Minister of Foreign Affairs and International Cooperation of Mali with Turkish Minister of Foreign Affairs Hakan Fidan on the margins of Antalya Diplomacy Forum, 2024. / Photo: Archive

Daga Nuri Aden

Daga cuɗanya kan harkokin diflomasiyya da kuma haɗa kai wajen harkokin kasuwanci , ababen da aka cimma a shekarar da ta gabata sun nuna nasarar salon hulɗar Turkiyya da Afirka a fannoni da dama cikin shekara 20.

Turkiyya ta ƙarfafa alaƙar diflomasiyyarta a nahiyar Afirka cikin shekarar inda shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya karɓi baƙuncin jerin wasu shugabannin Afirka a Ankara.

Baƙin sun haɗa da sabon Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye da Firayim Ministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine da Shugaban riƙon ƙwarya na Sudan Abdel Fattah al-Burhan da shugabar Tanzaniya, Samia Suluhu Hassan da Shugaba Abdel Fattah al-Sisi na Masar da sauransu.

Ga Turkiyya, karɓar waɗannan shugabannin Afirka hannu bibbiyu wani ɓanagare ne na manufofin da suka yi sharar fage wa alaƙarta da ke sauyawa da nahiyar Turkiyya ta daɗe tana kimantawa.

Shugaba Erdoğan ya nuna hakan a lokacin da ya jaddada muhimmancin ziyarar shugabar Tanzaniya ta farko zuwa Turkiyya cikin shekaru 14 a matsayin wani sauyi ga alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Ya bayyana muhimmancin Tanzaniya a Gabashin Afirka tare da shirya tsarin aikin cinikayya na gaba ciki har da ƙara cinikayya zuwa abin da ya kai dala biliyan ɗaya.

Baya ga ziyara tsakanin ƙasashe, Shugaba Erdoğan ya zanta da shugabannin Afirka a tarukan ƙasa-da-ƙasa irin taron shugabannin ƙasashen BRICS a birnin Kazan na Rasha inda ya gana da shugaban Congo Denis Sassou Nguesso.

Taron diflomasiyyar Antalya (ADF), wanda aka yi a watan Maris,ya taka muhimiyar rawa wajen ƙarfafa tattaunawa kan batutuwan duniya da na yanki. Shugabannin Afirka irin Shugaban Djibouti, Shugaba Ismail Ömar Guelleh da kuma takwaransa na Madagascar, Andry Rajoelina suna cikin baƙin da suka halarci zaman.

Yawaita zuba jari

Ɗaya daga cikin ababen da suka bambanta shekarar 2024 shi ne ƙarin dangantaka ta tattalin arziƙi tsakanin Turkiyya da ƙasashen Afirka yayin da kamfanonin Turkiyya suka ci gaba da shiga fagen kasuwancin nahiyar.

A Tanzaniya, kamfanonin Turkiyya sun aiwatar da ayyuka da suka kai na kuɗi dala biliyan 6.4. Taron kasuwancin Turkiyya da Tanzaniya na da niyyar samar da sabbin damarmakin ƙara huldar tattalin arziƙi.

An sake ganin alamun farfaɗo da tattalin arziƙi a ɓangaren bankuna da sufuri da kuma gine-gine. Bankin Turkiyya Ziraat Katilim ya zama bankin ƙasar waje na farko da ya fara buɗe reshe a Somaliya cikin shekara 50.

Kamfanonin Turkiyya irin su Summa Construction suna aiwatar da ayyukan gine-gine a faɗin nahiyar ciki har da zamanantar da filin wasan Amahoro na Kigalin Rwanda.

Fannin Sufuri ma ya sami muhimmin ci-gaba inda kamfanin gine-ginen Turkiyya Yapı Merkezi ya aiwatar da ayyukan gina layin dogo a Uganda da Tanzaniya.

Cikakken haɗin-kai

Turkiyya ta kuma taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa tsaro da zaman lafiya a faɗin Afirka.

Ana amfani da jiragen sama mara matuƙa (UAV) a ƙasashe irin su Mali da Burkina Faso da Nijar lamarin da ya ƙarfafa yaƙi da ta’addancin tare da taimakawa wajen tabbatar da tsaron kan iyakoki a yankin Sahel. Nijeriya ma ta sayi jirage masu saukar ungulu domin ƙarfafa tsaronta.

Turkiyya ta kuma yi wani shiga tsakani da ya samo sasanci na tarihi tsakanin Ethiopia da Somaliya bayan sun shafe kusa shekara ɗaya na zaman ɗar-ɗar tsakanin maƙwabtan na kusurwar Afirka.

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Ethiopia da Somalia ne cikin watan Janairu bayan Addis Ababa ta rattaɓa hannu kan yarjejeniyar samun damar amfani da tashan jiragen ruwa na yankin Somaliland da ya ɓalle daga Somaliya.

Bayan watanni na shiga-tsakani ƙasashen biyu sun rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya a Ankara cikin watan Disamba domin kawo ƙarshen rashi jituwar. Wannan ya samar wa Turkiyya yabo a duniya, ciki har da Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Amurka.

Haɗin kan Turkiyya da Afirka wajen ayyukan jinƙai da kuma ci-gaba yana da ƙarfi inda hukumomi kamar hukumar ba da agaji ta Turkiyya (TIKA) da ƙungiyar ba da agaji ta Red Crescent da kuma ma’akatar lafiya suke aiwatar da ayyukan ci-gaba a faɗin Afirka .

TIKA kaɗai tana da ofisoshi na gudanarwa 22 a nahiyar inda take aiki domin magance muhimman matsaloli a fannin lafiya da ilimi da kuma ci-gaban tattalin arziƙi.

Ƙara musaya

Turkiyya ta kuma ƙara yawan ofisoshin jakadancinta a Afirka inda yawan ofisoshin suka ruɓnya daga 12 a shekara 2002 zuwa 44 a shekarar 2022.

Wananna faɗaɗa harkar diflomasiyyar na zuwa ne a daidai lokacin da yawan ofisoshin jakadancin ƙasashen Afirka ke ƙaruwa a Ankara, inda ofisoshin suka kai 38daga 10 a shekarar 2008.

Ƙarin huldar diflomasiyya yana nuna ƙaruwar hulɗar siyasa da kuma tattalin arziƙi tsakanin Turkiyya da kuma ƙasashen Afirka.

An kuma sami ci-gaba a fagen musayar al’adu da ilimi inda cibiyoyi irin su cibiyar yaɗa al’adun Turkiyya ta Yunus Emre Institute da kuma ofishin shugaban ƙasa kan Turkawa da ke ƙetare da makamancinsu (YTB) da kuma cibiyar ba da tallafin ilimi na Turkish Maarif Foundation suka taka rawar gani wajen haɗin kan mutane.

Kamfanin jiragen saman Turkiyya ya ba da gudumawa wajen ƙara yawan taifiye-tafiye tsakanin Turkiyya da Afirka inda ta ke zuwa sama da wurare 60 a cikin ƙasashen Afirka 39 kafin annobar korona ta kunno kai kuma ta ke ƙara yawan wuraren da ta ke zuwa yayin da ake ɗage takunkumin zirga-zirgar jirage.

Fata na gaba

Turkiyya tana da niyyar zama wata cibiya ga ƙsashen Afirka wadda za ta sauƙaƙe samun shiga kasuwannin duniya ta ingantaccen hanyoyin sufuri da kasuwanci.

Ƙara yawan jiragen kamfanin jiragen Turkiyya wanda ake son ƙarawa zuwa Afirka ya nuna wannan burin.

Yayin da ake ci gaba da samun ziyaran manya da haɗin-kai na tattalin arziƙi da kuma tallafin jinƙai, shekarar 2024 ta kasance shekarar da ta nuna salon alaƙar Turkiyya da Afirka lamarin da ya share fagen ƙwaƙƙwaran haɗin-kai.

Yayin da ɓangaririn biyu ke auna yadda gaba za ta kasance dangantaka na taimaka wa juna ta fannin diflomasiyya da kasuwanci da tsar da kuma musayar al’adu shi ne abin da ya fi kyau.

TRT Afrika