Daga Sylvia Chebet
Ashley Summers, Ba'amurkiya wacce take da 'ya'ya biyu, ta je hutawa ne a kusa da tafkin Freeman da ke jihar Indiana a ranar 4 ga watan Yulin a karshen mako, inda ta fara jin cewa babu isasshen ruwa a jikinta kuma ta fara jin jiri.
Jim kadan bayan shan kwalabe hudu na ruwa da ya kai lita biyu a cikin minti 20, sai ta suma. 'Yan uwanta sun garzaya da ita gida, amma daga nan ba ta sake farfadowa ba.
Ciwon da asibiti ya ce ya yi ajalinta ya ba da mamaki. Ta tabbata Ashley ta rasu ne daga wani ciwo da ba a san shi ba sosai, wato matsalar da take biyo shan ruwa da ya wuce kima.
Mutane da yawa sun taso ana fadar alfanun shan ruwa a kai a kai, "akwai wani abu da ake kira over-hydration wato ruwa ya yi wa mutum yawa a jiki," kamar yadda Shugaban Bangaren Ruwa da Tsaftar Muhalli a Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Bruce Gordon, ya bayyana wa TRT Afrika.
Idan ruwa ya yi yawan da ya wuce kima a jiki yana sirka sinadarin electrolytes da ke cikin jini kuma hakan zai sa ruwa ya shiga cikin kwayoyin halitta, wanda hakan zai sa su su kumbara.
Idan wannan ya faru da kwayoyin halittar da ke cikin kwakwalwa, to hakan zai zama hadari kuma zai iya barazana ga rayuwa.
"Ilimin kimiyyar halittun jiki (Biochemistry) ya ce abin da ke faruwa shi ne ruwa yana sauya wuri a jiki. Saboda haka kwayoyin halittar suna da adadin electrolytes mai yawa, kamar yadda ake da shi a cikin jini.
Idan electrolytes suka fita daga gurbinsu, to jiki yana kokarin daidaita su, wanda hakan zai sa ruwa ya shiga cikin kwayoyin halittar," kamar yadda Gordon ya yi bayani.
Sinadarin Sodium yana taimaka wa jiki wajen daidaita ruwan jiki da kuma ciki da wajen kwayoyin halitta. Lokacin da sinadarin Sodium ya yi kasa saboda shan ruwa fiye da kima, ruwan jiki ya shiga cikin kwayoyin halitta daga waje. Likitoci suna kiran wannan yanayi "hyponatremia".
"Hakan yana faruwa, amma ba sosai," in ji Gordon, inda ya ce ya kamata mutane su sani ya dace su kiyaye fada wa hadarin.
Ya yi kama da karancin ruwa
Masana sun ce alamomin matsalar shan ruwa fiye da kima suna kama da matsalar karancin ruwa a jiki, wanda hakan yake da wahalar ganewa.
Mutum zai iya jin ciwon kai ko kuma jiri ko kuma hararwa – wadannan duka alamomin matsalolin biyu ne. Wannan ba zai iya fitowa karara ba. Tambayar da take da muhimmanci ita ce, "Shin na sha ruwa da ya wuce kima? Shin mene ne launin fitsarina? Shin ina jin kishirwa?"
Idan launin fitsari ya zama fari tas, to hakan yana nuna ruwa ya fara yawa a jiki. Kodayake masana kimiyya sun ce sauraron jikinka zai sa ka fahimci adadin ruwan da ya wuce kima ga jiki.
"Ba na jin abu ne mai wahala saboda muna jin kishirwa. Hakan yana sa muna iya daidaita bukatarmu ta ruwa da kuma samar da adadin da ya dace ga jiki na sinadarin electrolytes da kuma cikin jini," in ji Gordon.
Wane adadin ruwa ne zai zama matsala ga jiki?
Masana sun ce har yanzu babu wani adadin ruwa da za a ce tsaka-tsaki ne da jiki yake bukata.
"Babu wani bincike da ya nuna kada a wuce wani adadi ko kuma kada ya gaza kai wa wani adadi. Idan ka tuna, kananan yara ko jarirai suna bukatar ruwa kadan saboda jikinsu karami ne.
"Idan ba ka kazar-kazar, za ka yi amfani da ruwa kadan ne, idan kuma yanayi ya yi sanyi, za ka yi amfani da ruwa kadan ne shi ma," in ji Gordon.
Ya danganta hatta a wurare masu tsananin zafi, bai kamata matsakaicin mutum ya sha ruwa da ya wuce lita daya da rabi a sa'a daya ba.
Shan isasshen ruwa ya danganta daga mutum zuwa mutum kuma hakan ya kan dogara ne a kan yanayi da aikace-aikacen mutum da kuma shekarunsa.
"Sannan, kada ka manta cewa kana samun kaso 80 cikin 100 na ruwan da kake bukata daga abinci da abinsha. Gaba daya, lita biyu zuwa uku sun ishe ka a kowace rana," in ji Gordon.
Mutane suna fitar da ruwan jikinsu ta hanyar motsa jiki da shayarwa (ga mata masu goyo) da kuma a yanayin tsananin zafi da sauransu.
"Yana da muhimmanci ka rika shan ruwa yayin da ake tsananin zafi, amma kuma kada ka tsorata ka sha ruwan da ya wuce misali," kamar yadda Gordon ya yi gargadi.
Ya kuma ja hankalin mutane da kasa su rika shan ruwa da ya wuce misali, inda ya ce hakan zai iya zama matsalar idan ba a kula ba.
"Gaske ne bincike ya tabbatar da cewa shan ruwa ya taimaka wajen aikin zuciya da koda. Saboda da haka akwai dalili mai karfi kan muhimmancin shan ruwa. Amma kuma ba daidai ba ne mutum ya tasa galan din ruwa a gaba yana sha ba kakkautawa, kamar dai komai a rayuwa nan — ana so mutum ya tsaya tsaka-tsaki."
Kodayake yana da wuya samun alkaluman mutanen da suka mutu sanadiyyar shan ruwa da ya wuce kima, ana samun bayanai ne daga fagen wasanni da gasar shan ruwa.
Amma Hukumar WHO ta fi mayar da hankali kan matsalar rashin samun tsaftataccen ruwa da tsaftar muhalli, wanda yake sanadin mutuwar mutum miliyan 1.4 a duk shekara.
"A wajenmu a WHO, manyan batutuwan kiwon lafiya sun dogara ne kan electrolytes suna da alaka da karancin ruwa a jiki bayan fama da ciwon gudawa. Nan ainihin matsalar take," in ji Gordon.
Akwai bukatar wayar da kan jama'a kan matsalar shan ruwa fiye da kima, wannan ce babbar hanyar magance matsalar. Da zarar mutane sun fara ganin alamun ruwa ya fara musu yawa a jiki, to abin da ya kamata su fara yi shi ne su tsayar da shan ruwan haka kuma su garzaya a asibiti.
"Ya kamata mutum ya ga likita saboda akwai abubuwa da za su yi wajen daidaita sinadarin electrolytes da ke cikin jini. Idan abin ya yi muni sosai kuma, za a iya ba mutum ruwan gishiri na Saline with Salts," kamar yadda Gordon ya ce.
Komai ya dogara ne kan daidaita adadin electrolytes a cikin jini. Saboda haka ya kamata mutane su rika kula da yadda suke jin kishi da adadin ruwan da suka sha da kula launin fitsarinsu don kada su fada hadari.