1. Bai wa PKK damar gudanar da ayyuka a kasarta
Duk da Sweden ta bayar da tabbaci ga Turkiyya cewa kasar za ta yi aiki da dokarta ta yaki da ta’addanci tare da dakatar da PKK daga shirya taruka da yin zanga-zangar tsokana da tayar da zaune tsaye, ba wani matakin a zo a gani da aka dauka.
Kuma zanga-zangar nuna adawa da Turkiyya na ci gaba da gudana a kasar.
A watan Mayun 2023, an kafa tutar PKK a jikin ginin Majalisar Dokokin Sweden.
Ana kuma yawan daga hotunan shugaban ‘yan ta’addar da ke daure a kurkuku Abdullah Ocalan a wajen zanga-zangar, inda suke kuma kona hotunan Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.
A ranar 4 ga watan Yuni, magoya bayan PKK sun sake gudanar da zanga-zanga don tankwara Sweden kan ta janye dokarta ta yaki a ta’addanci da ta samar ba da jimawa ba.
Sun yi ta nuna hotunan shugaban ‘yan ta’adda Abdullah Ocalan a yayin da suke kuma yin kalaman batanci ga shugaba Erdogan.
Kusan masu zanga-zanga 1.000 ne suka taru inda ‘yan sanda suka rufe hanyoyi don su samu damar gudanar da zanga-zangar.
Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai sun ayyana kungiyar PKK a matsayin kungiyar ta’addanci ta kasa da kasa, saboda irin ayyukan ta’addanci na hare-haren bam da na kunar bakin wake da suke kai wa fararen hula da jami’an tsaron Turkiyya.
PKK ta kashe sama da mutum 40,000.
2. Mika wa Turkiyya ‘yan ta’addar PKK da FETO
A lokuta da dama Turkiyya ta nemi a dawo da ‘yan ta’addar PKK da FETO zuwa kasar daga Sweden.
A watan Yuni 2022, Turkiyya da Finlan da Sweden sun sanya hannu kan yarjejeniya a Madrid kan batun shiga NATO da kasashen biyu ke son yi.
Yarjejeniyar ta bukaci Finlan da Sweden da su dauki matakai kan damuwar da Turkiyya ke da ita kan yaki da ta’ddanci, ciki har da dawo da ‘yan ta’adda zuwa Turkiyya.
Amma kuma Sweden ta ki dawo da ‘yan ta’addar zuwa kasar Turkiyya.
Mambobin PKK a Sweden na kulla alakar ta’addanci sannan suna kasuwancin muggan kwayoyi, karbar kudade daga hannun mutane ba bisa ka’ida ba, tare da duakar nauyin ta’addanci.
Kotun Sweden ta tabbatar da wadannan tuhume-tuhume da ake yi wa PKK a karon farko a watan Yuni a lokacin da take sauraren karar wani dan ta’addar PKK din.
Mutumin da aka gurfanar a kotu kuma ya tafi gidan maza, ya yi yunkurin karbar kudin haram a ranar 11 ga Janairu ta hanyar amfani da bakin bindiga, harbi a sama da barazanar zai yi barna washegari matukar ba a bas hi kudin fansa ba.
Dadin dadawa ga ‘yan ta’addar YPG/PKK, Sweden ta ci gaba da baiwa ‘yan ta’addar GFethullah FETO izinin zama a kasar, kungiyar ta’addar da ta yi yunkurin kifar da zababbiyar gwamnatin Turkiyya a 2016.
Kungiya ce da ta kasha mutane sama da 250 da jikkata wasu 2,734 a yayin zanga-zangar nuna ada wa da ynkurin juyin mulkin.
3. Bayar da taimakon kudi da makamai ga PKK/PYD
Wani rahoto na musamman da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya buga a 2021 ya bayyana yadda Sweden ke samar da makamai ga ‘yan ta’addar PKK.
Kungiyar ta’addar, kamar yadda rahoton ya bayyana, na harar jami’an tsaron Turkiyya a Siriya a tsakanin 2017 da 2021 ta hanyar amfani da makaman da Sweden ta ba su.
Akwai kayan yaki guda 40 samfurin AT-4 a Sweden ta bai wa ‘yan ta’addar.
AT-4 daya daga cikin manyan kayan yaki da ke da sulken igwa da ake da su a duniya.
Jami’an tsaron Turkiyya sun kwace wadannan makamai a yayin farmakan da suka kai wa ‘yan ta’addar PKK, kuma sun dauki hotunansu daya bayan daya.
Haka kuma, Sweden ta haramta wa kamfanoninta sayarwa da Turkiyya makamai, bayan da Turkiyya ta fara kai farmakai a Siriya da nufin fatattakar ‘yan ta’addar PKK/YPG.
Daga 2019 ne ta janye wannan haramci in da ta dawo da kaowa makaman zuwa Turkiyya.
Sauya wannan ra’ayi na da alaka da niyyar Sweden ta neman shiga Kawancen NATO.
4. Kin daukar mataki kan masu nuna wariya da kyamar Musulunci
Batun kona Alkur’ani mai tsarki a gaban jami’an tsaron Sweden, na daya daga cikin batutuwan da dole Sweden ta gyara matsayinta a kai idan tana son Ankara ta sauya nata matsayin kan batun zama mamban NATO da Stolkhom ke nema.
A lokacin da ‘yan sandan Sweden suka nemi izinin kotu na bayar da kariya ga la’ananne mai kona Alkur’ani Mai Tsarki, kotun daukaka kara ta kasar ta ki amincewa da bukatar ‘yan sandan, amma ta bayar da damar aikata masha’ar da sunan ‘yancin fadin albarkacin baki.
Turkiyya ta yi suka da babbar murya ga wannan ta’annati, inda Shugaban Kasar Recep Tayyip Erdogan yake cewa zai dauki matakin toshe kofar da za ta baiwa Sweden damar zama mamban NATO matukar za ta dinga bayar da dama ana cin zarafin Littafin Musulmai Mai Tsarki.
Erdogan ya ce “Ba za mu amince da bukatar Sweden ta neman zama mamban NATO ba matukar kuna bayar da dmaa ana kona littafinmu na Alkur’ani Mai Tsarki, a yaga shi, sannan a yi hakan karkashin amincewar jami’an tsaronku.”