da ke tattare da kona Kur'ani ba su da karfi a shari'ance, kuma ba za a iya watsi da bukatar son konawar ba."
Kotun daukaka kara ta Sweden ce ta yi watsi da karar 'yan sanda ta hana izinin gudanar da zanga-zanga biyu a Stockholm, ciki har da ta kona Alkur'ani, mako biyu da suka wuce.