Shugaban Addini na Iran Ali Khamenei ya yi jawabi a wajen taro a Tehran, Iran a ranar 27 ga Oktoba, 2024. / Photo: Reuters

Daga Mahmoud Shaaban

Hare-Hare ta sama da ake sa ran Isra'ila za ta kai wa Iran, wanda ta kai a karshen makon na na iya tirsasa wa Iran shiga yaki kai tsaye a yankin.

Hare-haren sun sauka kan muhimman kayan Iran, ciki har da garkuwar makamai masu linzami da ke iyakar Iraki a Ilam da kayan makamai masu linzami, da yankin da a baya yake da alaka da burin samar da nukiliya na Iran, duk da dai ta bar wajen a 2003.

Kafar watsa labarai ta Iran ta nuna yadda aka dinga tare makamai masu linzami na Isra'ila, wani sako da ke sake tabbatar karin tantamar jama'ar Iran da ke tambayar manufar yakin da kuma irin zuba jarin da Iran din ta yi a Iraki da Lebanon.

Amma a wajen Iran, lamarin ya haura batun tasiri a yankin. Cakuduwar matsalolin soji, diplomasiyya, da tsarin rayuwa sun sanya kasar ama cikin raba daya biyun shiga sahun gaba a yaki, wanda har zuwa yanzu take yin sa ta hanyar wakilanta na filin daga.

Yadda lamarin ya faro

Shugabannin Iran sun fara fahimtar cewa harin da Hamas ta jagoranci kai wa Isra'ila a ranar 7 a Oktoba zai iya yaduwa da yin tasiri a dukkan yankin bayan mutuwar shugaban Iran Ebrahim Reisi da Ministan Harkokin Wajen Amir Hossein Abdollahian.

Ma'aikatan ceto bayan fadowar jirgin sama mai saukar ungulu da shugaban Iran Ebrahim Resisi ke ciki a Varzaqan, Gabashin lardin Azabaijan, Iran a eanar 20 ga Mayu, 2024. (Reuters).

Bayan jami'an sun rasu a hatsarin jirgin sama a Gabashin Azabaijan a watan Mayu, an dinga samun jita-jita a tsakanin masu ra'ayin rikau da masu son kawo sauyi a fagen siyasar Iran game da lamarin.

Duk da ikirarin jami'an gwamnati na cewa "hatsari ne da munanar yanayi ya janyo", wasu manyan jami'an Iran sun gamsu da cewa gwamnatin Isra'ila na da hannu wajen kitsa hatsarin jirgin saman mai saukar ungulu.

Zargin ya fi karfi a sahun manyan jami'an gwamnatin Iran, da wadanda suke filin daga da wadanda suke ofis, inda suke kara rura wutar cewa wannan abu na sunkuru da Isra'ila ta aikata na da manufar janyo Iran cikin yakin da ba za ta iya yin biris da shi ba.

Sai dai kuma, jami'an gwamnatin Iran sun dakatar da bayyana wannan sanarwa, inda suke cewar zargi daga jami'an na iya matsa lamba ga Iran, saboda hakan ne abin da jama'ar Iran, kawayensu sojoji da ke Lebanon, Iraki, Syria da Yemen suke tsammata a matsayin martani ga kisan Raisi da Abdollahian.

Jami'an Iran na tsoron irin wannan martani, na iya kai su ga yaki gaba da gaba da Isra'ila.

A tattaunawar boye da muka yi da wasu na cikin gida a tsakanin masu jagorantar Iran, a bayyane take karara cewa Tehran ta so yin zaben wuri don daidaita al'amura bayan mutuwar Raisi, sannan ta magance matsalar tattalin arzikin kasar, wadda lamarin ya karara ta'azzarawa.

Iran ta gudanar da zaben shugaban kasar cikin kwanaki 40 bayan mutuwar Raisi, inda suka kawo Maoud Pezeshkian ofis a watan Yuli. Amma, makonni kadan bayan hakan, a wani yanayi mai ban mamaki, Isra'ila ta kashe shugaban siyasar Hamas, Ismail Haniyeh a tsakiyar birnin Tehran, a daya daga yankunan da suka fi kowane tsaro a kasar.

A wannan lokaci, an tirsasa Iran sake tunanin matsayinta, wanda ya dade bisa doron goyan bayan kawayenta a yankin, inda ba ta nuna shiuga sahun yaki gaba da gaba.

Barin yaki a sahun gaba

A martanin d ata mayar, Iran ta fara duba yiwuwar dukar sabbin matakai, ta bar manufa irin wadda ta samo assali daga yakin Iran-Iraki na tunkarar makiya gaba da gaba, inda sabon tsarin ya fi fifita karfafa wa wakilar da ke wajen Iran su kalubalanci makiyanta na tarihi, Isra,ila da Amurka.

Babu wanda ya yi tsammanin kai hari kai tsaye a kasar Iran

Majiyoyina sun bayyana cewa - 'yan cikin gida da ke da kusanci sosai da gwamnati - ko shugaban addinin Iran Ali Khamenei ko masu ba shi shawara, babu wanda ya taba tunanin Firaministan Isra'ila zai kawo yakin da take yi zuwa ga iyakar kasarsu.

Shugabannin Iran sun yi tsammanin cewa Isra'ila za ta takaita hare-harenta ne ga wakilan Iran da ke kasashen waje, ciki har da Hezbollah a Lebanon, sojojinta a Syria, da mayaka 'yan Shi'a da Iran ke mara wa baya a Iraki. Babu wanda ya yi tsammanin za a samu hari kai tsaye a kan kasar Iran.

Iran ta umarci Hezbollah karara kan ta nisanci yakin gaba da gaba da Isra'ila, tana mai karfafa cewar a madadin haka ta din ga kai hare-hare iyakokin arewacin Isra'ila.

Amma wannan mataki ya sauya bayan kisan Sakatare Janar na Hezbollah, Hasan Nasrallah a watan da ya gabata, da kuma hare-haren da aka kai Lebano da Syria da suka taba zuciyar Iran.

Dogaro kan mayaka da ke wajen kasar, na raunata karfin Iran a yankin, yana bayyana ta a matsayin mai rauni a tsakanin makiya da kawayenta na tsawon lokaci.

Tafiya zuwa filin daga

Kafin ayyana yaki kai tsaye da Isra'ila a yankin, Iran ta fara neman goyon bayan diflomasiyya daga kawayenta na yankin da ma duniya baki daya, tana bayyana halascin matakin da za ta dauka.

Sannan sai Iran ta ayyana shiga filin daga a Satumba, hakan ya zama matakinta na farko na sauya fasalin harkallar yankin, sabanin burin Netanyahu.

An ga makamai a sararin samaniya bayan Iran ta harba makamai masu linzami na salvo, a lokacinda da ake samun kai hare-hare tsakanin Hezbollan da Tel Avivm a ranar 1 ga Oktoba, 2024.

An ga makamai a sararin samaniya bayan Iran ta harba makamai masu linzami na salvo, a lokacinda da ake samun kai hare-hare tsakanin Hezbollan da Tel Avivm a ranar 1 ga Oktoba, 2024.

Bayan matakin ramuwar gayya na farko na Iran, wanda ya hada da hara daruruwan makamai masu linzami zuwa Isra'ila, Netanyahu ya yi barazana sosai na "daukar matakin ramuwa mai girma".

Matakin siyasa na Iran wajen mayar da martani ya dinga daduwa, karkashin jagorancin shugaban addini Ali Khamenei, wanda kuma majalisar dokoki da jami'an kare hakkokin dan ada suka goyi baya da kara amonsa, wanda suka nuna adawa ga yin sako-sako ko wasa da martanin Isra'ila.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya yi wasu kalamai masu zafi, yana mai alkawarin za su dauki batun zuwa Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya don neman a hukunta isra'ila, inda yake kuma jaddada karfin ikon Iran na kare kanta a ciki da wajen kasar.

Da fari dai bayan 7 ga Oktoba, Iran ta yi nasarar yakin raunata abokan gaba, inda ta bukaci Hezbollah ma da ta yi aiki da irin wannan salo da dabara.

Sai dai kuma, a yayinda Isra'ila ke keta ka'idodin iyakar Iran, Tehran ta tsinci kanta da sabuwar manufar siyasa: ba za ta iya nade hannaye tana kallon ana yi mata haka amma kuma ta ce za ta dogara da kawaywanta - har masu yi mata biyayya - don cimma manufarta ta yanki, kamar lalatawa ko jinkirta yunkurin saanta juna.

Iran ta gano za ta iya daukar mataki kai tsaye, tana mai sauya fasalin yankin, a yayin da ake da tsaka da rauni da kuma yadda Amurka ta mayar da hankali ga zaben shugaban kasa.

A tsaka da kai hare-haren Isra'ila, Iran ta yanke hukuncin rungumar matakin da jama'a ke so na ta zama babbar abokiyar hamayyar Isra'ila a yankin.

Tehran ta aike da sakon cewa za ta mayar da martani ga barazanar yanki ta siyasa da ta soji idan hakan ya zama dole, tana mai sanin cewa dogaro kacokan kan wakilanta na yankin na iya zuwa da babban sakamako.

Dadin dadawa, duk wani jinkiri na shiga fagen daga kai tsaye, a yanzu shugabannin Iran sun gano cewa, hakan zai yi tasiri sosai kan karfin ikonsu a yankin.

Matakin fita yaki gaba da gaba na Iran ya samu karfafuwa ne da goyon baya daga kawayenta na Rasha da China, wanda goyon bayansu ya karfafa matakin na Tehran.

Tare da dabarunta, Iran ta tuntubi kasashen Gabas ta Tsakiya ta fuskar diflomasiyya, tana bayyana kanta a matsayin wadda ake kwara sakamakon hare-haren Isra'ila, tana kuma yin gargadin cewa yin biris ga damuwarta na iya haifar da sakamakon da ba za a so ganin sa ba.

An buga wannan makala da hadin gwiwar Egab.

Marubuci Mahmoud Shaaban dan jaridar dan kasar Masar mai bincike kan siyasa. Ya kammala digiri na biyu da yin bincike kan alakar Iran da Amurka, musamman wajen mayar d ahanmkali kan "Tasirin Takunkuman Amurka kan Iran a lokacin gwamnatin Donald Trump ." A yanzu haka, yana shirin kammala digirin digirgir kan fannin tsaron yanki inda ya mayar da hankali kan "Tasirin Yaki ta hanyar wakilci tsakanin Iran da Amurka kan Tsaron Tsaro a Gabas ta Tsakiya." Shaaban ya kware kan al'amuran Iran na tsawon shekaru kuma ya halarci tarukan siyasa da dama a Iran. Aikinsa na baya-bayan nan shi ne dakko rahotanni a zaben shugaban kasar Iran a watan Yuni 2024.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba dole ba ne ya zo daidai da ra'ayi, fahimta da kuma manufofin editan TRT Afrika ba.

TRT Afrika