An ajiye kayayyaki daban-daban na aiki da ‘yan sama jannatin ka iya bukatar amfani da su a kan jar kasar da ke shimfide a wajen / Hoto:  (AFP)

Kananan dakuna hudu da wajen motsa jiki da jar kasa mai yawa – NASA ta kaddamar da sabon wajen da ta gina don kwaikwayon yadda rayuwa take a Duniyar Mars, inda wasu mutane suka amince su zauna a ciki har tsawon shekara daya.

Mutanen za su zauna ne don gwada yadda rayuwa za ta iya kasancewa idan aka samu damar sauka a Mars din wacce ke makwabtaka da duniyarmu ta Earth a nan gaba.

An kirkiri wajen ne, wanda aka kaddamar da shi a ranar Talata don gudanar da wasu gwaje-gwaje uku da aka sa wa suna “The Crew Health and Performance Exploration Analog (CHAPEA).”

Ginin yana nan a cikin katafariyar cibiyar bincike ta Hukumar Sararin Samaniyar Amurkan da ke Houston, a Jihar Texas.

Mutum hudu da suka amince su yi gwajin za su fara a wannan bazarar mai zuwa, lokacin da NASA ke shirin sa ido da bin diddigin yanayin lafiyar jikinsu da ta kwakwalwarsu don fahimtar irin tsawon lokacin da dan adam zai iya jure zama a kadaice.

Mutanen za su yi amfani da injin tafiya a kansa don dai gwada yadda tsarin jar duniyar marar karfin maganadisun kasa yake / Hoto: (AFP)

Bayanan da za a tattara za su taimaka wa NASA fahimtar yadda za a yi amfani da ‘yan sama jannati da kyau a Duniyar Mars, in ji Grace Douglas, jagorar masu bincike a shirin na CHAPEA.

“Za mu fara fahimtar yadda za mu taimaka musu da irin abin da za mu samar musu. Kuma hakan zai kasance bayani mai muhimmanci sosai wajen daukar matakai kan abubuwan da za a mu yi amfani da su,” ta fada a lokacin da take zagaya wa da ‘yan jarida a wajen.

Irin wannan kuduri na dogon lokaci kan zo da “tarin iyakoki masu tsauri,” ta kara da cewa.

Akwai wurare daban-daban na gudanar da aiki a cikin ginin / Hoto: (AFP)

“Mutanen za su zauna a cikin ginin mai girman sikwaya mita 1,700 da aka sa wa suna "Mars Dune Alpha," wanda ke dauke da ban daki biyu da karamin lambu na shuka latas da dakin da aka ware na kula da lafiya da wajen hutawa da kuma wuraren gudanar da aiki da dama.

Sannan akwai wani dan daki da ke tsakanin ginin da waje da iska ke ratsawa da aka kwaikwayi yadda duniyar Mars take duk da cewa dai shi ma duk a cikin ainihin ginin yake.

An ajiye kayayyaki daban-daban na aiki da ‘yan sama jannatin ka iya bukatar amfani da su a kan jar kasar da ke shimfide a wajen, ciki har da wajen auna yanayi, da injin yin jan bulo da kuma wani rufaffen ginin gilashi da za a iya shuka tsirrai.

Kazalika akwai injin motsa jiki da ake tafiya a kai da ‘yan sama jannatin da suka amince su zauna a wajen za su dinga tafiya a kansa don dai gwada yadda tsarin jar duniyar marar karfin maganadisun kasa, yake.

“Ba zai yiwu a ce kawai mun ajiye su suna ta tafiya ta zagaye ba har tsawon sa’a shida,” Suzanne Bell shugabar sashen kula da lafiya ta hukumar NASA ta fada cikin raha.

Mutum hudu za su dinga amfani da injin tafiyar don gwada yadda doguwar tafiya da za a dinga tattaro samfur-samfur na abubuwa za ta kasance.

Wannan falo ne da wajen cin abinci da mutanen za su iya zama / Hoto: (AFP)

Har yanzu ba a bayyana sunayen mutanen da za su kasance a tawagar farko ta aiwatar da wannan gwaji ba tukunna, amma hukumar ta ce “za a bi ainihin tsarin NASA ne na yadda take zaben ‘yan sama jannatin da suka nemi aiki,” inda za a yi matukar la’akari da gogewar mutum a fannonin kimiyya da fasaha da injiniya da lissafi.

Masu bincike za su dinga gwada martanin mutanen a yayin da suke cikin yanayi na gajiya ko wahala, kamar takaita samun ruwa ko lalacewar wasu kayan aiki.

Sannan kuma an samar da wani muhimmin tsarin, na fasahar 3D a wajen.

A yanzu NASA tana matakin farko ne na shirin zuwa Duniyar Mars, duk da cewa yawanci abin da hukumar ta fi mayar da hankali a kai shi ne shirin zuwa Duniyar Wata na Artemis da ake yi, wanda ke burin ganin dan adam ya sake zuwa Wata a karon farko bayan shekara 50.

An kuma samar da fasahar 3D a wajen /Hoto: (AFP)
TRT World