Shugaban Turkiyya ya bukaci a bar kasarsa ta shiga Tarayyar Turai idan ana so ya amince Sweden ta zama mamba a NATO/ Hoto: Reuters Archive

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce zai nemi taron NATO ya bude wa kasarsa kofar zama mamba a Tarayyar Turai idan ana so ya amince wa Sweden ta shiga kungiyar ta NATO.

"Da farko, ina kira ga kasashen da suka sa Turkiyya ta kwashe fiye da shekara 50 tana jiran zama mamba a Tarayyar Turai, da su bari mu shiga kungiyar, daga nan za mu bari Sweden ta shiga NATO kamar yadda muka bari Finland ta zama cikin kungiyar" in ji Erdogan a taron da ya yi ranar Litinin jim kadan kafin ya bar kasar zuwa Vilniu, babban birnin Lithuania don halartar taron NATO.

Kazalika Erdogan ya jaddada cewa kyale Sweden ta zama mamba a NATO ya ta'allaka ne da cike sharuddan da aka gindaya a yarjejeniyar da suka sanya a Madrid a taron na NATO na shekarar da ta gabata.

A baya Erdogan ya nuna rashin jin dadinsa game da abin da ya kira gazawar Sweden wajen cika alkawuran da ta dauka na murkushe 'yan ta'adda na kungiyar PKK da masu goyon bayansu wadanda "suke yawo a kan titunan" Stockholm.

Tun shekarar 1987 ta nemi zama mamba a Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Tarayyar Turai -- wadda ta gabaci kungiyar Tarayyar Turai.

Ukraine za ta mamaye taron NATO

Za soma taron shugabannin NATO na kwana biyu a ranar Litinin 10 ga watan Yuli kuma zai mayar da hankali a kan yakin Rasha da Ukraine da tasirinsa a kan kungiyar da kuma matakan da za su dauka don karfafa kawancen soji da ke tsakanin kasashen kungiyar.

Kazalika za a tattauna kan bukatar Sweden ta shiga kungiyar ta NATO.

A gefen taron, ana sa rai Erdogan zai tattauna da takwarorinsa kan batutuwa daban-daban, cikinsu har da taron da zai yi da shugaban Amurka Joe Biden.

Finland da Sweden sun yi rajistar zama mambobin NATO bayan soma yakin Rasha da Ukraine a watan Fabrairun 2022.

Ko da yake Turkiyya ta amince Finland ta zama mamba a NATO, har yanzu tana jira Sweden ta cika alkawuran da ta yi a shekarar da ta wuce a Madrid kafin ta amince da ita.

A baya, Erdogan ya ce ba zai amince Sweden ta zama mamba a NATO muddin ta ci gaba da bai wa 'yan ta'adda da magoya bayansu mafaka.

TRT World