Raja Tariq yana rike da hoton dansa Raja Awais a jikin waya, wanda shi ma ya ba a ganshi ba bayan hatsarin jirgin ruwan a Tekun Bahar Rum: Hoto [Nasir Mehmood/AP]

Hameed Iqbal Bhatti ya shafe shekara sama da 20 yana aiki a Saudiyya cikin rufin asiri, amma shekara uku bayan komawarsa Pakistan, sai ya shiga cikin matukar damuwa.

Tattalin arziki ya shiga halin tangal-tangal a lokacin annobar korona, lamarin da ya jawo ya rufe shagon sayar da abincinsa.

A yayin da hanyoyin samun aiki suke kulle ga kuma tsadar rayuwa da ta dinga tasiri a kan samunsa, sai mutumin mai shekara 47 ya kukuta ya hada dala 7,600 ya bai wa wani mai safarar mutane don ya shigar da shi Turai.

Ya yi hakan ne da fatan ya sake gina rayuwarsa kamar ta baya, kamar yadda yayansa mai shekara 53 Muhammad Sarwar Bhatti, ya shaida wa Reuters.

"Ya shaida min cewa zai fara komai daga farko ko don inganta rayuwar 'ya'yansa a nan gaba," a cewar yayan nasa Mista Bhatti a hirar da aka yi da shi a gidansa da ke yankin Kashmir da ke karkashin ikon Pakistan.

Wani jirgin ruwa ya bar kasar Libiya dauke da kanin Bhatti da sauran daruruwan mutane suka nutse a tekun Girka, a wani lamari da ya kasance daya daga cikin mafi munin bala'in da ya samu 'yan ci-rani a shekarun baya-bayan nan.

Cikin wadanda suka mutu har da Ali Reza mai shekara 28, wanda ya yi kokarin tsallakewa Turai da taimakon masu safarar mutane, don samun aiki mai kyau.

“Muna jiran faruwar wani abin al'ajabi, don komai na iya faruwa," in ji Sawan Raza, yayan Ali da ya bata.

Raja Sakundar na kauyen Bindian village a Kotli, ya ce 'ya'yan yayyensa hudu 'yan tsakanin shekaru 18 zuwa 36 ma sun bata.

“A kafar watsa labarai muka ji labarin bala'in da ya afkun. Yaya kake tunanin iyaye za su ji a ransu idan aka ce dansu ya mutu ko kuma ba a ganshi ba," ya ce.

Neman wadanda ba a gani ba da kuma gano su waye suka mutu

Bayan afkuwar bala'in, sai hukumomi a Pakistan suka fara daukar samfurin kwayoyin halitta na iyalai fiye da 200 da ke neman a gano danginsu.

Iyalan sun je wajen hukumomi ne suna cewa suna tsammanin danginsu na cikin jirgin ruwan, a cewar Mumtaz Zahra Baloch, mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar.

A kalla an yi amannar 'yan Pakistan 209 ne a cikin jirgin, a cewar bayanan da hukumomin Pakistan suka bai wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

An ba da adadin mutum 209 din ne ta yin la'akari da bayanan da iyalan da suka kai wa hukuma labarin cewa danginsu suna cikin jirgin, wanda zai dau hanyar Libiya don isa Girka kuma a ba gansu ba, a cewar Hukumar Bincike ta Tarayya (FIA).

An ayyana makokin kwana guda a Pakistan don girmama wadanda abin ya rutdsa da su.

A hannu guda kuma, 'yan sandan Pakistan, sun kama fiye da mutum 10 da ake zargin su da safarar mutane, inda yawan wadanda aka kama din ya kai 17 a wasu samame da aka yi a kasar, ta ce.

Sannan akwai kusan mutum 30 da su ma aka kama bisa zargin su da hannu a lamarin.

Sai dai, ta ce gwamnatiba za ta iya tabbatar da yawan 'yan Pakistan din da suka mutu ko aka kasa gano su ba daga cikin jirgin da ya nutse din.

An kai samamen ne bisa umarnin Firaminista Shahbaz Sharif inda aka umarci dakarun tsaro su rusa kungiyoyin masu safarar mutanen.

A ranar Larabar da ta gabata ne jirgin ruwan na kamun kifi da aka cika shi makil da mutum 750, ya kife. Mutum 104 kawai aka ceto da suka hada da 'yan kasashen Masar da Pakistan da Syria da kuma Falasdinu, sannan an gano gawa 82.

Kazalika akwai kuma 'yan kasar Afghanistan da ba a san adadinsu ba a cikin jirgin.

Wani da ya tsira a lamarin yana samun kulawar masu aikin agaji a garin Kalamata na kasar Girka a ranar 14 ga watan Yunin 2023. (Angelos Tzortzinis/AFP)

Makudan kudin fasa kwabri

A ta bakin wasu da suka rayu, ko a lokacin da ake cikin jirgin ma 'yan ci-ranin Pakistan sun fuskanci wariya, kuma an rufe da yawansu a cikin wani daki da ke can kasan jirgin.

Da ake tabbatar da bayanai daga wajen iyalai, jami'an Pakistan sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, wadanda suka yi kokarin yin wannan tafiya mai cike da hatsari zuwa Turai, sun biya masu fasa kwabrin tsakanin dala 5,000 zuwa 8,000.

Jami'ai sun yi zargin cewa wasu daga cikin masu fasa-kwaurin sun yi ikirarin karbar kudade daga mutanen da ke cikin jirgin da ya nutse din.

A cewar hukumar FIA da kuma 'yan sanda, yawancin iyalan da suka ba da samfurin kwayoyin halitta sun fito ne daga yankin Punjab na gabashin kasar da kuma na yankin Kashmir da ke karkashin ikon Pakistan.

A can Masar kuwa, Sabah Abd Rabu Hussein ma na jiran ta ji wani labari a kan danta Yahia Saleh, wanda aka yi imani shi ma yana cikin wannan jirgin.

“Sai da na roke shi kar ya je,” in ji uwar a ranar Lahadi, "amma ya kai makura wajen gajiya da yanayin talauci da muke ciki."

Cikin sati daya da wuce, iyalan gidan Saleh na cikin rudanin fatan ganin dansu da ma sauran mutane. Suna so su san ko yana cikin wadanda suka tsira ko ya mutu ko kuma ba a gan shi ba har yanzu.

“Ina son ganin dana, ina son ganinsa ko a mace ko a raye," in ji mahaifiyar tasa, inda ta rufe idanunta da hannunta tana kuka.

Mahaifin Saleh ya ce kafin faruwar bala'in, sai da aka tilasta wa iyalan bai wa masu fasa kwabrin dala 4,500 bisa tsoron kar su cutar da dan nasu idan ba su biya ba.

Tafiya mai cike da hadari

Wannan hoton Muhammad Nadeem ne mai shekara 38, dan Pakistan mai 'ya'ya uku da hatsarin jirgin ruwan ya rutsa da shi (Akhtar Soomro/Reuters)

Ko kafin faruwar wannan iftila'i na satin da ya wuce na Girka, 'yan Pakistan da yawa sun sha bata bat sakamakon nutsewar jirgin ruwa a Tekun Bahar Rum.

Muhammad Nadee mai shekara 38, yana cikin jirgin ruwan da ya nutse a Libiya a watan Fabrairu, inda fiye da mutum 70 suka mutu.

Nadeem, daga gabashin birnin Gujrat, yana da 'ya'ya uku sannan shi yake kula da kanwarsa da mahaifiyarsa.

Ya yi aiki awani shagon sayar da kayan gado bisa albashi mai dan dama, amma hauhawar farashi ta sa abubuwa suka rincabe musu har bukatunsu suka fi karfinsu, a cewar mahaifiyarsa, Kosar Bibi.

"A da muna dan samun na ci da sha, amma daga baya abubuwa suka lalace," kamar yadda ta shaida wa Reuters.

Bibi ta ce danta ya bai wa wani kudi don ya shirya masa tafiya zuwa Italiya inda za a bi ta Libiya.

"Ya ce min mama, abubuwa za su yi mana kyau. Ya ce zai kai ni aikin Hajji, kuma zai yi wa kanwarsa aure," Bibi ta ce.

A karshe dai Nadeem bai samu kai wa ga Turai ba.

Reuters