Marion Peake mai shekara 37-‘Yar Afirka ta Kudu wadda ta shiga Gasar Sarauniyar Kyau bayan ta sha fama da cutar kansa. Hoto: Marion

Daga

Pauline Odhiambo

Kamar wata abar kwatancen marubucin soyayya Lord Byron, ta fito cikin murna da farin ciki tana tafiyar takama domin nuna cewa kyau ya wuce abin da ake iya gani a zahiri.

Marion Peake mai shekara 37-‘Yar Afirka ta Kudu wadda ta shiga Gasar Sarauniyar Kyau bayan ta sha fama da cutar kansa- ta bude wani babi na fafutika tare da nuna wa duniya cewa duk wani yanayi, za a iya nuna kyawunsa.

“Sai na rika jin kamar ni ba mace ba ce, kamar an dan sauya min jinsi,” in ji Marion wadda aka cire wa mama a shekarar 2018.

Yanzu Marion, wadda ta shiga Gasar Sarauniyar Kyau sau uku ba ta ganin wani bambancin tsakaninta da duk mai jin kanta a matsayin kyakyawa.

Sai dai ba ko yaushe take jin hakan, domin ta tabbatar da cewa ta sha fama da kuncin rayuwa da damuwa.

Gano cutar

A lokacin da Marion take shekara 32 a rayuwa, daidai lokacin da take shirye-shiryen murnar cikar karamar ’yarta shekara daya, sai kalubale mafi girma a rayuwarta ya mata sallama.

“Sai na rika jin kamar ni ba mace ba ce, kamar an dan sauya min jinsi,” in ji Marion. Hoto: Others

Sai ta lura cewa mamarta daya ya kara girma, kuma yana zafi. Da farko ta yi tsammanin tunanin ko saboda shayarwa ce kawai. Da aka yi gwaji, sai aka gano cewa tana da cutar kansar mana, wato wani yanayi inda wasu sinadaran da ke cikin jiki yake jawo wani sashe na jikin mutum ya yi ta girma da sauri.

A gwajin da aka yi wa Marion, an gano girman tsokar ya kai kwallon wasan table tennis.

“Na tuna lokacin da na je karbo sakamakon gwajin tare da mahaifiyata, sai nake cewa, “Ba zai taba yiwu ba in samu cutar kasa,” in ji Marion, wadda take da ’ya’ya biyu, kuma take jagorantar kungiyar Helping Those In Need.”

“A lokacin da suka tabbatar min cewa ina da kansa, sai na shiga damuwa. ’Ya’yana ne suka fara faxo min a rai. Sai na fara tunanin waye zai kula da su? Waye zai share musu hawaye idan suna cikin damuwa? Na shiga rudani da tuna-tune kasancewar na yi tsammanin mutuwa zan yi.”

Kansa mai mataki ta 3

Bayan an bayyana mata cewa cutar ta riga ta yi nisa, sai nan da nan aka fara shirin tiyata, inda aka ce za a yi tiyata guda biyu domin a hana yaduwar cutar wadda ta riga ta kai mataki na uku.

Abin farin cikin shi ne ta daina jin radadi, wanda hakan yake nufin za ta cigaba da harkokinta kwanaki kadan bayan tiyatar.

Shi kansa cigaba da shan maganin wani kalubale ne na daban ga Marion. Hoto: Marion

“An min tiyatar ce a ranar 5 ga Yuni, sannan aka sallame ni daga asibiti a ranar 8 ga Yuni. Washegari bayan an sallame ni, na ciyar da yara 250 duk da a lokacin ma ciko ne a kirjina,” in ji Marion, wadda yanzu haka take kula da yara mata 33.

“A lokacin wasu gani suke yi kamar ba ni da hankali, amma ni tunanina shi ne yadda zan ji dadin rayuwata.”

Cigaba da rayuwa

An dora Marion a kan maganin rage sinadaran da suke jawo kansa da za ta cigaba da sha har tsawon rayuwarta, wanda hakan ke nufin za ta rika shan kwayoyin magani kullum har karshen rayuwarta.

Shi kansa cigaba da shan maganin wani kalubale ne na daban.

“Sai na kara kiba sosai har ya kasance ina kai kilogram 104. Sai na zama mummuna, na shiga damuwa da kunci,” in ji ta.

Samun kwarin gwiwa

Domin kar ta bari rayuwarta ta susuce, sai Marion ta fara atisaye. “A lokacin burina kawai in samu kwarin gwiwa, in yarda da kaina, yadda zan iya kallon madubi in ce nima kyakkyawa ce,” in ji ta.

“Sai na fara cin abinci masu kyau da suke gina jiki, sannan na fara zuwa aitsaye, wanda hakan ya inganta min lafiyata. Sai na fara samu karfin gwiwa.”

A cikin ’yan watanni, sai Marion ta zubar da kilogram 42, sannan ta samu kwarin gwiwar shiga Gasar Sarauniyar Kyau.

“Rayuwa da manufa tana kara kwarin gwiwar cigaba da rayuwa mai kyau,” in ji Marion.

“Da lafiyata ta inganta sosai, sai na ga akwai bukatar in wayar da kan sauran mata irina da suke shiga kunci saboda yanayin surar jikinsu. Wannan ne ya sa na shiga Gasar Sarauniyar Kyau ta Afirka ta Kudu a bara,” in ji ta.

Yanzu haka ta kai karshen gasar, inda take da burin ganin ta lashe. Idan ta lashe gasar, za ta zama mace ta farko mai cutar kansar mama da ta taba lashe gasar a duniya.

“Ina tunanin nasarata za ta aika sako muhimmi na karfafa gwiwa ga mata domin su fito su yi yaki da duk wata kalubale da suke fusntanka a rayuwa. A duk wani yanayi da kike ciki, akwai yadda zai miki kyau,” in ji ta.

Cigaba da gwagwarmaya

Duk da cewa za a kara yi wa Marion wata tiyatar domin cire mata mahaifa-Tiyatar da ake tunanin za ta daidaita sinadaran da ke jikinta- ta bayyana cewa babu matsala domin za ta cigaba da zama uwa ga ’ya’ya mata da suke karkashin kungiyarta.

“Ita kanta tiyatar cire mahaifar kamar an kara sauya min jinsina ne domin hakan na nufin ba zan sake haihuwa ba,” in ji ta.

Amma kasancewar tana aiki domin canja rayuwar ’ya’ya mata da aka taba cin zarafinsu, da wadanda aka tsinta, sai hankalinta ya kasance a kwance.

“Rayuwa da manufa tana kara kwarin gwiwar cigaba da rayuwa mai kyau,” in ji Marion.

TRT Afrika