Masana sun shawarci mutane da su rika duba bayanai kan lokutan da amfanin abinci zai kare da kuma ko ya fara lalacewa. Hoto: Reuters

Daga Dayo Yussuf

Lokacin da 'yan sanda a Kenya suka kama katan-katan din madarar gari wadanda amfaninsu ya kare, hakan ya jawo mutane sun yi ta korafi kan al'amarin.

Da yawa sun damu da lafiyar 'ya'yansu da ma kansu. Sai dai kwace madarar da batun cewa shanta zai jawo matsala ga lafiya duka ba sabbin abubuwa ba ne a fagen kasuwanci a duniya.

Amma a matsayinka na mai amfani da kayayyaki sau nawa ka taba duba jikin abin da za ka saya don gane ko amfaninsa ya kare?

Bincike ya bukaci da ka rika yin haka a kodayaushe. Wani bincike da aka yi a Jami'ar Havard ya gano cewa cin abincin da amfaninsa ya kare zai iya jawo mutuwa da kuruciya.

Yayin binciken, masana kimiyya sun ciyar da kudaje da beraye abincin da ya gama amfani. Sakamakon yana da ban mamaki.

An gano abincin da amfaninsa ya kare yana rage tsawon rayuwar dabbar da aka ciyar da ita da kaso 10 cikin 100.

A zahiri, yawancin mukan gwammace mu yi amfani da ko da kuwa amfaninsa ya kare musamman idan lokacin amfani bai wuce ba sosai.

Ko da yake abinci yana da amfani ga lafiya da rayuwa, amma kuma cin abincin da ya gama amfani yana da hadari. Hoto: Reuters 

Masana kan abinci sun akwai lokutan da babu abin da zai same ka, amma hakan ya danganta kan yadda aka ajiye abincin.

Sun ce ajiye abincin a wuri mai sanyin da ya kai na kankara, hakan zai iya taimaka wa a wasu lokuta wajen hana abincin lalacewa – fiye da lokacin da aka rubuta a jikin kwalinsa ko ma'ajinsa.

Dokta Alice Ojwang, masaniya ce kan abinci a kasar Kenya, ta ce yana da sauki ka gano abincin da ya gama amfani daga kwalinsa ko mazubinsa ko kuma ma'ajinsa.

"Mutane da yawa ba su san yadda za su gane abinci ya gama amfani ba," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

"Za ka iya sayo 'ya'yan itace ko ganyenka amma ka kasa gane cewa ko ya gama amfani, sai dai idan ka ga ya fara rubewa."

Wannan ya zama matsala mai wuya da gwamnati za ta iya magancewa a bangaren masu sayar da kaya a gefen titi.

A ranar 17 ga watan Mayu, Kenya ta sanar da dakatar da jami'ai 27, ciki har da 'yan sanda da kuma wasu ma'aikatan kan batun sayar da wata nau'in siga da ba cancanci dan Adam ya yi amfani da ita ba kuma ana amfani da wannan nau'in ne wajen samar da sinadarin ethanol a masana'antu.

Masana sun ce za a ci gaba da samun matsaloli irin wadannan matukar mutane suka ci gaba da cin abincin da ya gama amfani.

Hadarin cin abu da ya lalace

Abincin da suka lalace kamar nama da kifi zai jawo bacin ciki daga kwayoyin bacteria nau'insu: Salmonella, E. coli, H. pylori da sauransu.

Kuma za ka iya fada wa hadarin kamuwa da kwayoyin bacteria masu hadari kamar fungi da ake samu a biredin da ya fara lalacewa.

Wannan zai iya jawo bacin ciki ko borin jini, kuma wasu lokuta zai iya jawo asthma da ciwon mafitsara da kuma ulcer.

Abincin da suka gama amfani ba sa karawa jiki lafiya, wato babu wani abu da kake samu daga gare su wanda hakan yake sa fada cikin yanayin barazanar kamuwa da cututtuka.

Ana samun kwayoyin fungi da nau'in abincin da aka yi daga alkama bayan amfaninsa ya kare. Hoto: AA

Dokta Ojwang ta gargadi cewa hatta abincin da aka ajjiye su cikin sanyin kankara za su iya zama matsala. "Wani abinci daya mai ban mamaki da zai iya jawo ma bacin ciki shi ne ice cream.

Hadarin shi ne idan abinci ya zama kankara kuma daga baya ya koma ruwa-ruwa za ka iya fada wa hadarin kamuwa da kwayoyin bacteria irinsu Listeria da ke kama 'ya'yan itace da ganyenyayyakin da suka yi kankara," in ji ta.

Alamomin da ake ji idan an ci abinci da ya lalace kuma ya zamawar jiki matsala su ne: ciwon kai da zazzabi da ciwon ciki da gudawa da kuma amai.

Masana sun shawarci jama'a da su garzaya asibiti da zarar sun ji wadannan alamomi saboda wasu suna iya jawo barazana ga rayuwa.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bukaci jama'a da su rika duba bayanai kan karewar amfanin kayan da za su saya gabanin su saya.

Abu ne da ake yawan gani a manyan kantuna suna wato karya farashin kayayyaki wadanda suke gab da gama amfani; saboda haka a kula sosai kafin sayan kayan abinci.

Dokta Ojwang ta ce abu mafi muhimmanci shi ne a kodayaushe kasan abin da za ka ci duk cewa akwai 'yar matashiya.

"Ka san cewa madarar da ta fara tsami ba ta cutarwa. Ba ta da matsala kuma za ta yi maka amfani a jiki. Idan madara ce da aka tatso daga dabbobi, za ka iya amfani da ita wajen yin cikwi da kuma yoghurt," in ji ta.

TRT Afrika