Daga Firmain Eric Mbadinga
Marie Edu, wata matashiya 'yar Kamaru da ke zaune a kasar Cote d'ivoire tana shirin kwanciya bacci a lokacin da take amsa wa masu yi mata sai da safe ko "a yi mafarki mai dadi" da wani salo da ba a saba gani ba.
"Ni ba na mafarki," Marie ta bayyana. Ba da wasa take ba. Marie ba ta san yaya ake mafarki ba kamar yadda mutane ke yi. Ko da a ce ta taba yi ma, to matashiyar ba ta iya tuna yadda yake.
"Na kan ji labaran mafarkan da mutanen da ke kusa da ni suke yi, amma ni ban taba yin kwatankwacin mafarki ba. Babu wani abu da zan iya tuna cewa na yi mafarki, ko kadan! Don haka, zan iya cewa ba na mafarki," Marie ta shaida wa TRT Afrika.
Akwai mutane irin Marie a fadin duniya wadanda wasu kwararru ke kiran su da "mutanen da ba sa mafarki". Sai dai, kwararru kan dabi'a na ci gaba da tafka muhawara kan ko akwai mutanen da ke iya rayuwa har su mutu ba su taba yin mafarki ba.
Isabelle Arnulf, shugabar sashen masu matsalar bacci a asibitin Salpêtrière da ke Paris, kwanan nan ta shaida wa sashen lafiya na mujallar Ça m'intéresse cewa akwai kashi 0.38 cikin 100 na mutanen duniya da ba sa mafarki.
A cikin bayaninta, kwararriyar kan sha'anin kwakwalwa kuma farfesa a jami'a ta fayyace bambancin da ke tsakanin "mutanen da ke yin mafarki amma ba sa iya tunawa da kuma wadanda kwata-kwata ma ba sa yin mafarkin saboda wasu dalilai. Wadanda suka fada cikin rukunin farkon sun kai daga tsakanin kashi 2.7 zuwa 6.1 cikin 100 na al'umma.
Wani kwararre a harkar bacci kuma likitan masu lalurar tabin hankali, Pierre Geoffroyc ya ce ba abin mamaki ba ne don mutum ba ya mafarki, sai dai ba a cika samun masu irin wannan dabi'a ba.
Mafi yawan mutane ba sa tunawa da abin da suka yi mafarkin akai. Bincike da dama sun nuna cewa idan ka farka cikin dare, kana iya rubuta irin mafarkan da ka yi. Amma su irin wadancan mutane ba za su taba iya yin hakan ba.
Komai yana cikin kwakwalwa
A bangaren Marie, tun lokacin da ta fahimci yanayinta sai ta fara bincike don gano ko lafiyarta kalau ko kuma akwai mutane da ba sa mafarki irinta.
"Na kusa shekara 30 da haihuwa, amma ban taba haduwa da wani wanda ya ce min bai taba mafarki ba. Shi ya sa ni ma ba na gaya wa mutane saboda ba na so a dinga yi min dariyar hakan," ta fada.
Duk da cewa Marie a karan kanta ne ta yi bincikenta, akwai bayanan kimiyya da dama na kwararru da mujalloli.
A fayyace, mafarki "wani yanayi ne da ke faruwa a lokacin da ake bacci, wanda kuma a kan iya tuna shi gaba daya ko wani bangare na abin da ya farun."
Sannan masu bincike sun yi ittifakin cewa akwai yiwuwar a samu mutanen da ba sa yin mafarki. Hakan a wasu lokutan kan faru ne sakamakon tasirin bugawar zuciya da lalacewar kwakwalwa ko wani tashin hankali da ya taba faruwa da ke shafar kwakwalwa.
Mutanen da suka daina yin mafarki ko kuma ba sa mafarkin gaba daya, suna karfafa mana gwiwar mu dinga kallon mafarki ta wata fuskar daban, mu dinga kallon su a matsayin wadanda bai kamata ana raina su ba.
Sako mai ma'ana
A Afirka da ma wasu sassan duniya ana ganin mafarki a matsayin wani abu mai ma'ana. Da yake mafarki wani yanayi ne mai zuwa da hotunan al'amura da dama, yakan danganci tsari da yanayin da mutum ke ciki ne.
A hannu guda kuma, ayyukan da Sigmund Freud ya yi na kimiyya a shekarar 1899 ne suka zama silar binciken kimiyya kan batun mafarki.
A ganin Freud, mafarki wani yanayi ne na wani abu da ba ma a sa ran faruwarsa ba, kafin da kuma bayan bincikensa, an sha fassara mafarki ta fuskar addini da al'ada.
A baya-bayan nan, azamar Marie ta neman amsa kan dalilin da ya sa ba ta mafarkai ya bude kofa ga sarkakiyar da ke tattare da batun.
Tabbas, sarkakiyar da ke tattare da mafarki ta kayatar da dan'adam a tsawon rayuwa, inda a lokuta da dama mafarkin kan zo daidai da wani abu da ke faruwa a zahiri.