Erdogan ya tunatar kan irin dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da Pakistan wadanda ya kira ‘yan uwan juna./Hoto:AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jaddada bukatar hada kai domin daukar mataki kan kin jinin addinin Musulunci da kyamar baki a kasashen Yamma.

“Mummunan hari kan littafinmu mai tsarki, Alkur’ani a Sweden a ranar Idin Babbar Sallah na nuna wani nau’i kin jinin Musulunci mai ban tsaro,” kamar yadda ya bayyana a wani bidiyo wanda aka tura wa wani taro karo na 46 na shekara-shekara na Kungiyar Masana Falsafa ‘yan asalin Pakistan da ke a Arewacin Amurka a ranar Asabar.

Erdogan ya jaddada cewa hakkin duka Musulmi ne kiyaye afkuwar irin wannan rashin hankali a nan gaba.

“Dukanmu Musulmai na da babbar rawar da za mu taka domin tabbatar da cewa irin wannan lamari, wanda a Turkiyya muka mayar da kakkausan martani a kansa, bai sake faruwa ba. Idan muka hada kai don daukar mataki da zuciya daya da hannu daya, babu wani a duniya da ya isa ya ci mutuncin Musulmi,” in ji shi.

Erdogan ya kuma kara tunatar da dangantaka mai karfi da ke tsakanin Turkiyya da Pakistan wadanda ya kira ‘yan uwan juna.

Fushi kan wulakanta Alkur’ani a Sweden

Kasashen Musulmi sun yi fushi matuka bayan da wani mutum, wanda kafafen watsa labaran Sweden suka bayyana a matsayin Kirista da ya shiga kasar daga Iraki, ya kona Alkur’ani a wajen Masallacin Stockholm a ranar Babbar Sallah.

Kasar Sweden ta amince da matakin da mutumin ya dauka. Sai dai daga baya ‘yan sandan kasar suka soma gudanar da bincike kan mutumin.

Daga Afirka zuwa Gabas ta Tsakiya da Kudancin Asia, Sweden ta sha caccaka mai zafi daga kasashen Muslmai har ma da wasu Kiristoci.

Dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a Pakistan da Morocco da kuma yi wa jakadunsu da ke Sweden kiranye.

Sa’annan Iran ta yi jinkiri wurin nada sabon jakada zuwa Sweden sa’annan wasu kasashen suka yi Allah wadai da wannan lamari a matsayin zanga-zanga domin martani ga Stockholm.

TRT World