Daga Maryam Bugaje
Wata dalibar jami’a a Nijeriya, Amina (ba sunanta na asali ba kenan), ta san yadda ake ji idan mutum ya ki canja launin fatar jikinsa – mafi muni ma idan aka tilasta masa yin irin wannan tunanin.
“Ana yawan tsokana ta saboda ni kadai ce ke da fata mai duhu a tsakanin ‘yan uwana mata da sauran danginmu, wadanda dukkaninsu suna da haske,” a cewar Amina, ‘yar kimanin shakara 26, a hirarta da TRT Afirka.
Irin wannan tsangwama da mutane, ciki har da danginta, ke yi wa Amina saboda launin fatar jikinta, ya jefa ta cikin mawuyacin hali na rashin samun kwarin gwiwa, lamarin da ya kara tsananta bayan ta fara jami'a.
Ba a jima ba ta fada tarkon abin da wata likitar fata da ke jihar Legas, Dokta Basirat Akanbi, ta ce “cututtuka”: na man bilicin din fata.
"Yawancin kawayena, ko dai fatarsu ta asali mai haske ce ko kuma suna amfani da mai na kara hasken fata.
"Da alama an fi son wadanda suka fi hasken fata sannan sun fi daukar hankali. Don haka, na fara amfani da wadannan samfuran man bilicin," a cewar Amina.
Da farko mayukan bilicin din da take amfani da su sun samar mata kwanciyar hankali, amma daga bisani sun zama illa a gare ta.
"Sun canja launin fatata, musamman gwiwona, lokacin da na yi kokari na daina, sai kuraje suka feso min, hakan ya sa na sake koma wa amfani da wadannan mayuka, amma a shekarar da ta wuce na daina," in ji Amina.
Mutane da dama, musamman maza, suna daukar fata mai haske a matsayin wacce ta fi kyawun gani.
Wannan hasashe yana matukar ingiza wasu da ke neman cin moriyar wannan manufa, lamarin da ke sanya su fara amfani da man shafawa da sabulai da ke sauya launin fata na bilicin don su kara hasken fatar ko su yi fari.
Barazana ga rayuwa
Kalmar "launi", da wata marubuciya Ba'amurkiyya Alice Walker ta rubuta a cikin wata makala a shekarar 1982, na bayyana yadda ake kyama ko nuna wariya ga mutane masu bakin launin fata.
“A lokacin da muka kai ziyarar karshe yankin Makoko, wata unguwar marasa galihu a Legas, kusan kashi 90 cikin 100 na mutanen da muka hadu da su suna amfani da mayukan canja launi fata na bilicin.
"Abin da ya fi damun mu shi ne na iyaye musamman mata da suke shafa wa kananan 'ya'yansu ciki har da jarirai man,” in ji Dr Akanbi.
Al'adar dai ita ce akan samu samfurin man da ke dauke da sinadarai na steroid, galibi ana kiransu da ‘tripple- action cream’ sannan a hada tare da man kadai kafin a shafa a fatar yara.
"Iyayensu na ikirarin cewa suna sanya fatar ta yi taushi ne kawai da man shea, amma da aka ci gaba da bincike an gano cewa suna hada mayukan da ke da sinadarin steroid ne kadai," in ji Dokta Akanbi.
Yawanci sinadarai da ake hada man kara hasken fata sun kunshi abubuwa da ka iya illa da barazana ga rayuwar dan Adam idan aka yi amfani da su na tsawon lokaci ba tare da neman shawarar likita ba.
Takamaiman sinadarai uku da aka fi samu a cikin wadannan samfuran man kara haske fata masu cutarwa kuma sun yadu sosai a duniya.
Motsewar fata
Duk da matakan takaita amfani da mayukan, ana ci gaba da samun su cikin sauki a yawancin kasashen Afirka, kuma yanayin da ake amfani da su ko kuma tsawaita amfani da suna iya cutar da lafiyar mutum.
Sinadarin steroids, babban jigo ne ga irin wadannan mayukan da ke da babban hadari.
"Yin amfani da sinadarin steroid na tsawon lokaci na iya haifar da motsewar fata, da ke bayyana jijiyoyi masu launin shudi ko kore sannan suna sanya tsufa da wuri da nankarwa da rashin daidaita launin fata da kuma rage garkuwar jikin fata,” kamar yadda Dokta Akanbi ta yi gargadi.
Kazalika ana amfani da sinadarin Hydroquinone wanda hukumar kula da abinci da magunguna ta Amurka ta ce shi ma yana da hadari kuma yana iya haifar da cutar kansa.
A cewar Dokta Akanbi, yana iya haifar da rashin daidaituwar launin fata, launin ruwan lemo ko ruwan kasa da kuma wani yanayin da aka fi sani da exogenous ochronosis, wanda galibi ake bayyana shi a matsayin kunar rana a kan fuska.
Haka kuma, yin amfani da sinadarin hydroquinone na tsawon lokaci na iya haifar da cutar koda da cutar hanta a cewar masana.
Mercury, sinadari na uku da ake amfani da shi wajen hada man, an fi sanin sa wajen kara hasken fata, amma duk da haka, kasancewar sa a cikin samfuran hada man na iya cutarwa don haka yana da kyau a yi taka-tsantsan da shi.
Har jariran da ba a haifa ba
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, ana saka sinadarin mercury a cikin yawancin man shafawa da sabulai na kara hasken fata wadanda ke iya zama illa ga lafiyar jiki.
Yana kuma cutar da koda da sanya kuraje da canza launin fata da samar da tabo a kan fata da kuma sanya damuwa da tashin hankali har ma da taba lafiyar kwakwalwa da dai sauransu.
''Sinadaran da ake hada mayukan kara hasken fata ba wai kawai suna haifar da hadari ga mai amfani ba su ba ne – illar na iya shafar jarirai da ke shan nono.
Sannan sinadaran na iya gurbata kayayyakin abinci da aka hada su tare ko cikin ruwan datti da aka wanke wasu kayan kwalliya a ciki," in ji Hukumar Lafiya ta Duniya.
Idan aka zubar da wadannan kayayyakin, ana fitar da sinadarin mercury a wuraren da ruwa ke kwarara kuma idan suka shiga cikin muhalli sukan haifar da wani tsari na 'methylation'.
Wannan tsari na sinadarin mercury da ya sauya daga baya na iya shiga cikin kayayyakin abinci, musamman cikin kifi, inda ake iya samun nau'i gubarsa mai yawa a ciki wanda aka sani da methylmercury.
Mata masu juna biyu da suka ci kifin da ke dauke da nau’in sinadarin methylmercury na iya sanya wa jariransu da ke ciki, yanayin da ka iya illa ga jariran.
Don magance wannan yanayi dai, wata yarjejeniyar kasa da kasa da aka fi sani da Yarjejeniyar Minamata ta bayyana cewa giram daya shi ne iyakar sinadarin mercury da ya kamata a saka cikin kayayyakin hada mayukan kara hasken fata.
Takunkumai masu tsauri
A wani bincike da “Zero Mercury Working Group” tare da Cibiyar Nazari ta “ Diversity Research” suka gudanar a shekarar 2018 sun gwada samfuri sama da 300 daga kasashe 22.
Sun kuma gano cewa kusan kashi 10 cikin 100 na mayukan kara hasken fata sun wuce iyakar da aka sanya musu.
Wasu samfuran mayukan suna dauke da fiye da adadi 100 na yanayin da aka tsarin musu.
Don takaita yawan amfani da wadannan mayuka masu cutarwa, Dr Akanbi ta ce ana bukatar wasu shirye- shirye da karin hanyoyin wayar da kan jama’a da kuma ka’idoji suka da su rike kamfanonin da ke hada wadannan mayuka da alhaki.
"Ya kamata a samar da wasu dokoki da za su haramta amfani da mayukan kara hasken fata ga jarirai da yara, a sanya wa masu hada irin wannan mai su biya haraji mai yawa.
Sannan a takaita amfani da man ‘tripple action’ sannan a daina sayar da shi a kan kanta a wuraren sayar da magungunan,” in ji ta.
Ga dalibar ‘yar Nijeriya, Amina, fahimtar da ta yi game da hadarin da ke tattare da kokarin sauya kamanninta, na iya zame mata babban bala’in ko kalubale mafi muni fiye da yadda ake mata shagube da ba’a a baya.
Amma mata irinta da dama na iya rasa karfin gwiwar da suke bukata.