Daga Sylvia Chebet
Kayan kuɓutar da rayuka da yin tiyata a asibitoci a kudancin Khartoum babban birnin Sudan sun ƙare, sakamakon haramcin hana shigo da kayayyakin kula da lafiya da gwamnatin kasar ta yi a yankunan da ke hannun mayaƙan RSF da suka kwace tun a watan Satumba.
Kungiyar Likitoci ta MSF ta yi kiran gaggawa kan a janye wannan haramci na shigar da kayan kula da lafiya, inda ta yi gargadin cewa rayuwar daruruwan mutane da suka hada da mata da yara kanana na cikin hatsari.
"Kwanan nan, an kawo wata yarinya mai shekara hudu zuwa sashen gaggawa na asibitinmu, bayan da harsashi ya same ta a ciki a cikin gidansu.
"Mahaifiyarta ta kai ta asibitoci uku kafin a karshe ta kawo ta asibitin Turkawa don yi mata tiyata," in ji shugabar MSF a Sudan, Claire Nicolet yayin tattaunawarsa da TRT Afirka.
"Mun sake fuskantar mummunan yanayi a lokacin da makamin roka ya fado kusa da wasu yara su hudu da suke wasa. Ba su gano cewar abu ne mai hatsari ba sai bayan da ya fashe a hannunsu."
Yara biyu daga cikin su sun samu munanan raunuka inda ya zama sai an yi musu tiyata a ciki.
Rayuwa da mutuwa
Nicolet ta kara da cewa "Idan ba a janye haramcin shigar da kayan yin tiyata zuwa Khartoum ba, to ba za mu samu damar yin ayyukan kula da marasa lafiya yadda ya kamata ba, musamman mata, yara kanana da kuma wadanda yaki ya rutsa da su."
A yayin da babu sararin ajiye kayan yin tiyata a asibitocin Kharotum, Nicolet ta kara da cewar a makonni masu zuwa za a jigata sosai. Wannan haramci na nufin mutuwar duk wani mara lafiya da ke cikin halin rai mutu kwakwai kenan.
"Kaso biyu cikin uku na tiyatar d aake yi a asibitin Turkiyya na ciro jarirai ne daga cikin iyayensu mata.
"A watanni biyu da suka gabata kawai, mun yi irin wannan tiyata sau 170 - idan babu kayan aikin gidanar da wannan tiyata, mata da dama da jariran da za a haifa za su rasa rayukansu."
Nicolete ta damu matuka game ada matan d ake nakuda da suke bukatar tiyata don ciro jarirai daga cikinsu, wanda ba su da zabi da yawa a Khartoum.
"Idan aka ci gaba da hana kawo mana kayan yin tiyata, za su zama ba su da wani zabi da ya rage."
Kungiyar ta Likitocin Komai da Ruwanka ta kuma kara da cewa tun farkon watan Satumba aka fara aiki da wannan haramci, amma sai a ranar 2 ga Oktoba ne gwamnatin Sudan ta sanar da game da dukar matakin.
Amma kuma yakin da bangarori biyun ke yi na ci gaba da janyo asarar ga fararen hula.
Ta'azzarar rikici
"Tiyata na da muhimmanci wajen kubutar da rayuwa da kowa yana da hakkin a yi masa, kuma na daya daga cikin hanyoyin kula da lafiya da yaki ke sanyawa dole a yi amfani da su," in ji Nicolet inda ta kara da cewa "jefa bama-bamai, fashewar su da harbi da bindigu na janyo ciwukan da ke bukatar tiyata."
A ranar 10 ga Satumba, a lokacin da aka kai hairn bam kasuwar Gorro, lamarin ya rutsa da mutane 103 inda 43 suka rasa rayukansu, an kai wdanda suka jikkata su 60 zuwa Asibitin Koyarwa na Bashair.
"Sai dai kuma, MSF sun dakatar aikin tiyata a wannan waje a watan Oktoba saboda haramcin da aka sanya, ma'ana a yanzu Asibitin Turkiyya ne kadai ya rage da ake yin tiyata a Khartoum," in ji Nicolet.
Asibitin na Turkiyya ya sake rikicewa a lokacin da aka jikkata wasu mutane 128 kuma aka kai su sashen gaggawa na asibitin bayan wasu hare-hare da aka kai a ranar 12 da 13 ga Nuwamba.
Kungiyar ta kuma ce an yi tiyata da yawa, kuma akwai marasa lafiya da dama da ke kan layi.
"Sakamakon haka, a yanzu babu isassun kayan aiki da magunguna a asibitin da za si kai nan da wata daya. Idan kungiyar MSF ba ta samu damar kawo kayayyakin ba, to za a rufe dakin tiyata na Asibitin Turkiyya, wanda hakan zai sanya a samu karin mutuwar mutane da dama."
An hana kawo magunguna da likitoci
MSF sun samu labarin cewa an hana duk ma'aikatan lafiya da na ayyukan jin kai yin tafiywa zuwa wani waje, wanda ahakan ke kara ta'azzara mummunan halin da ake ciki.
"Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance da aka mikawa MSF daga mahukuntan Sudan kan wannan batu, gaskiyar zance shi ne babu wani jami'in lafiya na Sudan ko na kasar waje da ya samu damar shiga kudancin Khartoum don yin aiki tun farkon watan Oktoba."
"Mahukuntan Sudan sun ce za su bayar da dmaar shigar tireloli 90 zuwa Khartoum don kai kayan agaji da magunguna, amma har yanzu ba a ga hakan ta tabbata ba," in ji MSF.
Nicolet ta ce an hana motocin MSF yin tafiye-tafiye baki daya.
"Kawai ma'aikata d akayan kula da lafiya na MSF da ke jiran tsammani a Wad Madani, waje mai nisan kasa d akilomita 200 daga Khartoum," in ji ta. MSF na neman dukkan wata hanya ta tabbatar da an kula da marasa lafiya.
Amma kuma, Nicolet ta ce babu zabi da yawa da ake da shi.
Mutuwa da raba mutane da matsugunansu
An yi hasashen cewa an kashe sama da mutane 10,000 a tsawon watanni takwas da aka dauka ana gwabza yaki tsakanin bangarori biyu masu adawa da juna a Sudan.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa an tirsasawa mutane miliyan 6.3 gudun hijira, inda kimanin miliyan guda suke fice dags Sudan, tun bayan yakin da aka fara a a ranar 15 ga watan Afrilu.
Tare da yadda ake samun daduwar rasa rayuka, raba mutane da matsugunansu da jikkata wadanda ba a iya yi musu magani, Sudan ba za ta zama yadda take a baya ba.
Kungiyoyin bayar da taimakon jinƙai sun ce dole ne a dakatar da yakin don hana karin tabarbarewar al'amura.