Jami'an Kotun ICC sun koka kan yadda Isra'ila ke yi musu barazana su da iyalansu tsawon lokaci/ / Hoto: Reuters Archive

Daga

Ihsan Faruk Kilavuz

"Ina jaddada cewa duk wani yunkuri na kawo cikas, tsoratarwa ko yin tasiri ga jami'an wannan kotun dole ne a daina nan take."

Babban mai shigar da ƙara na Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC ne ya bayar da wannan gargaɗin a lokacin da ya fito fili ya bayyana shirinsa na bayar da takardar sammaci ga shugabannin Isra'ila da Hamas.

Duk da cewa wannan gargaɗin ya yi kama da maganar shari'a wadda aka saba yi a kowane lokaci, wani bincike da kafafen watsa labarai uku waɗanda suka haɗa da Guardian da +972 Magazine da Local Call suka yi ya gano cewa Karim Khan da gangan ya yi waɗannan kalaman kuma ya jefa su ga ɓangarorin.

Binciken na hadin gwiwa ya gano cewa, manyan jami'an gwamnatin kasar Isra'ila da na tsaron Isra'ila ne suka kitsa wani aikin sa ido na tsawon shekaru tara da suka shafi kotun ta ICC domin dakile binciken laifukan yaki da cin zarafin bil'adama da shugabannin Isra'ila suka aikata.

Ba kamar Kotun Duniya ta ICJ ba wadda ke shari'a kan batun matakan da ƙasa ke ɗauka, ICC tana mayar da hankali ne a kan mutane waɗanda ake zarginsu da aikata laifukan yaƙi.

Haka kuma, ɓangaren na Isra'ila na kallon binciken da ICC ɗin ke son yi kan Isra'ila a matsayin "wata barazana ta nan take" inda kuma Isra'ilar ke son karkatar da ayyukanta kan tsoratar da mutane, inda take son mayar da hankali kan tsohon babban mai shigar da ƙara Fatou Bensouda da kuma wanda yake kai a yanzu Khan.

Aikin da Isra'ilar ke son yi a asirce na kawo cikas ga binciken yana da sa hannun manyan ma'aikatun gwamnatin Isra'ila waɗanda suka haɗa da Ma'aikatar Shari'a da Ma'aikatar Harkokin Waje da Ma'aikatar Leƙen Asiri da kuma ɓangarorin farar hula da na soji.

Persona non grata: Fatou Bensouda

Fatou Bensouda dai ta dade tana fuskantar batanci daga Isra'ila, yayin da ta fara gudanar da bincike na farko da na hukuma kan laifukan yaki da jami'an Isra'ila suka aikata a yankunan Falasdinawa da ta mamaye bayan shigar Falasdinu a kotun ICC.

Bensouda ta ƙaddamar da shirin gudanar da binciken laifukan yaƙi a abubuwan da Isra'ila ta aikata a Gaza a 2014 duk da irin matsin lambar da ta fuskanta daga ɓangaren 'yan adawa na Isra'ila da Amurka.

Babban abin da Tel Aviv take adawa da shi kuwa shi ne tana ganin cewa kotun ba ta da hurumi kan Isra'ila.

Tel Aviv ta jima tana nuna turjiya kan cewa ICC ba ta da hurumin tuhumar Jami'an Isra'ila sakamakon ƙasar ba mamba bace ta Rome Statute, wanda ita ce yarjejeniyar da ta kafa kotun, haka kuma sakamakon Falasɗinu ba cikakkiyar mamba bace ta Majalisar Ɗinkin Duniya.

Duk da haka, an amince da Falasɗinu a matsayin cikakkiyar mamba ta ICC a lokacin da aka sa hannu a 2015, bayan an amince da ita a Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya a matsayin 'yar kallo kuma mamba wadda ba cikakkiya ba.

Jim kadan bayan shiga kotun, hukumar Palasdinawa ta bukaci ofishin mai shigar da kara da ya binciki laifukan da aka aikata a Gaza, da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye da kuma Gabashin Birnin Kudus.

Fatou Bensouda, wadda a lokacin ita ce shugabar mai shigar da ƙarar, ta ƙaddamar da binciken wucin-gadi domin gano cewa ko an cike ƙa'idoji domin gudanar da cikakken bincike.

Matakin da Bensouda ta ɗauka ya ja hankali a Tel Aviv wanda ya jawo Isra'ila ta ɗauki mataki, inda ta tattara sojoji da ƙwararru a ɓangaren shari'a da leƙen asiri, domin kawo cikas ga binciken. Wannan yunƙurin Majalisar Tsaro ta Isra'ila ce ke sa ido a kansa, wanda ke aiki a ƙarƙashin ofishin firaminista.

An bayyana cewa tsohon shugaban Mossad Yossi Cohen shi ne ke jagorantar wannan shirin da ake yi a kan Bensouda, wanda aka soma tun kafin ma ta yanke hukuncin soma gundanar da bincike kan zargin aikata laifukan yaƙi a yankunan Falasɗinu da Isra'ila ta mamaye.

Ɗaya daga cikin matakan sun haɗa da batun taron sirri a tsakaninsu.

A cewar rahoton, aikin na sirri an ce ya samu amincewa daga manyan jami'an gwamnatin Isra'ila, haka kuma katsalandan ɗin da Cohen ya yi a binciken ya wuce katsalandan wanda hakan ya koma barazana kai tsaye ga rayuwarta.

Ya yi amfani da zalunci da barazana a kan Bensouda da iyalanta.

Bugu da ƙari, rahotanni sun ce hukumar leƙen asirin ta aika da barazana ga babbar mai shigar da ƙarar da iyalanta inda suka aika mata da hotunan sirri da suka ɗauki mijinta a lokacin da ya je Landan.

Duk da irin wannan barazanar da Tel Aviv ta ci gaba da yi wa Bensouda, ta ci gaba da tsayawa a kan matsayarta.

A Maris ɗin 2021, dab da lokacin da za ta sauka daga muƙaminta, ta sanar da batun ƙaddamar da bincike a hukumance bayan gudanar da binciken wucin-gadi.

Bayan haka, wa'adin Bensouda a matsayin babbar mai shigar da ƙara ta kawo ƙarshe a Yunin 2021, inda ta miƙa alhakin kama jami'an Isra'ila da aikata laifukan yaƙi a yankunan Falasɗinu ga Karim Khan.

Laifuka dangane da 'aiwatar da hukunci'

Karim Khan ya yi suna a kafafen watsa labarai a 'yan kwanakin nan bayan ya sanar da buƙatar kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da kuma Ministan Tsaro Yoav Gallant.

Bayan ayyana wannan matakin mai muhimmaci kan shugabannin Isra'ila, a cikin sanarwar Khan ya ƙara jaddada cewa ana katsalandan a kan harkokin shari'ar.

Ya bayyana cewa, "Ba zan yi ƙasa a gwiwa ba wurin hukunta duk wani yunƙuri na kawo cikas ko barazana ko kuma ƙoƙarin yin katsalandan ga jami'an kotun ICC ba!"

Khan ya nuna cewa tsarin shari'a na kasa da kasa ba zai tsoratar da haramtattun ayyuka da laifuka da Isra'ila ke amfani da su wajen kawo cikas ga tsarin shari'a ba.

Tel Aviv ta kira ruwa a wannan lokaci inda a halin yanzu take fuskantar ƙarin yiwuwar ƙarin wani binciken a ƙarƙashin sashe na 70 a kudin Rome Statute.

Sashe na 70 mai taken "laifuka dangane da aiwatar da hukunci," yana magana a kan katsalandan da nufin kawo cikas ko ƙoƙarin yin tasiri a tsarin bincike da tsarin shari'a a matsayin laifuffukan da za a hukunta su, tare da tabbatar da kiyaye waɗannan shari'o'in.

A kan wannan lamarin, irin wannan barazanar da Isra'ila ke yi ga kotun ta faɗo a ƙarƙashin hurumin ICC wanda aka bayyana a sashen: Ayyuka kamar katsalandan, tsoratarwa, ko ƙoƙarin yin tasiri a tsarin bincike domin hana su gudanar da ayyulansu yadda ya kamata za a hukunta su.

Haka kuma, Khan ya jaddada cewa kotun tana da ƙarfi, inda ta bayyana cewa za ta yi tsayin daka kan laifuffukan da suka shafi gudanar da adalci

Dalilin da ya sa ya kamata a samu adalci a duniya

Yakin da Isra'ila ke yi da Falasdinawa ba bisa ka'ida ba ya daɗe da rikidewa zuwa "yaki da dokokin kasa da kasa da kanta".

Ana ci gaba da saka ayar tambaya dangane da matsayin Tel Aviv na cewa "ta fi ƙarfin shari'a". Don hakar kasar ta yahudawa ta kara kaimi ga ayyukanta da ke karya dokokin kasa da kasa. Sabuwar dabararta ita ce: "Idan babu dokar kasa da kasa, babu keta."

Dangane da haka, Isra'ila, wadda a baya ta yi ƙoƙari ta tabbatar da cewa ayyukanta na cikin "cikin iyakokin doka" don mayar da martani ga zarge-zargen "ketare", yanzu ba ta jin bukatar irin wannan hujja, har ma da "fatalwa" hukumomin shari'a na kasa da kasa, kamar yadda. gani a kisan kiyashin da ta yi kwanan nan a Rafah duk da hukuncin da ICJ ta yanke.

TRT World