Hakan Fidan ya rike muhimman mukamai a fannin harkokin waje da kuma ma’aikatun tsaro. / Hoto: AA

An nada Hakan Fidan, shugaban hukumar leken asirin Turkiye [MIT], a matsayin Ministan Harkokin Wajen Kasar, cikin jerin sunayen sabbin ministocin da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana.

Fidan, wanda ya maye gurbin Mevlut Cavusoglu a matsayin babban jami’in diflomasiyya na kasar, an haife shi a unguwar Hamamonu ta birnin Ankara a shekarar 1968.

Ya kammala karatu a makarantar Sadarwa ta Soji, wato Army Signal School da kuma makarantar Koyar da Harsuna ta Soji, wato Army Language School, sannan ya kammala mafi yawan karatunsa a lokacin da yake aiki a rundunar Sojin Turkiyya [TSK].

A lokacin da yake aiki a kungiyar kawance ta NATO a ketare, Fidan ya samu digiri na farko a Kimiyyar Siyasa da Gudanarwa daga Jami’ar Maryland, bayan haka kuma ya samu digiri na biyu da na uku a fannin Koyar da Huldar Kasa da Kasa a Jami’ar Bilkent.

Bayan aikinsa a TSK, Fidan ya mayar da hankalinsa kan harkar ilimi kuma ya koyar da huldar Kasa da Kasa a jami’o’in Hacettepe da Bilkent a babban birnin Turkiyya, Ankara.

Fidan ya rike muhimman mukamai a hukumomin harkokin kasashen waje da na tsaro.

Ya yi mataimakin karamin sakataren harkokin waje da na tsaro a babbar ma’aikata da kuma hukumar Turkiyya ta ba da tallafi ga kasashe masu tasowa (TIKA).

Ya taba kasancewa daya daga cikin 'yan majalisar gudanarwa a hukumar IAEA ta kiyaye yaduwar makamin nukiliya da wakilin firaminista na musamman da mataimakin karamin sakataren hukumar leken asiri ta MIT da shugaban hukumar MIT da kuma wakilin shugaban kasa na musamman.

Fidan ya yi aiki a matsayin shugaban MIT na shekara 13 tun 27 ga watan Mayun shekarar 2010, kuma Shugaba Erdogan ya taba bayyana mutumin, mai shekara 55, "mai kiyaye asirinsa ".

Yana da aure da ‘ya’ya uku.

TRT Afrika da abokan hulda