Madubin hangen nesa a sararin samaniya na James Webb a karon farko ya gano wani waje da ruwa ke kwance a kewayen da duwatsun astiriyod masu zagaye a saramaniya, suka yi cincirindo a Ungwaurmu ta Rana (Solar Sysytem), da masana kimiyya suka yi amannar cewa watakila nan ne ainihin inda tekunan da suke duniyarmu ta Earth suka samo asali.
Gano wannan lamari ka iya bai wa masana kimiyya masaniya a kan yadda tekunan duniyarmu suka samu, kamar yadda hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka NASA ta fada a wata sanarwa.
'Yan sama jannatin da ke aiki da madubin hangen nesa mai kaifin dauko hotuna tar-tar daga nesa na Webb, da kudinsa ya kai dala biliyan 10, sun tabbatar da cewa sun ga ruwan ne a kusa da wata tauraruwar Comet mai suna 238P/Read, wacce ke zagayenta tsakanin duniyar Jupiter mai cakudadden gas da makwabciyarmu Mars.
Binciken ya gano cewa ruwan kankara zai iya zama a yankin duwatsun astiriyod mai zafi da ke zagaye Jupiter, NASA ta ce, ya kuma samar da asalin ruwan da ke duniyarmu ta Earth ta hanyar fadowar duwatsun astiriyod din cikin Earth a tun farkon lokacin da ake halittar duniyar tamu, biliyoyin shekaru da suka wuce, kafin ma a halicci dan adam.
Asalin samuwar ruwa a Duniyar Earth
Ruwa a kusa da tauraruwa kan kasance cikin yanayin iskar gas kuma watakila ya rabu ne daga wani abu mai kama da duniyar Earth, inda 'yan sama jannati ke tunanin taurarin comet su ne tushen ruwa a Earth, kamar yadda wani bincike da aka wallafa a Mujallar Nature ya bayyana.
"Abin da muka sani har yanzu shi ne babu wanda ya san dalilin da ya sa a duniyarmu ta Earth kawai ake samun ruwa da rayuwa, in ji Stefanie Milam, wani masanin kimiyya da ke aiki a sashen shirin samar da madubin Webb.
Milam ya ce fayyace yadda ruwa ke kwance a wurare da yawa a Unguwarmu ta Rana zai taimaka wajen yadda duniyoyin unguwar ke aiki da yadda ko watakila za a iya rayuwa a cikinsu kamar Earth.
Tauraruwar Comet 238P/Read tana nan a cikin zagayen da cincirindon duwatsun da ke shawagi a sararin samaniya suke.