Donald Trump yayin da yake magana tare da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a wajen Taron Tattalin Arziƙin Duniya (WEF) na shekara a Davos, Switzerland ranar 25 ga Janairun 2018. / Hoto: Reuters/Carlos Barria

Daga Gokhan Batu

Sake zaɓar Donald Trump a matsayin shugaban ƙasa ranar 5 ga Nuwamban 2024, ba a tsammanin zai sauya goyon bayansa ga Isra’ila.

Sai dai kuma, alaƙarsa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ba za ta zama mai ƙarfi kamar yadda take a wa’adin mulkinsa na farko ba.

Baya ga haka, Gabas ta Tsakiya da shi kansa Netanyahu, ba irin yadda suke lokacin da Trump ya bar mulki suke a yanzu ba.

A yayin da rikici a dangantakar Amurka da Isra’ila ya yi karfi, Netanyahu ya fuskanci kalubale da dama da gwamnatin Biden tun watan Janairun 2023, tun daga Dokar Kwaskwarima ga Tsarin shari’a, zuwa ga mamaya ba bisa ka’ida ba a Yammacin Kogin Jordan.

A wannan lokaci, ya samu nasarar jure wa ‘yan democrat, kuma a wasu lokutan yana amfani da tirjiyar tasa a matsayin dabarun siyasa na cikin gida.

Amma kuma, idan aka kalli salon mulkin Trump a wa’adin farko, za a iya cewa Netanyahu na iya fuskantar kalibale wajen dorewar wannan abota.

Haka zalika, bayan yaki ya lafa ne za a fahimci ko akwai Netanyahu mai karfi da zai iya dakatar da siyasar Isra’ila a lokacin da hakan ya zama tilas.

Rashin gasgata juna tsakanin shugabannin biyu ya bayyana ne a matsayin babban lamari a wannan gaba, a lokacin da Trump ke yin tawaye ga sakamakon zaben shugaban kasa na 2020, Netanyahu ya taya Biden murna a wani sakon bidiyo - abinda Trump ya kira rashin biyayya.

Karfin Trump, raunin Netanyahu

Bayan zabuka biyar tun 2018, a kuma lokaci ma tikicin siyasa - ciki har da shekara guda a matsayin dan adawa - Netanyahu ya dawo kan mulki a karshen 2022 sakamakon bayar sa dama masu tsaurin ra’ayin addini su shiga majalisar dokoki ta knesset.

Amma kuma, matsayinsa ya kasance mai rauni saboda rikicin shari’a da ake ci gana da yi kan hotonsa na ‘mai samar da tsaro’ bayan harin 7 ga Oktoba.

Netanyahu ya karfafa lura da damuwa kan bukatar da kawancensu ke da ita, kan waye gwamnatinsa za ta dogara da shi, sannan a wasu lokutan yana kawo rarrabuwar kai a jam’iyyar Likud.

Sakamakon haka, Netanyahu a yanzu na kan kujerar shugaba wanda iya tsira saga tarkon siyasa a Isra’ila. Ya fuskanci kalubale da dama a cikin gida, ya san cewa a yayin da 2025 ke karatowa, za a samu matsin lamba game da zabe, kuma duk da jinkiri, dole ne a yi bincke kan matsalar tsaron da ta janyo harin 7 ga Oktoba.

Kazalika, guguwar gwagwarmayar ‘yan adawa da ta faro a 2023, ta ci gaba inda a yanzu ta rikide zuwa gwagwarmayar neman kubutar da fursunonin yaki.

Karancin zabi kan manufofin kasashen waje

A bangaren manufofin harkomin waje, zabin da Isra’ila ke da shi ya ragu sosai tun tsakiyar shekarun 2010.

A wancan lokacin, Netanyahu na da fahimtar juna da Putin, inda suka dinga kulla alaka da dabarun aiki, kamar fadada dangantaka da China da ayyuka irin su fadada tashar jiragen ruwa ta Haifa karkashin kulawar China.

Sai dai kuma, saboda ‘yar alakar da ke tsakanin Amurka da Isra’ila, wannan mataki na tuntubar bangarori da sama bai samu dawwama ba.

Bayan harin 7 ga Oktoba, manufofin kasashen waje na Isra’ila sun karkata kacokan ne ga Amurka, musamman wajen hadin kan tsaron kasa. Kari kan hakan, tun wannan lokaci, kokarin aiki da Yarjejeniyar Abraham a zamanin mulkin Trump da kokarin fadada sasantawa sun fuskanci cikas sosai.

Akwai ra’ayi sosai kan yadda manufofin Amurka kan iya sauya wa a matakin duniya da yankuma, musamman a bangarorin da rikici ya shafa.

A yayin da wannan ne wa’adinsa na karshe, kuma duba ga irin abubuwan da suka faru a baya, ciki har da kalubalen Covid-19 - Trump zai fara wannan sabon wa’adi da karfin gaske.

Wannan na iya yin tasiri kan manufofinsa a yankuna, tare sa mayar sa hankali ga yake-yaken da ya yi alƙawarin kawo karshen su.

A matsayin shugaban da a baya ya hada kai da Netanyahu, Trump ya taka muhimmiyar rawa a ayyukan cigaba da dama da ke da manufar rage nuna wariya ga Isra’ila a yankunan duniya.

Mayar da ofishin jakadancin Amirka zuwa Jerusalem, amincewa da ‘yancin kasar Isra’ila kan mamaye tsaynukan Golan na Syria.

Da Yarjejeniyar Accord. Wadannan ne ke karfafa gwiwar matsayin Netanyahu, suna ba sho damar karfi a mulki. Za a iya cewa wadannan nasarori sun bayar da gudunmowa sosai ga yadda jam’iyyar Likud ke samun kujeru da dama a majalisa a lokacin da ake ta rikicin siyasa har zuwa 2023.

Rikitacciyar abokantaka da Netanyahu

Rashin iya hasashen me Netanyahu zai yi, ya sanya shi zama abokin da shugabannin Amurka ba za su amince da shi ba, musamman a yayin da burin Isra’ila ya sha bamban sa bukatar Amurka a yankin.

Yayin sa yake amfani da salon alakar Amurka da Isra’ila, Netanyahu na kubutar da siyasar cikin gida ta hanyar tsirurutar dai da rashin jituwa tsakanin kasarsa da Amurka.

A lokacin da ‘yan adawar Amurka suka yunkuro, sai ya tashi yana nuna shi me kare bukatun Isra’ila. Idan ra’ayin kasashen ya zo daya, sai ya dinga numa ai ya samu babbar nasara.

Wannan fuska biyu na taimaka wa Netanyahu wajen ci gaba sa yin farin jini ba tare sa duba fa illar alakar ba.

Misali, a lokacin yakin neman zaben 2019, ya numa hadin kansa ga Biden da Putin, kuma bayan 7 ga Oktoba, ya bayyana kansa a matsayin mai kare muradun Isra’ila, duk da cin kari da Biden game da tsagaita wuta a Gaza.

A nan Netanyahu ya yi allawarurruka da dama ga gwamnatin Amurka, hakan na sanya Biden sanar da shirin tsagaita wuta.

Sai dai kuma, sanarwar da Netanyahu ya dinga fitarwa yana nuna adawa ga wasu sharuddan tsagaita wutar ya jefa Biden cikin tsaka mai wuya.

Dadin dadawa, Netanyahu ya bayani marasa kyau bayan duk an kammala shirya komai.

Duba ga salon mulki na Trump, akwai yowuwar ba zai lamunci yaudarar Netanyahu ba a wannan karon.

Dabarun Netanyahu na ba shi damar jan hankalin jama’a a cikin gida, a gefe guda kuma yana dakile yunkurin Amurka, tare da bata sunan shugaban kasa, ba zai samu karbuwa ba a karƙashin Trump.

Alkawarin kawo karshen yaki?

Ba tare da kallon wacce gwamnati ce ko waye shugaban kasa ba, ba a tsammanjn za a samu wani ragi a alakar Amurda Isra’ila ko a tallafin da Amurka ke baiwa Isra’ila.

Sai dai kuma, Trump ba shugaban da zai bari a yi masa irin cin kashin da Netanyahu ya yi wa Biden ba.

Za a iya cewa, a yayin da wa’adin Trump na biyu ba lallai ya farantawa Falasdinawa ba, Netanyahu na iya fuskantar tasgaro.

Wata babbar gaba a yakin neman zaben da Trymp ya yi ita ce; kawo karshen yake-yake, inda wannan zai zama babban batu a manufofinsa na kasashen waje.

Duba ga shuhurar sa ta yi a fagen kasa da kasa, gwamnatin Trump na iya daukar matakai a kan wannan layi.

Asalin batun shi ne, shin wanne yaki ne zai kawo karshe - watakila wannan kalibale ne ga Netanyahu.

A yayin da ake ganin tasiri a aikace na matsayin tlTrump na “kawo karshen yaki”, a sannan ne za a fahimci yadda alakarsa da Netanyahu za ta kasance.

Kawar da batun goyon bayan Isra’ila daga Netanyahu

Ko ma dai yaya ne, akwai yiwuwar Trump ya dauki matakin kalubalantar Netanyahu a wannan sabon zango na mukkinsa.

A yayin da ba a tsammanjn Isra’ila ta dinga aiki dari bisa da ri da me Amurka za ta ce, za a iya sa fan za ta fuskanci matsin lamba.

A wajen Trump, raba goyon bayan Amurka ga Isra’ila daga Netanyahu na iya zama magakin kawo gyara, wanda hakan zai sauya akalar yadda zai mu’amalanci Isra’ila da Netanyahu.

A wannan gaba, kwaskwari ga majalisar ministpci da Netanyahu ya yi kwanan nan - ya maye gurbin Gallant da Istael Katz a matsayin ministan tsaro - ana iya yi wa hakan kallon wata dabara ta salon mulki.

Sai dai kuma, a watanni biyun da ke tafe kafin rantsar da Trump, halin da Isra’ila ke ciki a sahun yaki na iya yin tasiri kan wannan dangantaka.

Saboda haka, a yayin da ba a hasashen ganin Trump ya zama kamar yadda ya kasance a lokacin mulkinsa na farko, yadda yakin zai kasance zai zama babban jigo wajen fayyace zurfin sauyin alakar Trump da Netanyahu.

Marubucin, Gokhan Batu mai nazari ne kan Isra'il a a sashen Department at ORSAM (Center for Middle Eastern Studies). @_Gokhan_Batu

Togajiya: Ra'ayoyin da marubucin ba sa wakiltar ra'ayoyin editocin TRT Afrika ba.

TRT Afrika