Daga Jianlu Bi
Matakin shugaban Amurka Donald Trump na sanya harajin kaso 25 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigo wa da su daga Canada da Mexico da kuma harajin kaso10 cikin 100 kan kayayyaki daga China, ya fusata duniya tare da haifar da martani na yaƙin kasuwanci.
Bayan wasu 'yan kwanaki da yin hakan ne China ta mayar da martani, inda ta ɗora harajin kashi 15 cikin 100 kan albarkatun gawayi da kuma gas ɗin Amurka da kuma harajin kashi 10 kan wasu kayayyakin, wanda zai fara aiki daga ranar 10 ga watan Fabrairu.
Kazalika Trump ya kakaɓa wa Mexico da Canada haraji, sai dai ya dakatar da aiwatar da matakin da wata ɗaya bayan wata tattaunawar gaggawa da ya yi da kasashen biyu waɗanda ke makwabtaka da juna.
Ita ma ƙungiyar Tarayyar Turai ta kuduri aniyar mayar da martani bayan barazanar da Trump ya yi na sanya wa ƙasashe 27 mambobin ƙungiyar irin wannan haraji.
Dabarar tunzurawar da Amurka ta ɗauka na nuna wani babban sauyi a harkokin cinikayyar duniya, wanda ka iya janyo mumunar haɗari, ba wai ga Amurka kadai ba har ma da dorewar tsarin tattalin arzikin ƙasa da ƙasa.
Wani masanin tattalin arziki na Amurka kana farfesa a jami'ar Columbia Jeffrey Sachs ya bayyana damuwarsa game da waɗannan dabaru na ƙasar, yana mai kwatanta hakan da ''yaudara mai illa ga tsarin mulkin Amurka'' tare da gargadin cewa wannan tsari na kariya zai iya lalata tattalin arzikin duniya ba wai na Amurka kadai ba.
Ko da yake dai, wannan yanayin ya bai wa China damar faɗaɗa tasirin dabarunta da kuma yiwuwar sake fasalin tsarin tattalin arzikin duniya.
Caca da ke cike da haɗari
Dalilan gwamnatin Amurka na sanya haraji sun kashi zuwa fuskoki da dama. Tana da kudurin magance rashin daidait a kasuwanci tare da kare masana'antu na cikin gida da kuma tunkarar abin da ta dauka a matsayin rashin adalcin cinikayyar sauran ƙasashe.
Alal misali, Amurka ta sha yin nuni kan gibin cinikayyarta da China, wanda ya kai dala biliyan 382.9 a shekarar 2022, a matsayin babban hujja ga manufofin cinikayyarta.
Tana mai bayyana jadawalin kuɗin fito a matsayin mai mahimmanci wajen ''daidaita kasuwa'' da kuma ƙarfafa masana'antu na ciki gida.
Ko da yake, tasirin jadawalin kuɗin fito don cimma waɗannan buƙatun yana ci gaba da haifar da muhawara.
Ka’idar tattalin arziki da shaidu na tarihi sun nuna yadda sau tari da dama kakaba haraji ke janyo matakan ramuwar gayya, wanda a wasu lokutan kan rikide zuwa yakin kasuwanci da ke shafar ko wane bangare da abin da ya shafa.
Tarihi yana ba da gargaɗi mai ƙarfi, kamar dai dokar Amurka kan haraji ta ‘’Smoot-Hawley a shekarun 1930, wacce ta kakaba manyan haraji da ya girgiza tsarin kariya zuwa ga mumunar sakamako.
Lamarin da ya hada da rugujewar kasuwancin ƙasa da ƙasa, tare da tarbarbarewar alaƙar zaman lafiya tsakanin ƙasashe, haka kuma musamman zuwa ga yakin duniya.
Daya daga cikin wannan misali shi ne, yakin kasuwanci tsakanin China da Amurka na shekarar 2018 zuwa 2019.
Amurka ta sanya harajin biliyoyin daloli kan kayayyakin China, lamarin da ya sa ita ma Beijing mayar da martani da kakaba haraji kan kayayyakin Amurka, ciki har da kayayyakin amfanin gona kamar waken soya.
Sakamakon hakan ya haifar da ƙarin farashi kayayyakin amfani daban-daban na Amurka, tun daga kan na'urori zuwa tufafi, inda hakan ya matukar tasiri kan manoma Amurkawa waɗanda kayayyakin da suke fitarwa zuwa China ya ragu sosai.
Wani bincike da babban bankin Amurka ya yi, ya kiyasata cewa yakin cinikayya ya rage yawan kudaɗen shigar kasar na GDP da kusan kashi 0.3, wanda ya yi daidai da asarar dala biliyan 62 da aka yi.
Kazalika, bayanai sun yi nuni da cewa yaƙin cinikayya ya samar wa kamfanonin Amurka aƙalla dala tiriliyan 1.7 a darajar kasuwar hannun jari da kusan ayyuka 300,000.
Yunkurin Trump na amfani da kuɗin fito ko haraji a matsayin makamin yaki a dabarun tattalin arziki na ƙasa da ƙasa babban caca ce da ke cike da haɗari da ke barazana wajen raba ta da ƙawayenta tare da rage ƙimar hukumomin kasashen duniya kamar ƙungiyar cinikayya ta duniya (WHO) da amincin Amurka a matsayin wadda ake dogaro da ita a fannin kasuwancin duniya.
Rikicin kasuwanci na baya bayan nan da ƙungiyar Tarayyar Turai kan harajin tama da karafa ya sanya matsin lamba kan dangantakar dake tsakanin ƙasashen da ke yankin Tekun Atlantika tare da haifar da damuwa game da makomar tsarin cinikayyar duniya.
Dogaron da Amurka ta yi kan harajin ya rage karfinta wajen jagorantar batutuwan da suka shafi cinikayyar duniya kana hakan ya buɗe kofa ga sauran ƙasashe kamar kasar China wajenbayyana tasirinsu a tsara makomar cinikayyar kasashen duniya.
Wata dama ga China
A wannan koma baya da aka fuskanta na rikicin kasuwanci, China ta samu kanta a wani matsayi na musamman da za ta iya cin moriya tare da ciyar da kanta gaba wajen sake fasalin tsarin duniya.
Manufar tsarin harajin Amurka mai ya haifar da gibi a jagoranci na harkokin cinikayyar ƙasashen duniya, wanda a yanzu haka China ke da burin cikawa.
Ci gaban karfin tattalin arzikin China da kuma yadda take son yin cudanya da kasashe bisa sharuddansu ya sa ta zama babban abokiya da ke daukar hankali, musamman ga kasashe masu tasowa.
A yanzu haka, Beijing ce babbar abokiyar cinikayya tsakanin ƙasashe 140 da yankunansu.
A yankin Latin Amurka China ta zama babbar abokiyar cinikayya ga kasashe da dama, sannan a jere a cikin shekaru 15, birnin Beijing ya kasance babbar abokiyar cinikayya da kasuwanci mafi girma a Kudancin Amurka.
Alƙaluma sun nuna cewa, a shekarar 2023 yawan cinikayyar da ke tsakanin ƙasashen biyu ya kai dalar Amurka biliyan 181.53, inda Brazil ta zama ƙasa ta farko a yankin Latin Amurka da ta zarce dala biliyan 100 wajen fitar da kayayyaki zuwa China.
Yayin da Amurka ke janyewa daga matsayinta na jagoranci, China na shirin taka rawa a wannan bangaren don samar da wasu hanyoyin samun ci gaba da haɗin gwiwar tattalin arziki.
Shekaru masu zuwa za su taka muhimmiyar rawa wajen tantance ko China za ta iya samun nasarar yin amfani da wannan dama da kuma tabbatar da matsayinta na kan gaba a karni na 21 da ake ciki.
Marubuci: Jianlu Bi mai sharhi ne kan al'amuran yau da kullum da ke zama a Beijing. Aikin bincikensa ya haɗa da siyasar duniya da sadarwa.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.