A yayin da ake da damar maye gurbin shugabannin da aka kashe, ba lallai a yi saurin mantawa da sanadin mutuwar tasu ba. . / Hoto: AFP

Daga Jasmine El-Gamal

Bayan kisan gillar da Isra'ila ta yi wa jagoran siyasar Hamas, Ismail Haniyeh a Iran da sanyin safiyar ranar 31 ga watan Yuli, yankin Gabas ta Tsakiya yana shig wani yanayi na shirin ko-ta-kwana.

Shugaban addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya lashi takobin "yin zazzafan hukunci" kan abin da ya kira "gwamnatin masu tsattsaurar aƙidar son kafa ƙasar Isra'ila". A halin da ake ciki, Amurka ta ce ba ta da masaniya game da harin tun da farko.

Idan aka yi la’akari da yadda tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya ke ƙara ta’azzara bayan harin da aka kai wa Isra’ila a watan Oktoba da kuma yaƙin da kasar take yi a Gaza, ana iya kallon kisan Haniyeh ta daya daga cikin hanyoyi biyu: ko dai a matsayin wani yunƙuri na ƙarfi da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi na tabbatar da cewa zai iya kawo karshen yaƙin ta hanyar yin "nasara", inda zai cika baki da haɓaka ƙimarsa mara kyau a gida; ko kuma a matsayin wata alama ta ƙara rauni da keɓewar Isra'ila.

Nazarin da ke fitowa daga yankin na nuna cewa ga alama hanya ta biyun ce aniyar tasa.

Ta'azzarar yaƙi

Haniyeh yana cikin tawagar masu shiga tsakani a tattaunawar tsagaita wuta. Mutuwarsa a hannun ɓangaren 'yan adawa da ake fafata yaƙin da su wato Isra'ila, ga alama za ta ƙara tunzura ƙungiyar Hamas da kuma jawo tsaiko daga ɓangarenta wajen samun mafita a tattaunawar zaman lafiyar, ko kuma mafi muni ta ma wargaje baki ɗaya.

A wani taron manema labarai bayan kisan gillar, Netanyahu bai ce komai a kan lamarin ba amma ya ce zai ci gaba da yaƙin kuma ba zai bari matsin lambar cikin gida ko ta ƙasashen duniya su sa ya daina ba tare da ya cim ma abin da yake so ba.

Firaministan ya kuma cewa Isra\ila a shirye take ga duk wani lamari da ka iya tasowa, yana mai cewa ba shi da niyyar bayar da kai a tattaunawar tsagaita wutar ko kuma dakatar da yaƙin wanda zuwa yanzu ya yi sanadin rayukan dubban Falasɗinawa da kuma na aƙalla mutum 70 da ake garkuwa da su.

A yanzu Isra'ila na fuskantar barazanar hare-haren soji daga Iran da ma Hamas wadanda duk suka sha alwashin yin ramuwar gayya da ɗaukar fansar ran Haniyeh, sannan a Labanon shugaban Hizbullah Hassan Nasrallah ya ce ƙungiyar za ta rama kisan gillar da Isra'ila ta yi wa babban kwamandanta Fuad Shukr.

Har ila yau, da wuya idan kisan jiga-jigan shugabannin kungiyoyi irin su Hamas da Hizbullah ba tare da yin la'akari da tushen wanzuwarsu da kiraye-kirayen da ake ba, a zahiri ya raunana azamar kungiyoyin da ƙarfinsu da goyon bayan da suke samu daga jama'a.

A yayin da ake da damar maye gurbin shugabannin da aka kashe, ba lallai a yi saurin mantawa da sanadin mutuwar tasu ba.

Kira ga kwantar da hankali

A hannu guda kuma, sauran ƙasashe sun yi saurin fara yin kira da a kwantar da hankula, inda mataimakin wakilin Japan a Majalisar Dinkin Duniya yake gargadi a wajen wani taron gaggawa na MDD bayan kisan gillar da aka yi wa Haniyeh da Shukr cewa yankin ka iya "faɗawa cikin yaƙi gadan-gadan."

A wajen taron dai kuma, jakadan Birtaniya a MDD ya yi kira ga a sabunta tsarin samar da zaman lafiya, yana mai cewa "ita hanyar zaman lafiya dole a samar da ita ta tattaunawar diflomasiyya" kuma "samar da zaman lafiya na dogon zango ba zai yiwu ta tayar da bama-bamai da harbe-harbe ba."

Shi ma mataimakin jakadan Amurka a MDD ya ce Amurka za ta "ci gaba da aiki tuƙuru don hana ɓarkewar yaƙi a faɗin yankin, wanda zai fara da cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta ba tare da ɓata lokaci ba ta hanyar sakin waɗanda ake garkuwa da su a Gaza.

Tashin hankali da fito-na-fiton da ake yi tsakanin Isra'ila da Iran ya fara ne wata uku da suka wuce bayan da tuni ƙasashen biyu suka sa yankin ya kusa faɗawa yaƙi gadan-gadan.

A ranar 1 ga watan Afrilu ne Isra'ila ta kai hari kan wata harabar ofishin jakadancin Iran a Syria, har wani babban Kwamandan Rundunar Juyin-Juya Hali ta Iran (IRGC) ya rasa ransa, lamarin da ya jawo Iran ta kai wani hari da ba a taɓa ganin ba kwana biyar bayan hakan, da ya haɗa da harba makamai masu linzami fiye da 300 da ƙaddamar da jiragen yaƙi marsa matuƙa zuwa Isra'ila daga iran da Iraƙi da Yemen.

Dangerous cycle

Duk da cewa dukkan ɓangarorin tun watanni 10 da suka wuce sun bayyana cewa ba sa son fara yaƙin da zai shafi yankin duka, duk wani hari da aka kai da na ramuwa da aka mayar na ƙara barazanar da za ta jefa Gabas ta Tsakiya a yaƙi ne sosai.

Idan har hakan ta faru, to ba mamaki a samu wani yanayi da zai munana rikicin fiye da yadda za a iya shawo kansa, da sanya miliyoyin mutanen yankin cikin gagrumar matsala.

A yanzu dai kallo ya koma kan ganin abin da Iran za ta yi. Yayin da ake da tabbacin cewa Khamenei da abokan hulɗar Iran a yankin za su mayar da martani ko ma ta yayya ne kan kisan gilla biyun da Isra'ila ta yi, za su iya zaɓar yin hakan ta wani salo da yake a taƙaice kuma da za a iya shawo kansa.

A response should be significant enough for Iran, Hamas and Hezbollah to save face while not going so far as to draw Israel in further. Whether they can strike that balance remains to be seen.

Ya zama wajibi Iran da Hamas da Hezbollah su mayar da martani domin kare ƙimarsu amma kada martanin ya zama wanda zai harzuƙa Isra'ila ta sake yin wata sabuwar ɓarnar. Sai dai za a duba ido a gani ko za su iya yin hakan.

Yanzu, fiye da kowane lokaci, ya zama tilas shugabanni masu sauƙin kai su yi wani yunƙuri, kuma masu mulki na ƙasashen waje su yi aiki tare da ɓangarorin da abin ya shafa don ja da baya daga ƙangin da ake ciki da kuma ceto al'ummar yankin da tuni suka gaji da kashe-kashe da wahalhalu.

Dole ne shugabannin Isra'ila su fahimci gaskiyar cewa babu wani adadin hare-haren soji da zai sa ƙasarsu da al'ummarsu su kasance cikin aminci a tsawon lokaci.

Rashin sadaukar da kai ga samar da zaman lafiya a siyasance, ba abin da hakan zai yi sai sake raunana yanayin da sa wa a manta da shi.

Duk wata hanya da za a bi da ba ta diflomasiyya ba za ta iya zama mai haɗari.

Marubuciyar maƙalar, Jasmine El-Gamal mai sharhi kan harkokin tsaron ƙasa ce kuma tsohuwar mai ba da shawara ta Gabas ta Tsakiya a Pentagon. Ita ce ta kafa kamfanin Mindwork Strategies, LTD, kamfani mai ba da shawara tare da manufa don taimaka wa ƙungiyoyi su kirkiro hanyoyin tausayawa da hanyoyin al'adu ga manufofin waje da sadarwa da kula lafiyar kwakwalwar mutane a wurin aiki.

Togaciya: Dukkan ra'ayoyin maƙalar na mawallafiyar ne ba na TRT Afrika ba.

TRT World