Recep Tayyip Erdogan ya kaddamar da sabuwar majalisar ministocinsa a Fadar Shugaban Kasa ta Cankaya bayan ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasa a zauren majalisar dokoki da ke Ankara babban birnin kasar.
Ranar Asabar Erdogan ya sanar da tsohon mataimakin firaiminista Cevdet Yilmaz a matsayin sabon Mataimakin Shugaba Kasa.
Mambobin Majalisar Zarwartarsa su ne:
- Ministan Shari'a: Yilmaz Tunc
- Ministan Ma'aikatar Kula Da Iyali da Walwala: Mahinur Ozdemir Goktas
- Ministan Kwadago da Tsaron Al'umma: Vedat Isikhan
- Ministan Muhalli, Raya Birane da Sauyin Yanayi: Mehmet Ozhaseki
- Ministan Harkokin Waje: Hakan Fidan
- Ministan Makamashi da Albarkatun Kasa: Alparslan Bayraktar
- Ministan Matasa da Wasanni: Osman Askin Bak
- Ministan Bailtulmali da Kudi: Mehmet Simsek
- Ministan Cikin Gida: Ali Yerlikaya
- Ministan Al'adu da Yawon Bude Ido: Mehmet Nuri Ersoy
- Ministan Ilimi na Kasa: Yusuf Tekin
- Ministan Tsaro: Yasar Guler
- Ministan Lafiya: Fahrettin Koca
- Ministan Masana'atu da Fasaha: Mehmet Fatih Kacır
- Ministan Noma da Gandun Daji: Ibrahim Yumakli
- Ministan Cinikayya: Omer Bolat
- Ministan Sufuri da Ababen More Rayuwa: Abdulkadir Uraloglu
An soma 'sabon karni a Turkiyya'
Da yake jawabi yayin rantsar da sabuwar majalisar ministocin, a taron da manyan jami'ai daga kasashe 81 suka halarta, Erdogan ya ce zai gudanar da taron farko da ministocinsa ranar Talata.
"Za mu ci gaba da zama tsintsinya madaurinki daya a yayin da muke gina Turkiyya ta sabon Karni tare da sabuwar majalisar ministoci," in ji shi.
Erdogan ya sha alwashin yin aiki tukuru "domin kare martabar Jamhuriyar Turkiyya da tsare sunanta a duniya a shekaru biyar da ke tafe."
Shugabannin kasashe 50 da firaiministoci 13 da ministoci da wakilai na kungiyoyin kasashen duniya ne suka halarci bikin rantsar da shi, ciki har da wakilan kungiyar tsaro ta NATO, kungiyar kasashen yankin Turkic, da kungiyar hada kan kasashen Musulmai.
Cikin shugabannin da suka halarci bikin har da shugaban kasar Azerbaijan Ilham Aliyev, da na Jamhuriyar Turkiyya ta Arewacin Cyprus Ersin Tatar, da shugaban Venezuela Nicolas Maduro, da Firaiministan Pakistan Shehbaz Sharif da Firaiministan Armenia Nikol Pashinyan.
Tun da farko, Erdogan ya sha rantsuwar kama aiki a zauren majalisar dokoki don yin karin shekara biyar a matsayin shugaban kasar Turkiyya.
Ranar 28 ga watan Mayu ne 'yan kasar Turkiyya suka kada kuri'a a zagaye na biyu bayan da a zagaye na farko na ranar 14 ga watan Mayu aka rasa samun dan takarar da ci fiye da kashi 50 na kuri'un da ake bukata don yin nasara.
Erdogan ya samu kashi 52.18 na kuri'un da aka jefa, yayin da dan jam'iyyar hamayya Kemal Kilicdaroglu ya samu kashi 47.82.