Daga Hamzah Rifaat
A mummunar niyyarsa ta ci gaba da kasance wa a kan mulki tare da binne laifkansa na siyasa, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dora kansa a kan hanyar yaki zalla - kuma ya dasa tushen ba za a samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ba.
A wajen mutane da dama, jami'in mutum ne makaskanci kasa da karfa da ke tsakanin al'umma, sakamakon umarnin kama shi da aka bayar a kotun kasa da kasa da martanin da ya fuskanta daga duniya sakamakon kashe mutane a Gaza, inda ya dinga jagorantar kashe bani adam a yankin.
Netanyahu ya kuma nuna tsagwaron halin ko in kula a manufofinsa na cikin gida, inda a bayyane karara yake daukar alhakin aikata laifukan yaki. Hakan ya sanya shi zama saniyar ware, mai kaudin baki, da zama shi kadai a harkokin siyasar Isra'ila da duniya baki daya.
To me gwamnatin Netanyahu ta yi idan aka zo batutuwan cikin gida da na yanki.
Niyyar kisan kiyashi
Har a lokutan yaki, ana dora wa shugabanni alhakin su nuna halayya mai kyau. Shaida na nuni da cewa Netanyahu bai taba aiki da wannan alhaki ba.
Saboda yadda ya yi biris game da ci gaba da kisan kiyashi a Gaza da Lebanon mai makotaka, an kacalcala daukacin Gabas ta Tsakiya a watannin da suka gabata.
Talauci ya karu sosai, an tsugunar da Falasdinawa, 'yan kasar Lebanon da Siriyawa da dama, kuma babu yiyuwar tsagaita wuta duk da cewa taron kasashen Larabawa-Musulmi an la'anci hare-haren na Isra'ila.
Yanayin tsaro a Gabas ta Tsakiya da dukkan yankin ya tabarbare saboda yadda Netanyahu ya biris da rayuwar 'yan adam - da yadda kasasen Yamma suka ki su dakatar da shi - ya sake karfafa gwiwar 'yan ta'addar da a yanzu suke ganin za su iya kai wa fararen hula hari a wasu kasashen kuma su zauna lafiya.
Niyyar aikata kisan kiyashi ta Netanyahu iri daya ce da ta Adolf Hitler ga Nazi a Jamus. Yadda Isra'ila ta dinga ruwan bama-bamai a Gaza a kan idanuwan Netanyahu, hare-haren baya-bayan nan a Siriya da lebanon da aka kashe fararen hula 'yan ba ruwana da kuma yadda yake ta kauce wa tsagaita wuta ya isa ya zama shaidar aniyarsa ta kakkabe Falasdinawa da Larabawa baki daya.
Rashin mutuncin Netanyahu ya sake fito wa karara yayinda zuciyarsa ta kekashe kan kisan mutane, wanda abu ne bako ga wanda yake ikirarin kare martabatar "wayewar Yammacin duniya da kalubalantar dabbanci".
Ka dauki martaninsa a lokacin da aka kai hari kan na'urorin sadarwa a watan Satumba a Lebanon. Duk da hadin kan matsaya daga masu kare hakkokin dan adam da Majalaisar DInkin Duniya kan cewar fashewar dubunnan na'urorin a Lebanon "mummunan saba wa dokokin kasa da kasa ne," ofishin Netanyahu ya bayyana karara cewa shi da kansa ne ya bayar da umarnin kai harin.
Tabbas, rahotannin kafafen yada labarai na Isra'ila sun bayyana cewa Netanyahu ya ce a kai harin duk da adawa da ya fuskanta daga manyan jami'an tsaron kasar. Irin wannan mummunan hali da rashin tausayi kan kisan fararen hula a Lebanon.
Yadda Firaministan ya yi watsi da muryar bai daya a Isra'ila d ahalin ko in kularda da ke kashe fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba na nuni da mummunr dabi'a, sannan hakan ya sanya zama mai nuna wariya da bai yarda da aiki da ra'ayoyin jama'a daga bangarori daban-daban ba wajen dabbaka manufofi.
Irin wannan ra'ayi na dabbaka manufofi ba ware shi kawai yake yi a fagen kasa da kasa ba, na kuma nuni ga da yadda yake watsi da jin dadin jama'arsu.
Rikita-Rikitar cikin gida ta Isra'ila
A karkashin Netanyahu, tattalin arzikin Isra'ila na fuskantar rashin tabbas. Masanan tattalin arziki irin su tsohon gwamnan babban bankin Isra'ila, Karnit Flug, ya bayyana hakan wannan yaki da ake ci gaba da yi a Gaza da Lebanon, kuma ya yi gargadi da cewar illa ga harkokin cikin gidan na da yawa.
Asali dai, shugabanni na mayar da hankali ga walwalar jama'arsu, sannan su yi kasafin kudi da tanade-tanade ga 'yan kasa da daukar matakan fadada walwala da karin kudade ga inganta ilimi da hana matasa shiga halin tagumi.
Sai dai kuma gwamnatin Netanyahu, na yin abubuwa akasin wadannan.
Majalisar zartarwar Isra'ila a wannan watan ta amince da kasafin kudin 2025, inda aka kara yawan kudaden da ake kashe wa tsaro, maimakon ayyukan cigaban al'umma, kula da lafiya da ilimi ga 'yan kasa marasa galihu. Kasafin Netanyahu ya yanke kudade a bangarorin da ba su shafi tsaro ba, ya kara yawan haraji, ya dakatar da ayyukan walwala da rage yawan albashin ma'aikatan Isra'ila.
Sabon kasafin kudin ya kuma bukaci matsakaicin 'yan Isra'ila su biya haraji da yawa, a lokacin da gwamnati ta dakatar da biyan kudade ga tsofaffi, nakasassu da wadanda suka tsira daga kisan mummuke ga Yahudawa.
A yayin da goyon baya ke ragu wa a ciki da waje, Netanyahu ya kusa durkushewa amma kalamansa ke tserar da shi. Kuma dukkan kalaman na cike da karya a tsawon rayuwarsa ta siyasa.
Rikicin tsaron ya fi kuntatawa jama'ar kasar a yayin da Hezbollah ke ta kokarin daukar fansa kan hare-haren a arewacin kasar.
Yanzu, Netanyahu ya jefa tsaron duk wani dan kasar Isra'ila cikin garari. Radadi kan na gaza karbo wadanda aka yi garkuwa da su a lokacin yakin, wand ake kara bakantawa 'yan Isra'ila rai da jefa su cikin halin rashin tabbas.
Gangamin yada labaran karya
A yayin da goyon baya ke ragu wa a ciki da waje, Netanyahu ya kusa durkushewa amma kalamansa ke tserar da shi. Kuma dukkan kalaman na cike da karya a tsawon rayuwarsa ta siyasa.
Ka dauki bayaninsa a majalisar dokokin Amurka a watan Yuli. Ya yaba wa Isra'ila cewa wia ta bayar da izini ga tireloli 40,000 na kayan taimako sun shiga Gaza, kuma ya musanta aiki da manufar jefa mutane cikin yunwa.
Wannan ya nesanta daga gaskiya. Majalisar Dinkin Duniya ta ce Isra'ila na aiwatar da cikakkiyar kawanya, ciki har da hana kayan abinci, ruwa da magunduna shiga Gaza. A yayin da aka dan sassauta kai kayan tallafin abinci saboda matsin lambar kasashen duniya, kalaman Netanyahu jirkita gaskiya ne kuma wani bangare na farfagandarsa ta yaki.
Wannan ya hada da kalaman tuhumar ikirarin mai gabatar da kara na ICC cewa Isra'ila na kisan 'yan Gaza da gan-gan, kuma yana musanta irin barnar da aka rawaito ana yi a yankin. Irin wannan yada bayanai na karya na da manufar karkatar da hankulan mutanen kasar da na duniya zuwa ga goyon bayan Netanyahu a yayin da shi kuma yake ci gaba da aikatra munanan laifuka na kisan kiyashi ga bil'adama.
Har ta kai ta kawo ma jama'ar Netanyahu ma ba sa yarda da bayanan da suke fada. A yayin da suka daga cikin gida da waje ke kara yawa, Firaministan ya zabi kare kujerarsa ta hanyar rufe bakunan 'yan adawar Isra'ila.
A baya-bayan nan, ya kori Ministan Tsaro Yoav Gallant. Hakan ta faru ne a ranar da ake yin zaben AMuka,wanda ke nufin Netanyahu na tirsasa sabuwar gwamnatin da za ta zo ta yi aiki da shi kawai, (Amurka na da kyakkyawar alaka da Gallanta).
Korar Gallant ta yi daidai da fitar rahotannin cewa Netanyahu ya samu labarin za a kai harin 7 ga Oktoba, kuma ya nemi da a boye hakan. Wannan ya sanya wasu manazarta yin hasashen cewa Netanyahu ya kori Gallant ne don kawar da hankulan jama'a daga wannan abin kunya da aka gano.
Idan wannan ne, wani sabon misali ne na Netanyahu kasancewar sa kwararren yaudara a yayin da yake ta kokarin ci gaba da zama a kan mulki.
Gaskiya mai daci ita ce matukar Netanyahu zai ci gaba da kasancewa a ofis, ba za a taba samun tsaro a Gabas ta Tsakiya ba, Isra'ila za ta ci gaba da samun damuwa a cikin gida da durkushewar tattalin arziki. Wannan na da tasiri ga zaman lafiyar kasa da kasa.
Karin munanan labarai ma su ne, duk wanda ya maye gurbinsa, ba lallai ya damu da inganta rayuwar Falasdinawa ba, musamman a lokacin da Trump ya dawo kan mulki a Washington. Za a ga yadda za a ci gaba da mamaya, tare da rungumar wahalar da Falasdinawa ke sha ba tare da yi wa hakan kallon wata matsala ba, sannan da karin barazana ga zaman lafiyar Gabas ta Tsakiya.
Game da haka, Netanyahu na ci gaba da yin yadda yake so, kuma shi ne mai alhakin duk wadannan munanan ayyuka.
Marubuci, Hamzah Rifaat ya yi karatutttukan digiri a Nazarin Zaman Lafiya da Rikici a Islamabad, Pakistan da a Harkokin DUniya da kuma Diplomasiyya da Cibiyar Nazarin DIplomasiyya ta Bandaranaike a Colombo, Sri Lanka. Hamza ya kuma zama Babban Maziyarcin Cibiyar Muryoyin Kudancin Asiya a Cibiyar Stimson da ke Washington DC a 2016.
Togaciya: Ra'ayoyin da aka bayyana a nan na marubucin ne, kuma ba sa wakiltar ra'ayi, komahangar editocin TRT Afrika.