Daga Coletta Wanjohi
Alhida Hammed ya yi kasa a gwiwa bisa ga fatansa na ƙarshe - a yanzu ƙarfin hali kawai yake yi na rashin sanin makomarsa.
Ɗan gudun hijirar daga Sudan wanda a halin yanzu yake samun kulawa a wani asibiti dake gundumar Renk a makwabciyar ƙasar Sudan ta Kudu sakamakon raunin da ya samu daga harbin bingida, yana tunanin yadda rayuwarsa za ta kasance cikin yanayin radadi da juriya a tsawon wannan shekara.
Ya tsunduma cikin tashin hankali ne tun daga watan Afrilun 2023 lokacin da yaki ya barke tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai ɗaukin gaggawa na RSF, wanda ya mamaye sassan kasar.
Rayuwar Hammed - da ta sauran miliyoyin 'yan Sudan - ta zama tamkar mafarki mai ban tsoro wanda taki ƙarewa tun daga lokacin.
"Ƙauyenmu ya kone kurmus," in ji shi yana mai bayyana ranar da ya bar gidansa da ke jihar kogin Nilu ta Sudan.
"Kowa yana gudu ta hanya daban-daban don neman tsira. Gabaki ɗayanmu mun rasa matsugunanmu, mun koma zama a ƙarkashin bishiyoyi. Ba ni da sha'awar komawa gida. Yanzu ba mu da gida - yana mai cike da mummunan tunani."
Ƙungiyar Doctors Without Borders (MSF), wacce ke kara kaimi wajen kai ɗauki ga dimbin ‘yan gudun hijirar da suka isa gundumar Renk, ta fitar da rahoton da ke cewa sama da mutane 5,000 daga kogin White Nile da Blue Nile ne suke tsallakawa zuwa Sudan ta Kudu kowace rana tun daga farkon Disamba.
''Mun kara tantuna 14 a kusa da asibitin don samarwa majinyata wuraren da za a kula da su,'' in ji Emanuele Montobbio, jami'in ayyukan gudanarwa na MSF a Renk.
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta kiyasta cewa har zuwa ranar 22 ga watan Disamba, adadin wadanda suka rasa matsugunansu a Sudan ya haura mutum miliyan 12, kana sama da miliyan uku daga cikinsu sun nemi mafaka a wajen kasar.
Ƙasashen Chadi da Libya da Masar da Habasha da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da kuma Sudan ta Kudu duk sun arbi 'yan gudun hijira daga Sudan.
Ƙungiyar MSF ta kiyasta cewa adadin sabbin 'yan gudun hijira 80,000 da suka isa Sudan ta Kudu na buƙatar kulawar lafiya.
An yi wa kaɗan daga cikinsu aikin tiyata da kuma allurar riga-kafi a makonnin da suka gabata, yayin da sama da marasa lafiya 100 wadanda suka jikkata suke cikin mawuyacin yanayi.
Tsananin ƙarancin abinci
Ga sauran mutane da suka rage a Sudan, yunwa na matukar barazana ga rayuwarsu kamar dai yadda yakin ya kasance.
A ranar 27 ga watan Disamba, shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ya ce mutane 78,000 a kudancin babban birnin kasar, Khartoum, sun samu tallafin abinci da kayan jinƙai a karon farko tun bayan barkewar rikici.
Cikin sama da watanni 20, yakin da ake yi a yankin ya hana kai agaji na jinƙai.
Wani rahoton baya- baya nan da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya suka fitar ya yi gargadin cewa sama da mutane miliyan 24.6 a faɗin Sudan, adadin da ya zarce rabin al'ummar da aka tattara na fuskantar tsananin karancin abinci.
Daga cikin adadin, mutane miliyan 8.1 na cikin "yanayi na bukatar gaggawa" yayin da a kalla 638,000 ke cikin "tsananin matakin bala'i".
"Hukumar Abinci da Aikin Noma ta FAO ta damu matuka game da tabarbarewar yanayin samar da abinci a Sudan, musamman a sansanin 'yan gudun hijira na Zamzam da sauran matsugunan yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula, inda al'amura ke kara tabarbarewa cikin sauri," in ji daraktan agajin gaggawa da juriya na FAO,Rein Paulsen.
A karshen shekarar 2024, Sudan ta yi asarar lokacin samun yawan amfanin noma na girbi.
''Ana ɗaɗa fuskantar matsalar yunwa a Sudan,'' in ji daraktan tsaron abinci na shirin WFP Jean-Martin Bauer ya yi gargadi a kai.
"Mutane suna kara rauni kuma suna mutuwa saboda rashin samun abinci a tsawon watanni da dama."
Da yake har yanzu ana ci gaba da gwabza yaƙin, akwai yiwuwar Sudan ta iya asarar lokacin yin noma da ke tafe.
''Rayuwar miliyoyin matsa na cikin garari. Samar da abinci da ruwa da kuma magunguna za su taimaka wajen ceton rai daga fadawa cikin tsananin rashin abinci mai gina jiki, amma muna bukatar tsaro mai dorewa da kuma hanyar da za mu iya kaiwa zuwa ga yara da masu rauni da kuma ceton rayuka,'' a cewar daraktar ayyukan gaggawa na UNICEF, Lucia Elmi.
Shirin zaman lafiya na Turkkiya
Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta dage kan cewa dole ne masu ruwa da tsaki a Sudan su nemo hanyar warware wannan matsala ta cikin gida.
Duk da kokarin da kungiyar bunƘasa ci gaban kasashen gabashin Afrika (IGAD) da makwabciyarta Sudan ta Kudu ke yi bai cimma wata nasara ba, Turkiyya na kokarin ganin an sassauta rikicin Sudan tare da Hadaddiyar Daular Larabawa UAE.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kira shugaban sojojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan a makon da ya gabata inda ya yi tayin shiga tsakani don warware matsalar.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shugaba Erdogan ya kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Habasha da Somaliya.
Kokarin UAE na shiga tsakani ya samo asali ne daga wasu dabaru , kamar kiyaye hanyoyin jigilar kayayyaki na Bahar Maliya da saka hannun jari a albarkatun ƙasa na Sudan, wanda ya ƙara dakula yanayin yankin.
Duk da cewa Sudan na mutunta gudunmawar tattalin arzikin da Hadaddiyar Daular Larabawa ke bayarwa, manufofin Abu Dhabi sun sanya ayar tambaya game da tasirin kasashen waje a cikin harkokin cikin gidan Sudan.
"Muna fatan shirye-shiryen da aka gabatar ciki har da shawarar shugaba Erdogan, mai cike da hikima da kwarewa, wanda ya bayyana shirinsa na shiga tsakani Sudan da Hadaddiyar Daular Larabawa, za su yi nasara," in ji Ministan harkokin wajen Sudan Ali Youssef.
Ya zargi dakarun RSF da alhakin matsalolin da Sudan ke ciki, yana mai nuni da kin bin sharuddan "yarjejeniyar Jeddah" da aka rattabawa hannu a watan Mayun 2023.