A ranar Lahadi za a gudanar da zaben zagaye na biyu inda sakamakon zaben zai byyana wanda zai ci gaba da jagorantar Turkiyya. Hoto/AA

‘Yan Turkiyya za su jefa kuri’a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa wanda ake ganin shugaba mai ci Recep Tayyip Erdogan zai kayar da babban abokin adawarsa Kemal Kilicdaroglu bayan ba a samu wani dan takara da ya samu sama da kaso 50 cikin 100 na kuri’un da aka jefa a zagaye na farko ba da aka gudanar 14 ga watan Mayu.

Za a soma zaben na ranar Lahadi da misalin karfe 8:00 na safe agogon kasar [05:00GMT] a kuma kammala da misalin karfe 5:00 agogon kasar [1400GMT]. Zuwa cikin daren Lahadi, alamu za su fito fili na wanda ake ganin zai samu nasara a zaben kasar.

Sama da mutum miliyan 60 aka yi wa rajista domin su yi zabe, daga ciki har da mutum militan 4.9 wadanda za su yi zabe a karon farko. Jimlar akwatunan zabe 191,885 aka samar ga masu zabe a kasar.

Kamar yadda hukumar zaben Turkiyya ta tabbatar, sama da mutum 1,895,430 suka jefa kuri’a a ofisoshin jakadanci da ke kasashen waje zuwa karfe 10:00 na safe agogon Turkiyya a ranar Alhamis.

A zaben da aka gudanar na 14 ga watan Mayu, jimlar ‘yan Turkiyya 1,839,470 da ke kasashen waje suka je domin jefa kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa.

Wadanda ba su samu sun jefa kuri’arsu ba a kasashen da suke zuwa lokacin da aka kayyade, za su iya zaben a shingen bincike na kwastam har zuwa karfe biyar agogon kasar a ranar Lahadi.

Babbar nasarar Turkiyya

A ranar Asabar, Erdogan ya yi kira ga jama’a da su fito su kada kuri’a, inda ya ce “bari mu soma sabon karnin Turkiyya da kuri’unmu.

“A gobe, mu tafi rumfunan zabe a tare domin Turkiyya ta samu babbar nasara. Mu kara karfi wajen aiwatar da abin da aka aiwatar a zaben ‘yan majalisa na 14 ga watan Mayu ga zaben shugaban kasa,” in ji Erdogan a Twitter.

Miliyoyin masu zabe suka tafi rumfar zabe a ranar 14 ga watan Mayu domin zaben shugaban kasar da kuma ‘yan majalisar kasar 600.

Kawancen jam’iyyu na Erdogan ne suka zama masu rinjaye a majalisar kasar, inda aka tafi zagaye na biyu a zaben shugaban kasar sakamakon babu dan takarar da ya samu sama da kashi 50 cikin 100 na kuri’un kasar.

Erdogan mai shekara 69 ya take zaben jin ra’ayi da kasashen yamma suka yi inda ya sha gaban abokin takararsa Kemal Kilicdaroglu da kusan maki biyar a zagaye na farko.

Erdogan ya samu kashi 49.52 inda abokin takararsa Kilicdaroglu wanda shi ne babban abokin adawa na Jam’iyyar CHP da kuma kawancen jam’iyyu shida suka samu kashi 44.9.

‘Ina sa rai za mu tafi tare’

Bangaren Kilicdaroglu suna ta kokarin samun kwarin gwiwa bayan rudun da suka shiga sakamakon yadda Erdogan ya kasance a kan gaba a zagayen farko.

Wannan zaben zai yanke hukunci kan wa zai jagoranci Turkiyya, kasar da ke kungiyar NATO da ke da mutum miliyan 85 haka kuma kasar duniya mafi karbar ‘yan gudun hijira, inda take da ‘yan gudun hijira mutum miliyan 5 inda miliyan 3.3 daga Syria suka fito, kamar yadda bayanai daga ma’aikatar harkokin cikin gida suka nuna.

Wanda ya zo na uku a zaben shugaban kasar Sinan Ogan ya bayyana cewa ya goyi bayan Shugaba Erdogan saboda aniyar da yake da ida “ta yaki da ta’addanci ba kakkautawa,” inda yake alakanta hakan da kungiyar ta’addanci ta PKK da kawarta YPG da kuma FETO wadda ke da hannu a yunkurin juyin mulkin da aka yi a 2016.

Wani jigo a kasar Turkiyya Umit Ozdag, wanda shi ne shugaban Jam’iyyar ZP da ke adawa da ‘yan gudun hijira, ya ayyana goyon bayansa ga Kilicdaroglu bayan ya bayyana cewa zai kori ‘yan gudun hijira.

Jam’iyyar ZP din ta samu kashi 2.2 a zaben da aka gudanar a wannan watan na ‘yan majalisa. Wata kuri’ar ra’ayi da kamfanin Konda ya yi, ya saka zaben zagaye na biyu bisa hasashen cewa Erdogan zai samu kashi 52.7 sai kuma Kilicdaroglu kashi 47.3 bayan rarraba kuri’un da ba tantance ba.

An gudanar da kuri’ar jin ra’ayin tsakanin 20 zuwa 21 ga watan Mayu kafin Ogan da Ozdag su bayyana goyon bayansu.

“Turkiyya tana da wata tsohuwar al’ada ta dimokradiyya da kuma al’adar kishin kasa, kuma a halin yanzu ‘yan kishin kasar ne ke gaban gaba. Erdogan ya hada addini da kishin kasa ,” in ji Nicholas Danforth, wani masanin tarihin Turkiyya.

“Karin Erdogan na nufin karin Erdogan. Mutane sun san wanene shi kuma me yake so kasarsa ta cimmawa, kuma da alama cewa da dama daga cikinsu sun amince da hakan.”

Erdogan a ranar Asabar ya bayyana cewa yana kyautata zaton cewa wadanda suka zabi jam’iyyun adawa a ranar 14 ga watan Mayu kamar CHP da DEVA da HDP da Jam’iyyar IYI za su sauya shawara su zabi People’s Alliance a ranar Lahadi.

TRT World