Ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta bayyana wa Majalisar Dinkin Duniya cewa ta ayyana Volker Perthes, wakili na musamman ga Sakatare Janar na Majalisar a kasar a matsayin wanda ba a “bukatar aikinsa” a kasar baki daya.
Shugaban gwamnatin sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya aike wa Majalisar wasika inda ya zargi Perthes, wanda shi ne shugaban tawagar hadaka ta MDD a Sudan (UNITAMS), da kara iza wutar rikicin kasarsa, don haka ya bukaci MDD ta maye gurbinsa.
Sanarwar ta fito ne makonni biyu bayan da babban hafsan sojin na Sudan ya zargi Perthes da neman a tsige shi.
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya fada a karshen watan jiya cewa ya “kadu” da ganin wasikar Janar Abdel Fattah al-Burhan.
"Guterres na alfahari da aikin da Volker Perthes ya yi kuma ya nuna cikakken goyon bayansa ga wakilinsa na musamman," a cewar mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric a wata sanarwa da ta yi fitar.
Perthes tsohon malami ne da ya jagoranci wata tawaga a Sudan tun daga 2021 kuma ya yi tsayin daka wajen kare martabar Majalisar Dinkin Duniya daga zarge-zargen da ake yi mata na rura wutar rikicin Sudan, in ji Dujarric.
Ta ce "janar-janar biyu da ke yaki da juna" su ne ke da alhakin abin da ke faruwa a kasar.
Tun daga watan Afrilu aka soma gwabza fada tsakanin sojojin Sudan da dakarun rundunar RSF a babban birnin kasar Khartoum da kuma yammacin yankin Darfur.
Sama da mutane miliyan 1.4 ne suka rasa matsugunansu a kasar sannan mutum 476,800 kuma suka tsere zuwa kasashe da ke da makwabta, wadanda tuni akasarinsu ke fama da talauci da rikice-rikicen cikin gida, a cewar alkaluman Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM).
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane miliyan 25 - fiye da rabin al'ummar Sudan - a yanzu suna bukatar agajin jinkai, sannan ya zuwa yanzu an kai agaji da ya kai ga taimaka wa kimanin mutane miliyan 2.2 tun daga karshen watan Mayu.