Wadanda suka yi ido hudu da mutuwa suna yawan tuno wasu manyan abubuwa da suka faru da su a baya, da hango sauki bayan tsanani da ganin wasu abubuwa da ke faruwa nesa da su da ganawa da wasu danginsu da suka rasu ko kuma tuno wasu manyan abubuwa da suka faru a rayuwa.
Kasancewar wadannan labaran da mutane da yawa daga bangarori mabambanta suka bayar suna kama ta fuskoki da dama, hakan yana ishara ne da cewa akwai yiwuwar masana kimiyya za su iya gano wani abu da ba a fahimce shi ba a baya.
Wani bincike da aka wallafa ranar Litinin a Mujallar Proceedings of the National Academy of Science (PNAS), masu bincike a Jami'ar Michigan sun gano wasu hujjoji kan yadda aikin kwakwalwar wasu wadanda suke gab da mutuwa ya karu.
Yayin da ba wannan ba ne binciken farko, amma abin da ya bambanta wannan bincike da na baya shi ne yadda ya fayyace abubuwa sosai "irin yadda da ba a taba gani ba a baya," in ji babbar marubuciya Jimo Borjigin.
Dakin binciken Jimo Borjigin ya mayar da hankali wajen fahimtar yadda kwakwalwa ke tafiyar da wasu ayyuka na da suka jibanci natsuwa
Masu nazarin sun duba bayanan wasu marasa lafiya hudu wadanda suka mutu sanadiyyar bugun zuciya yayin da aka dora su a kan wata na'ura mai suna Electroencephalogram (EEG) monitoring.
Duka su hudun sun yi doguwar suma ne kuma aka cire su daga kan na'urar da ke taimaka musu saboda fahimtar da aka yi cewa cutar da ke damunsu ta wuce taimakon da likitoci za su ba su.
Lokacin da aka cire su daga kan na'urar da ke taimaka musu yin numfashi, biyu cikin marasa lafiyan hudu – mace 'yar shekara 24 da wata dattijuwa mai shekara 77 – an fahimci cewa bugun zuciyarsu ya karu da kuma karuwar aiki a kwakwalwa, wadanda suke alaka da kasancewa cikin hayyaci.
Binciken farko – ciki har da wani fitattacen bincike da aka wallafa a 2022 kan wani dattijo mai shekara 87 wanda ya rasu bayan wani abu ya fada masa, an ga karuwa wajen aikin kwakwalwarsa.
Binciken Jami'ar Michigan din ya kuma yi nazari mai zurfi kan sassan kwakwalwa daban-daban, inda aka ga "yadda ayyuka ke karuwa a bangaren gaban kwakwalwa".
Wurin ya kunshi bangarori uku da ake kira temporal da parietal da kuma occipital lobes, wadanda suke da alaka da canjin yanayin hayyaci.
"Idan wannan bangaren kwakwalwar ya fara aiki to hakan yana nufin mara lafiya yana ganin abubuwa ko jin abubuwa kuma zai iya fara jin alamun abubuwa," in ji Borjigin, ya kara da cewa bangaren "yana aiki sosai kenan."
An yi nazari kan aikin kwakwalwa da bugun zuciya a kowace dakika, har tsawon sa'o'i na karshe na rayuwar mara lafiya, hakan ya karawa nazarin karfi in ji ta.
Ba a iya fahimtar abin da ya sa aka kasa fahimtar yanayin hayyacin biyu daga cikin marasa ba yayin da sauran biyun an fahimci wani abu.
Borjigin ta yi fatan zuwa gaba ta sake tattara bayanan daruruwan mutane – inda hakan zai sa wata kila a samu wadanda za su rayu da yawa.
Wata hanya da za a iya yin hakan shi ne samar da wani yanayi mai kama da mutuwa yayin ake duba yanayin mara lafiyar a dakin bincike.