Cutar TB na kashe mutane miliyan 1.3 a kowace shekara a duniya. Hoto: Wasu  

Daga Sylvia Chebet

"E! Za mu iya kawo karshen cutar tarin fuka!" Ba wai kawai wani taken ba ne. Taken ranar tarin fuka ta duniya na bana, wanda ake yi a duk ranar 24 ga Maris, ya nuna irin ci gaban da aka samu a fannin kimiyya da rigakafin cutar tarin fuka da ya taimaka wa Afirka wajen shawo kan wannan cuta mai saurin yaduwa.

Wani sabon binciken asibiti da aka gudanar a Cape Town na kasar Afirka ta Kudu, ya nuna cewa mafi yawan maganin cutar kanjamau yana aiki da kyau tare da ingantaccen maganin kariya ta cutar tarin fuka.

Gabaki ɗaya dai, maganin riga-kafin tarin fuka ko TPT ya ƙunshi wani tsari na maganin guda ɗaya ko fiye da haka wanda ake baiwa mai dauke da cutar da nufin hana yaduwarta, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.

Masanan da suka gudanar wa wannan bincike sun gano cewa, ɗan digon maganin riga-kafin cutar tarin fukar da aka bayar sau daya a mako har tsawon makkonni 12, yana da karfin inganta lafiya da kuma hana mutuwa.

Dokta Ethel Weld, mataimakiyar farfesa a fannin likitanci a Makarantar Magunguna ta Jami'ar Johns Hopkins da ke Amurka kuma babba a sashin bincike, ta ce akwai alamomin da suka tabbatar da ''sahihanci da juriyar hadin maganin''.

Kazalika masaniyar gwajin ta ba da tabbaci ga likitoci game da fara ba da maganin riga-kafin tarin fukar da wuri ga mutanen da ke cikin hadarin kamuwa da cutar.

An ware ranar 24 ga watan Maris a matsayin bikin ranar tuni da cutar tarin fuka (TB) a kowace shekara a duniya. Hoto: Wasu

“Muna sane da cewa ana samun mutuwar mutane kusan 200,000 da ke da alaƙa da cutar tarin fuka daga cikin masu dauke cutar kanjamau a kowace shekara.

Abin takaici akan wannan batu shi ne akwai yiwuwar hana mace-macen da ake samu sakamakon hakan,'' in ji ta.

“Tasirin maganin idan aka haɗa yana hana kamuwa da cutar da kuma duk wani illar da zai biyo bayan, wanda ba wai mutuwa kadai ya ke yi har da mummunan sakamako kan iyali da ‘yan'uwa.

Kazalika akwai nakasu da kuma tashin hankali na tattalin arziki da zamantakewa da za a yi fama da su," in ji Dr Weld.

Wadannan sabbin sakamakon suna da muhimmanci musamman ga yankin kudu da hamadar Sahara, wanda ke da nauyi mai yawa na cututtukan guda biyu.

A duk duniya, cutar tarin fuka na haddasa mutuwar mutane miliyan 1.3 a kowace shekara sannan illarsa na shafar miliyoyi mutane.

Ga majiyyaci, nauyin yaƙi da cututtuka biyu masu barazana ga rayuwa da ke haɗe da juna - yana da girma sosai.

Cututtukan biyun suna buƙatar magunguna masu ƙarfi da galibi ke barin marasa lafiya buƙatar ruwa sosai, Dr Weld ta ce yana da mahimmanci a sami gajeriyar hanya wacce za ta iya kashe cutar tarin fuka da cikin sauri.

"A lokacin da suka fi fama da rauni, dole maganin ya zama wanda za a iya jure masa don marasa lafiya su sami damar iya kammala maganin bisa ka'ida," in ji ta.

Tsarin amfani da maganin riga-kafin

Domin haɗin maganin ya yi tasiri, ya kamata a ba da shi nan da nan bayan an gano shi, a cewar Dr Weld.

Kwayar cutar ta tarin fuka tana kusan ko'ina, amma mutanen da ke da karfin garkuwar jiki su suka fi tsira daga yaduwar cutar.

Yana zama ba ya aiki ko a ɓoye a jikin wasu, sannan yana haɓaka zuwa cikakkiyar kwayar cutar tarin fuka lokacin da garkuwar jikin ya ragu, a cewar masana.

"Dole ne mu tuna cewa idan har za mu iya kawar da kwayar cutar tarin fuka, mu kawar da ita a lokacin da take kokarin haɓaka ba wai lokacin da ta mamaye ko ina ba, ta haka ne zamu iya fatattakar wa cutar." Inji Dr Weld.

Sabon maganin rigakafin cutar tarin fuka (TB) yana da matukar mahimmanci wajen magance cutar. Hoto: Wasu

Masana sun ba da shawarar an yi amfani da wannan tsarin a kowace kasa da ke fama da matsalar cutar tarin fuka ko kuma wuraren da cutar ta zama ruwan dare.

"Hanya daya tilo da za mu kawo karshen cutar tarin fuka ita ce idan muka bi tsarin hana yaduwar cutar.

"Yanzu muna da tsarin da za mu iya bi domin cimma hakan," in ji Gavin Churchyard, shugaban kungiyar kula da lafiya ta Aurum Institute da ke Johannesburg, a hirarsa da TRT Afrika.

Tsarin dokar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi ta wayar da kan jama'a game da yadda kimiyya ta ba da damar kawar da cutar tarin fuka ta hanyar nasara a riga-kafin cutar.

"A yau, muna da ilimi da kayan aiki da kuma kudurin siyasa don kawo karshen wannan cuta da ta shafe shekaru da dama kana ta kasance daya daga cikin manyan cututtukan da ke kashe mutane a duniya," in ji babban daraktan WHO Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus.

Sai dai, har yanzu nasarar samun maganin riga-kafin cutar ya yi kasa sosai.

A cewar WHO, ci gaban da aka samu wajen samar da sabbin hanyoyin gano cutar da magunguna da alluran riga-kafin har yanzu suna fuskantar tsaiko sakamakon rashin isasshen jari a wadannan fannoni.

Duk da hujjojin da ke nuna cewa saka hannayen jari kadan na iya haifar da gagarumin fa'idar ga kiwon lafiya da tattalin arziki a kasashe daban-daban, tare da samar da ribar da ya kai dalar Amurka 39 kan kowace dala da aka saka.

Kira don aiki tare

Hana kamuwa da cuta da dakatar da yaduwarta daga kwaya zuwa ciwo na da mahimmanci don rage cutar tarin fuka da kuma kawo karshen cutar mai kisa baki daya.

Don yin wannan, yana da mahimmanci a ba da maganin riga-kafin tarin fuka ga mutane da ke cikin haɗarin kamuwa da ita.

Dr Tereza Kasaeva, daraktan shirin tarin fuka na WHO a duniya, ta ce hukumar za ta ci gaba da ba da jagoranci yaki da cutar tarin fuka a duniya.

"WHO za ta yi aiki da dukkan masu ruwa da tsaki har sai mun kai ga ceto kowane mutum, dangi da al'ummar da suka kamu da wannan cuta mai kisa."

TRT Afrika