Daga Pauline Odhiambo
Taro na farko na duniya kan batun maganin gargajiya wanda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta shirya a Jihar Gujarat ta India ya hada kan ministocin lafiya da masana kimiyya da likitoci daga kasashe 88.
Taron wanda aka yi shi tsakanin 17 zuwa 18 ga watan Agusta, an yi shi ne domin fito da hujjoji kan wasu alfanun da ke tattare da magungunan wadanda za a iya amfana da su a duniya baki daya.
Wannan taron yana da muhimmanci matuka ga Afirka inda kashi 80 cikin 100 na al’ummar nahiyar ta dogara ne kan magungunan gargajiya domin magance cututtuka.
A wasu kasashe da ke nahiyar, adadin ma ya wuce haka. Alkaluman da ake da su a kasa sun bayyana cewa adadin mutanen da suka dogara da maganin gargajiya ya kai kashi 90 cikin 100 a Burundi da Habasha.
Sai a Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo da Afirka ta Kudu kashi 80 sai kuma Benin da Cote d’Ivoire da Ghana da Mali da Rwanda kashi 70 sai kuma kashi 60 a Tanzania da Uganda.
Dokta Bruce Aylward, mataimakin babban darektan WHO kan harkokin kiwon lafiya na duniya, ya ba da shawarar samar da ingantacciyar hanyar tabbatar da shaida "don bai wa ƙasashe damar haɓaka ƙa'idoji da manufofin da suka dace game da magungunan gargajiya, na haɗin gwiwa, da haɗin kai".
Ƙoƙarin da ake yi na saka ka’idoji a bangaren maganin gargajiya ba wai kawar da harkar za a yi ba, kamar yadda ya yarda da yaduwar su a cikin al'ummomi, inda aka samu hujjoji da suka tabbatar da amfaninsu.
Wani rahoton 2023 wanda Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi ya nuna cewa kaso 40 cikin 100 na magungunan asibiti na da wani sashe na maganin gargajiya.
Kamar yadda aka bayyana a taron na WHO, magunguna da dama kamar irin su aspirin da artemisinin da kuma na cutar dajin yara na da wasu sinadarai daga magungunan gargajiya.
Sai dai a duniyar da mutane da dama har yanzu suke hada maganin gargajiya da tsafi ko maita a Afirka, hada maganin gargajiya ta wannan fannin da na zamani yana da wuya.
Duk da shakku a wasu bangarori, Refiloe Letuma, mai shekaru 30 mai maganin gargajiya a Afirka ta Kudu, ta tabbatar da cewa magungunan gargajiya na da muhimmanci matuka a tsarin kiwon lafiya na zamani.
Refiloe wadda kwararriya ce a bangaren ilimin kwamfuta, na kiran kanta a matsayin ‘sangoma’ – wanda suna ne da ake bai wa bokaye da likitocin gargajiya masu amfani da rauhanai a al’adar Afirka ta Kudu.
“Wasu mutane na guduna idan suka gano cewa ni sangoma ce. Yana damuna a farko, amma a halin yanzu na koyi na yarda da hakan,” kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika. Ta bayyana cewa akasarin iyalanta da ‘yan uwanta suna ba ta kwarin gwiwa.
Tsirrai masu warkwarwa
Hukumar WHO ta ce maganin gargajiya na Afrika shi ne amfani da itatuwa da wasu al'adu don samar da waraka da kariya daga cututtuka da inganta lafiya jiki da ta kwakwalwa.
Refiloe wacce mai bin addinin Kirista ce kuma tana ba mutane magungunan gargajiya kusan shekara uku kenan. "Mutane da yawa ba su fahimci abin ba, inda suke cewa masu maganin gargajiya na bin addinin gargajiya," in ji ta.
"Abin da muke yi shi ne muna kiran Ubangiji kafin mu fara komai. A aikina na bayar da magani, ina farawa da yin addu'o'i ne."
Refiloe, wadda take ba mutane maganin gargajiya, tana da rijista da Kungiyar Masu Bayar da Maganin Gargajiya ta Afirka ta Kudu wadda take kawo tsari a aikin ta hanyar da takardar shaida ga masu yi.
"Da takardar shaidar za ka iya zuwa ko ina don neman itatuwa. Misali zan iya tafiya zuwa Mozambique don samo itatuwa kuma na dawo Afirka ta Kudu ba tare da fuskantar wani kalubale ba," in ji Refiloe.
Akwai akalla masu bayar da maganin gargajiya 200,000 a Afirka ta Kudu – wato adadin ya nunka na likitoci kusan sau goma – wanda ake da kimanin 27,000 a kasar.
Bayanai daga Hukumar WHO sun nuna cewa ana nazari kan itacen Sutherlandia microphylla da ake samu a Afirka ta Kudu wajen maganin cutar kanjamau.
Masana sun yi amannar cewa itacen yana kara kuzari da dandano baki da kiba. "Muna amfani da ganyen African potato wajen wanke jinin jikin mutum," in ji Refiloe.
Hypoxis hemerocallidea ko African potato ko kuma Star grass, magani ne ga mutanen kasashen kudancin Afirka ciki har da Mozambique da Zimbabwe da kuma Afirka ta Kudu.
Makomar magani
Babban taron farko kan magungunan gargajiya na hukumar WHO ya ce kasashe akalla 100 ne ke da tsare-tsare a kan magungunan gargajiya.
A wasu kasashe mambobin WHO, magungunan gargajiya suna cikin tsarin hanyoyin kula da kiwon lafiya na inshorar lafiyar kasashen. Mutane da yawa suna shan magungunan gargajiya wajen neman kariya da magance cututtuka da ba sa yaduwa da sauransu.
Yayin da yake jawabin rufe taron Dokta Hans Kluge wato daraktan hukumar WHO a Turai ya ce "Tare da ku mana sauya al'amura, muna kara fito da hanyoyin magani da kiwon lafiya."
Ya ce babban aikin da ke gaba shi ne mu hada gwiwa don samar da hanyar da ta dace wajen shigo da magungunan gargajiya cikin tsarin kiwon lafiya na duniya.
"Mun sake nanata muhimmancin samar da hujjoji da aikinsa da ingancinsa da rashin cutarwar magungunan gargajiya. Wannan yana nufin samar da hanyoyin zamani wajen yin nazari a kansa," in ji shi.
Kamar yadda Shugaban Hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce babban tasirin maganin gargajiya shi ne "fahimtar da muke da shi kan dangantakarsa da lafiyar dan Adam da kuma muhallinsa."
Ya bukaci a rika samar da karin bayanai da dabaru ta yadda za a rika amfani da shi, inda ya ce ya kamata duniya ta fahimci abin da ke faruwa a zahiri na yadda mutane da yawa da ke matalautan kasashe suke dogaro da magungunan gargajiya.
"A kaf tarihi, a duka kasashe da al'adu mutane sun yi amfani da magungunan gargajiya wajen kiwon lafiyansu da walwalarsu," kamar yadda Shugaban WHO ya bayyana yayin babban taron a Indiya.
"Wannan ya sa WHO a shirye take wajen taimaka wa kasashe su bunkasa magungunan gargajiya," kamar yadda ya ce yayin da ya ci gaba da magana.
Akalla kasashe mambobin WHO guda 170 ne suka bukaci bayanai da hujjoji don su samar da tsare-tsare da dokoki kan amfani da magungunan gargajiya ta hanyar da ba zai cutar ba.
Dokta Shyama Kuruvilla, babban Mai bayar da shawarwari ne kan tsare-tsaren magungunan gargajiya na hukumar WHO ya ce "a zahiri yake cewa aikin da ke gabanmu babba ne wato yadda amfani da kimiyya wajen zurfafa fahimta da bunkasa magungunan gargajiya wajen inganta lafiyar mutane da walwalarsu, ba tare da cutar da duniyar da muke ciki ba."