Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce masu mulkin kama-karya ba sa zuwa zabe zagaye na biyu.
"Ta yaya mutumin da zai shiga zagaye na biyu na zabe maimakon ya tabbatar an kammala zaben a zagayen farko ya zama mai kama-karya? Wannan shi ne gaskiyar batu," kamar yadda Erdogan ya shaida wa wakiliyar CNN Becky Anderson a wata hira da aka watsa a ranar Juma'a.
"Muna kawance da 'yan majalisar dokoki 322 kuma jagoran wannan kawancen zai tafi zabe zagaye na biyu a matsayin na farko. To wane irin dan kama-karya ne wannan?
Da aka tambaye shi ko zai ci gaba da aiki da Shugaban Kasar Amurka Joe Biden, sai shugaban Turkiyyan ya ce: "Babu ko shakka."
"Zan yi aiki da Mista Biden kuma idan Biden ya tafi zan yi aiki da duk wanda ya gaji kujerarsa," ya kara da cewa.
Rashin adalcin kasashen Yamma a kan Rasha
Erdogan ya yi magana a kan matakan da kasashen Yamma karkashin jagorancin Amurka ke dauka a kan Rasha a kan yakin da kasar ke yi da Ukraine, yana mai cewa Kasashen Yamma ba sa bin lamarin ta hanyar yin adalci tsakanin kasashen biyu da ke yaki.
"Kana bukatar bin matakan adalci a kan kasa irin Rasha, wanda hakan zai fi zama hanya mafi dacewa," a cewar shugaban Turkiyyan, yana mai ba da misali da Shirin Fitar da Hatsi da Tsaba ta Bahar Aswad wanda aka cimma bisa kokarin Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya.
"Ba wai bukatun kasashen Yamma kawai muka duba ba, har ma da na kasashen Afirka," in ji Erdogan.
"An tsawaita wannan shiri na fitar da tsaba da karin wata biyu daga ranar 18 ga watan Mayu. Ta yaya kuke ganin hakan ya yiwu? Ya yiwu ne saboda kyakkyawar alakarmu da Shugaba Putin," ya ce.
Zabe zagaye na biyu
Zaben shugaban kasar Turkiyya na 2023 ya tafi zagaye na biyu bayan da aka rasa dan takarar da ya samu mafi rinjayen kuri'un da ake bukata a zagaye na farko da aka yi ranar 14 ga watan Mayu.
An kammala zagayen farko na zaben a ranar Lahadi ba tare da kowane dan takara ya samu kashi 50 cikin 100 na jumullar kuri'un da aka kada ba, amma Shugaba Erdogan mai mulki ne ke kan gaba.
Bayan ayyana sakamakon, Erdogan ya ce kasar ta sake kammala "wata nasarar ta dimokuradiyya", yana mai cewa kasar ta sake ganin yawan mutanen da suka fita zabe a tarihinta da kashi 86.98 cikin 100.
Ya samu kashi 49.51 cikin 100 a zagayen farko na zaben, kamar yadda shugaban Hukumar Koli ta Zaben Kasar (YSK) Ahmet Yener ya bayyana.
Yayin da babban abokin karawar Erdogan, Kemal Kilicdaroglu ya tsira da kashi 44.88 cikin 100. Zaben da za a yi zagaye na biyu ranar 28 ga watan Mayu zai zama fafatawa ce tsakanin Erdogan da Kilicdaroglu.