Daga Dayo Yussuf
Ranar Ma'aikata ta wannan shekarar a Tanzania ba wai kawai bikin 1 ga Mayu ba ce da aka saba gani ma'aikata na yi. Ta zama wata babbar rana a tarihin kasar, duba ga inganta amfana da yanayin haihuwa, inda gwamnati ta amince da karin kwanakin hutu a wajen aiki ga iyaye mata da suke haifar bakwaini.
Mutane da dama sun yi murna bayan smaun sanarwar da suka dade suna sauraro, wadda mataimakin shugaban kasar Tanzania Dr Philip Mpango ya fitar. Kungiyoyin fafutuka da na kwadago sun yi matukar murna da samun sanarwar saboda sanin muhmancinta ga ma'aikata a fadin kasar.
Wani abin faranta zuciya game da wannan cigaba shi ne irin yadda iyayen da suka haifi bakwaini suke shan wahala, wanda hakan ya sanya suna bukatar karin kwanakin hutu.
Ana ajiye bakwaini a waje na musamman don kula da lafiyarsu da sanya musu idanu har sai sun yi ƙwari sosai, inda ake sallamar su zuwa gida ko babban daki a asibiti.
Wannan na iya daukar makonni ko ma watanni a wasu lokutan, kuma mafi yawan sharuddan aiki ba sa bayar da damar hutu idan an haihu ko an fada irin wannan yanayi.
"Zan so na jaddada cewa hutun haihuwa na daya daga cikin haƙƙoƙin ma'aikata, kuma ana bayar da tsawon kwanaki 84 ga wanda ya haifi yaro daya, da kwanaki 100 ga wanda ya haifi sama da yaro daya," in Dr Mpango, a ranar ma'aikata yayin da yake bayani.
"Idan ma'aikaci ya haifi yaro ko yara d asuke bakwaini, hutun iyaye mata zai fara aiki ne da zarar likita ya tabbatar da yanayin lafiyar jariran. Muna yi gyara ga dokar Daukar Aiki Da Alaka Ma'aikata don bayyanawa ƙarara cewar hutun haihuwa na fara wa ne daga lokacin da jariri bakwaini ya kammala samun kulawa ta musamman, idan likitoci suka tabbatar."
Lamari ne da ya shafi zuciyarta
Dorris Morrel, wata mai fafutuka da ke gangamin neman karin hutu ga matan da ke kula da bakwaini, ta sa irin muhimmancin da wannan doka sabuwa ke da shi ga irin wadannan iyaye. Ita kanta bakwaini aka haife ta, shi ya sa take da alaka sosai da lamarin.
"Mun dade muna ta gwagwarmaya saboda wannan," Doris ta shaida wa TRT Afirka. "Mun yi farin ciki cewa mun matsa daga matakin gwagwarmaya, a yanzu damar na hannun gwamnati don yin doka da amincewa da ita saboda jarirai bakwaini da iyayensu."
Dokokin d asuka shafi haihuwa d aake da su a yanzu haka ba su damu d alafiyar bakwaini ba, ana tirsasawa iyaye mata su ji da matsalarsu da wahalhalunsu su kadai. A wasu lokutan, dole ne su zaba tsakanin aikinsu ko kula da jariransu.
Doris ta ce "Abin takaici ne hata wajen bayyana sabuwar haihuwa, dokar ba ta bayyana bakwaini amatsayin jariri ba. Daga nan ne ya kamata a fara ganin sauyin ta yadda matan da ke haihuwar bakwaini za su zama masu 'yanci wajen samun hutu," in ji Doris.
Matsala wajen haihuwar jarirai
A likitance bakwaini na nufin jaririn da aka haifa kafin ya cika makonni 37 a mahaifa.
Bayani na kusa shi ne tsakanin makonni 36 da 36 da ake kira "babban bakwaini" kuma na iya zama mara fuskantar hatsari sosai bayan haihuwa. Wadanda ake haifa a tsakanin makonni 25 zuwa 34 ne ake kallon sun fi rauni kuma "matsakaitan bakwaini".
Jarirai mafiya fukantar hatsari su ne wadanda ake haifa a kasa da makonni 25, wadannan su ne ake kira "cikakkun bakwaini".
Ciki cikakke shi ne wanda ya cika makonni 40 cif. Bakwaini na da karancin cikar gabbai da sassan jiki, kuma na iya fuskantar matsalar lafiya d ake bukatar kulawar likitoci ta musamman.
Doris ta kara da cewa "ba kai kake tsara za ka haifi bakwaini ba. Jaririn na fito wa ne bisa hatsari.
"Uwa da ta haihu kalau za ta iya tafiya gida washe gari, kuma ta yi hutunta na watanni uku. Ba daya ba ne ga wadda ta haifi bakwaini."
Babban kalubalen da ke tattare da bakwaini shi ne kula da yanayin lafiyarsu da ke biyo baya.
Matsalolin da aka fi gani su ne na girma, ciki har da matsalolin numfashi saboda huhun d abai gama girma ba, wahalar cin abinci saboda rashin isassun sinadaran tsotsa da hadiye mama d ama matsalar narkewar abinci, suna gwagwarmayar rike dumin jikinsu, samun cututtuka saboda raunin jiki da garkuwa, sannan da karancin habakar kwakwalwa.
Tsaro ga ma'aikata
Kungiyoyin ma'aikata sun bayyana cewa sabon tsarin hutun haihuwa zai taimaka wajen tseratar da ayyuka iyaye mata.
"Jariran da ake haifa bayan cikar makonni 40 na kaiwa kilo 2 zuwa 5. Bakwaini kuma ba sa wuce kilo 1.5 ko ma kasa da haka. To dole uwa ta dawo da jariri zuwa asibiti ko a kwantar da su tare har sai jaririn ya kara nauyi.
Hukumar lafiya ta Duniya ta bayyana cewa daga cikin jarirai goma ana haifar bakwaini daya. A kowace saniya 40, daya daga cikin wadannan yara na mutuwa.
Rahoton ya hada da hasashen da aka sabunta na WHO da UNICEF kan yawaitar bakwaini, wanda Cibiyar Kula da Lafiya ta Landan ta fitar.
A takaice dai, an gano yanayin haihuwar bakwaini bai sauya ba a kowanne yanki na duniya a shekaru 10 da suka gabata, kuma wasu miliyan 152 sun fuskanci haihuwa a matsayin bakwaini a tsakanin 2010 a 2020.
Haihuwar bakwaini na daya daga cikin yanayin da ke janyo mutuwar yara kanana, inda ke kashe daya daga cikin yara biyar kafin su cika shekara biyar da haihuwa.
Wannan kudirin doka na Tanzania na jiran amincewar majalisar dokoki.
Labari mai dadi shi ne yadda Shugabar Kasar tanzania Samia Saluhu Hassan ta bayyana goyon bayanta ga kudirin dokar, wanda zai sanya a aiwatar da ita cikin auri.
Sauran bangarorin da aka nemi a yi wa kwaskwarima a dokar sun hada da bayar da dmaar aikin rabin rana na tsawon watanni shida ga matan da suka haifi bakwaini bayan sun dawo aiki daga hutun haihuwa, da kuma hutun kwanaki 14 mai amon kwanaki 3 ga iyaye maza da aka yi wa haihuwa.