Masana sun ba da shawarar ziyartar likitan hakori akalla sau ɗaya a shekara. Hoto: Reuters

Daga Abubakar Famau

Tallace- tallacen man wanke hakora a mafi yawan lokuta kan sanya masu saye cikin damuwa sakamakon yadda ake nuna saukin samun hakora farare kal-kal idan mutum ya dan matsa man a kan magogin wanke bakinsa, tare da tabbacin zai cire masa duk wani dattin da ya makale a kan hakora, sai dai da wuya a iya cimma wannan manufa.

Abin da ba sa fada shi ne hanyar samun ingantaccen hakora masu lafiya- na halittar dan'adam ko akasain haka- tare da samun fuskar da za ta kalli duniya cike da murmushi.

Tsaftar baki, gami da jerarrun hakora da numfashi mara wari, suna da matukar muhimmanci ga lafiya da jin dadin dan'adam baki daya.

Ka’ida ta farko ita ce kowane mutum ya ga likitan hakori akalla sau daya a shekara, ko da kuwa babu wata matsala da ta bayyana a hakoransa.

Likitoci sun bayyana cewav cututtuka irin su cutar zuciya da ciwon sukari da matsalolin da suka shafi numfashi da sauran wasu matsaloli na kiwon lafiya suna da alaƙa da yanayin tsaftar baki.

Mutane miliyan 400 na fama da cututtukan hakori a Afirka. Photo: TRT Afrika

Duk da cewa wanke baki ba wani aikin kimiyya ba ne, amma mutane kadan ke mai da hankali wajen bai wa bakinsu kulawa kamar yadda suke kula da lafiyar jiki baki daya.

Ana samun hakan ne sakamakon wasu dalilai, ciki har da bukatar karin ilimi game da muhimmancin kulawar hakora, sannan a wasu lokutan saboda gujewa tsadar farashin jinyar hakora musamman dasa hakora na wucin gadi.

Bincike ya nuna cewa sama da mutane miliyan 400 ne ke fama da cututtuka da suka shafi hakora a Afirka, inda abubuwa da dama ke taka rawa wajen samun matsala ta lafiyar hakora.

Kazalika an gano rashin tsaftar baki da kuma yawan cin abinci masu tsaki a matsayin manyan dalilai da ke haddasa matsalar hakori.

Ma'aunin wannan matsala shine yadda ake dada samun wuraren ayyukan kula da hakora musamman a birane.

A birnin Dar es Salaam na Tanzaniya, alal misali, akwai asibitocin 250 da ke kula da lafiyar hakori da kuma samar da hanyoyin kwalliyar hakora iri daban-daban.

Kalubalen samun farashi mai rahusa

Yayin da ayyukan likitan hakori ke kara bunkasa, yawancin mutane ba za su iya biyan makudan kudade don kula da hakoransu ba, musamman hakora na wucin gadi sakamakon tsadarsu.

Kimanin kashi 90 cikin 100 na asibitocin hakori suna shigo da hakoran roba da sauran na'urorin dashen hakaro dalilan da suka sanya wadannan kayayyaki ba su isa ga yawancin jama'a.

Dakta Joshida Benjamin Cosmas, wani likitan hakori ne a Dar es Salaam, ya ce mafi yawan majinyatansa na fama da tsadar dashen hakora.

"Farashin jerin hakora na wucin gadi yana tsakanin dala 350 zuwa dala 900, tare da kalubalen jinya ta tsawon wata daya zuwa uku,'' in ji likitan.

''Ana biya shillings 30,000 zuwa 100,000 wajen dasa hakori daya a Tanzaniya, kwatankwacin dala 20 zuwa 40'', a cewar Dakta Benjamin a yain hirarsa da TRT Afirka.

Sabbin hanyoyi

Hakora da ake samarwa sun fi  arha da 80% fiye da na shigo da su. Photo: TRT Afrika

Abbas Mshindo, wani mai zane a wurin gwaje-gwajen fasaha na Lab X Technologies a Tanzaniya, yana daya daga cikin matasan da ke kokarin cike gibin da ke tsakanin aikin kula da hakora da farashi mai rahusa.

Ta hanyar amfani da fasahohin da ake kirkiro su daga cikin gida, Abbas da tawagarsa sun samu hanyar kera hakora na wucin gadi cikin sauri sannan a farashi mai rahusa fiye da yadda ake shigo da su daga kasashen waje.

"Muna iya fitar da hakora da muka kera na wucin gadi har 18 a rana, kwatankwacin hakora 126 a mako," in ji Abbas.

Saukin farashin hakoran da suke kera wa ya kai kusan kashi 80 cikin 100 na wadanda ake shigo wa da su daga Dubai da Indiya da kuma China.

Ana iya cewa yanzu tafiya ta soma kankama ma wadannan matasa da suke neman tallafi don shawo kan kalubalen da ke kan gabansu.

"Bangaren kiwon lafiya yana da ka'idoji da yawa, hakan na da kyau, amma matsalar da ke ci mana tuwo a kwarya a yanzu ita ce, lokacin da hukumomi ke dauka wajen tabbatar da tsarin samfuran kayayyaki'', a cewar Abbas.

Ana amfani da fasahar 3D ta ci gaba wajen samar da haƙoran yin dashe. Photo: TRT Afrika

Baya ga wannan kalubale, ya yi nuni da cewa, har yanzu akwai bukatar kara wayar da kan jama'a game da yadda ake amfani da fasahar 3D wajen samar da hakora.

“Wannan ya zama mana matsala hatta wajen samun gogaggun ma’aikata,” in ji Abbas.

Amma ga wadanda za su iya biyan kudin samun jerarrun hakora na wucin gadi, za a iya cewa Abbas ya yi dacen samun sana'ar da za ta samar masa riba.

TRT Afrika