Erdogan ya yi nasara a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa wanda aka yi ranar Lahadi inda ya samu kashi  52.18 na kuri'un da aka kada. / Hoto: Reuters Archive

Za a rantsar da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a majalisar dokokin kasar ranar Asabar, a cewar daraktan sadarwar kasar.

A yayin da yake tattaunawa da gidan talabijin na 24 TV ranar Alhamis, Fahrettin Altun ya ce Shugaba Erdogan zai sanar da kafa sabuwar majalisar zartarwarsa a ranar ta Asabar.

Bayan ya sha rantsuwa, Erdogan zai ziyarci Anitkabir, inda kushewar Ataturk take, in ji Altun.

Kazalika shugaban kasar zai karbi bakuncinshugabannin kasashen duniya a bikin cin abincin dare ranar rantsar da shi, in ji kakakin gwamnatin.

Altun ya ce daga bisani da daddare Shugaba Erdogan zai sanar da kafa sabuwar majalisar zartarwarsa.

Ya zargi kamfanonin sada zumunta na duniya da nuna son kai lokacin zabukan kasar ta Turkiyya, yana mai cewa da alama shafin Twitter ya rika yin ''abubuwan da za su biya bukatun Amurka'' lokacin zaben.

Erdogan ya yi nasara a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa wanda aka yi ranar Lahadi inda ya samu kashi 52.18 na kuri'un da aka kada, yayin da babban mai hamayya da shi Kemal Kilicdaroglu ya samu kashi 47.82.

TRT World