Tsiron Schrenkiella parvula, wadda wani tsiro ne na rukunin “extremophyte” ta zamo mai iya rayuwa a matsanancin yanayi a muhallin da take tsirowa a gefen Tafkin Gishiri wanda ke yankin tsakiyar Anatolia na Turkiyya. / Hoto: Alper Gezeravci via X

Daga Karya Naz Balkiz

Wani gagarumin gwaji da masana kimiyyar Tukiyya suka gudanar a duniyarmu da kuma a duniyar samaniya zai iya zama silar fatan dan'adam na yin matsuguni a wasu duniyoyi.

Jigon wannan gwaji shi ne wani tsiro da ake cewa Schrenkiella parvula, wanda ke fitowa ya kuma rayu a yankin Tafkin Gishiri na Türkiye.

“Rayuwar dan'adam ta ta'allaka ne kan rayuwar tsirrai, wato iskar oxygen. Idan muna son mu kafa matsugunai a samaniya, dole sai mun kai wasu tsirrai da kuma abin da zai tallafa wa rayuwarsu,” in ji Farfesa Rengin Ozgur Uzilday, mai jagorancin binciken Turkiyya na EXTREMOPHYTE.

Ta fada wa TRT World cewa, “Domin wannan, muna bukatar tsirrai da za su iya rayuwa a yanayi irin na wajen duniyarmu”.

Karkashin shirin Artemis mission, hukumar binciken samaniya ta Amurka NASA, tana shirin gina matsugunin mutane da dogon zango kan duniyar wata. Daga nan, suna fatan “bude hanyar yin haka a duniyar Mars”.

Ozgur Uzilday ta bayyana cewa, sai dai kuma, turbayar da ke kan duniyoyin, wadda ake kira da “regolith”, gabadaya ta bambanta daga turbayar duniyarmu. Turbayar ba ta da halittu da ke rayuwa cikinta, kuma abubuwan da ta kunsa sun bambanta sosai, wanda hakan ba ya bari a rayu cikinta.

Ga misali, hawan farko na turbayar duniyar Mars tana da guda. Bayanai da aka samo daga motocin da suka je duniyoyin, turbayar tana da matsanancin yawan gishiri, da aluminium, da silicon, da magnesium, wadda ta kunshi sauran sinadarai da suka hada da chromium da boron.

A nan ne aikin masana kimiyyar Turkiyya ya zo.

Ozgur Uzilday ta ce, “Mun ba da shawarar wasu tsirrai daga wasu sassan duniya, inda muka lura akwai matsanancin yanayi, za su iya rayuwa a turbayar duniyoyin waje har su iya tsiro da shan rana."

Daya daga cikin wadannan tsirran na “extremophyte” shi ne Schrenkiella parvula, wanda yake rayuwa a matsanancin yanayi da ke duniyarmu da kuma a gefen tafkin Salt Lake da ke tsakiyar Anatolia.

Tsiron yana iya zuka da adana gishiri a kwayoyin halittunsa, kuma yana rayuwa har cikin ruwan teku, inda yake jure kafrin yawan gishiri a ruwa da ya kai millimolar 600, wanda ma;aunin gwada yawan sinadari ne a cikin abu mai ruwa.

Tsiron wanda ke jure gishiri, wanda a kimiyya yake rukunin “halophyte”, yana kuma jure wa sinadaran lithium, da chromium, da boron, da magnesium. Hakan ya sa tsiron yana iya rayuwa ciki kasa da ke da mai guba da ke cutar da yawancin tsirrai, kuma ya sa ta dace da noma a wajen duniya.

Amma ba wannan ne kadai siffofin da suke muhimmai. Wani abu da ba za a iya gwada a duniyarmu ba shi ne ko wadannan tsirrai suna iya girma ba tare da karfin maganadisun kasa ba.

Ozgur Uzilday ya ce, “Kenan, abu na farko da za mu yi shi ne mu duba ko wannan tsiro za ta iya rayuwa a waje mai karancin maganadisun kasa”.

An gudanar da wani bangare na gwajin a kan tashar sararin samaniya ta International Space Station, inda dan Turkiyya na farko da ya je sararin samaniya, Alper Gezeravci, wanda ya kwashe kwanaki 18 a can cikin watan Fabrairu na wannan shekara.

Kwatanta samaniya da duniya

Tawagar ta Ozgur Uzilday ta aika iri guda 50 zuwa dakin binciken da ke sararin samaniya, inda aka ya yafin Schrenkiella parvula kuma ta tsiro cikin yanayin gishiri, da yayi daidai da yanayin da ake tsammanin na duniyar wata ne ko na duniyar Mars.

Ta ce, “Gwajin da muka yi a tashar samaniya ta ISS ya nuna tsiron zai iya rayuwa ya girma a yanayin gishiri, kuma a inda ke da karancin maganadisun kasa, kuma har ya fito da ganye cikin yanayin na gishiri”.

Ta kara da cewa, an samu zangon girma na kwanaki takwas, a lokacin da tsirran suka fitar da ganyayensu na farko kuma suka yi saiwa. Hakan ya zarce tsammani game da kyawun yadda tsiron zai yi.

Lokacin shirin dawowarsa, Gezeravci ya girbe samfuran tsiron na Schrenkiella parvula, kuma ya adana su a ruwan magani da ya daskarar da gangar tsiron da kwayar halittarsa cikin awon zafi na -80 ma’aunin Celsius lokacin dawowar. Samfuran sun isa Jami’ar Ege ranar 29 ga Fabrairu.

Tawagar ta Ozgur Uzilday kuma ta kwatanta yin gwajin a duniyarmu don gano yadda yanayin samaniya zai yi tasiri kanta. A yanzu suna nazarin samfuran daga tashar samaniya ta ISS tare da kwatantawa da na doron duniya.

Ozgur Uzilday ta ce, “Mutane na dokin jiran mu bayyana bambancin da muka gano. Amma abin da muka fi son gani shi ne a ce ba wani sauyi. Wadannan tsirran suna rayuwa a duniya, don haka muke so mu ga irin wannan sakamako a samfuran da aka gwada a tashar ISS.

Idan an kwatanta da samfuran nan duniya, zuwa yanzu ba a ga wani babban canji ba. Wani muhimmin bambanci shi ne cewa cikin yanayin karancin magana disun kasa, tsirran sun fito da saiwoyi a wani yanayin na daban.

Ozgur Uzilday ta yi bayanin cewa, “A duniyarmu, idan iri ya fara fitowa, yana tura saiwarsa zuwa inda maganadisun kasa ke jan sa kasa, sai karansa ya tashi zuwa inda haske yake.

“Amma hakan ya sauya matuka a yadda aka gani yanayin karancin maganadisun kasa, saboda tsiron ya rasa inda zai fuskanta saboda rashin maganadisu”, cewar Ozgur Uzilday

A kwanaki masu zuwa, tawagarta za ta yi amfani da fasahar nazarin halitta don gano sinadarin DNA da RNA na samfuran daga mabambantan yanayin guda biyu, don tantancewa.

Gezeravci (dama) ya samu horo sosai kan yadda ake gudanar da kowane matakin gwajin, watanni kafin tafiyar tasu zuwa tashar ISS. A hoton kuma akwai: Rengin Ozgur Uzilday (hagu) da dan Turkiyya na biyu da zai je samaniya Tuva Cihangir Atasever (tsakiya). / Hoto: Turkish Space Agency Via X

Nau’in tsiro na farko

Idan tsiron zai iya cigaba da jurewa yanayin wajen duniya, tsiron na Schrenkiella parvula ba wai zai rayu a turbayar duniyoyin waje, amma hakan zai sauya zubinsa da kaurinsa, inda zai haifar da karin gwaggwaban yanayin da tsiro zai rayu.

Ozgur Uzilday ya ce, “Turbasar sama-sama ta duniyar wata tana da kauri matuka. Tsirran da muke ci ba za su iya yin saiwa cikinta ba. Haka nan kuma, turbayar ba ta rike ruwa kamar yadda kasarmu take.”

Wannan ne babban kalubale ga noma a samaniya, musamman ganin wahalar ruwa a sauran duniyoyi. Ta bayyana cewa, “Ko dai sai mun yi safarar ruwa mai yawa daga duniya ko kuma mu samar da shi, kuma kowanne cikinsu zai yi tsada sosai”.

“Ko kuma za mu iya duba hanyoyi sauya turbayar kanta.”

Ana kallon nau’in saiwoyin tsiron da za a fara gwadawa za su iya tsinka turbayar, yadda zai saukaka wa sauran tsirrai su yi saiwa yayin da suke inganta karfinta na rike ruwa. Hakan zai rage yawan ruwan da ake bukata don noma.

Abin da zai rage shi ne kunshin sinadaran turbayar samaniya. Ba wai kawai turbayar tana da guba ba, haka nan kuma rashin sinadaran gina kasa, wanda da shi ne tsirran duniyarmu ba za sui ya rayuwa ba su ba.

Ozgur Uzilday ta fada wa TRT World cewa, “Muna ba da shawarar tsiron Schrenkiella parvula za a iya amfani da shi a matsayin shukar ciko a turbayar don shirya ta daidai da bukatunmu”.

Da take nuni kan karfin tsiron na shanye sinadaran da ba a so kamar gishiri, da chromium da aluminium, ta kara da cewa ana iya “girbewa da kona tsiron, don a kawar da wadannan sinadaria daga turbayar wata. Daga nan za a iya sake shuka shi kuma a rubar da shi don shirya kasar da za a yi shukar da za a ci.”

A karshe, karfin tsiron na Schrenkiella parvula wajen iya rayuwa a yanayi mai kunci, zai ba da gwarin gwiwa kan fatan fara noma a duniya samaniya, sannan ya nuna juriyar rayuwa.

Babban matakin cigaba

Ozgur Uzilday ta ayyana cewa, “An koyar da ni ilimin halittun samaniya a tsakiyar shekarun 2000, yanzu kuma ina koyarwa dalibaina. Gwaje-gwaje kan yanayin karancin maganadisun kasa a hurumin da sai dai kawau mu yi kallo”.

Lokacin da Hukumar Binciken Samaniya ta Turkiyya ta sanar da cewa tana karbar takardun neman bincike a shirin tura mutane samaniya, nan da nan suka nemi shiga.

Ta jaddada cewa, “Muna nazarin rayuwa, da halittu, amma duka rayuwa a duniya ta dogara ne kan maganadisun kasa. Yana da muhimmanci mu nazarci ko abin da muka gano suna da wata ma’ana a yanyin karancin maganadisun kasa, don ganin yadda halittu ke canjawa a wadannan yanayin”.

Tare da hadin gwiwa da Cibiyar Binciken Kimiyya da Fasaha ta Turkiyya (TUBITAK), suna tattara bayanan duka ayyukansu don adana jigon binciken samaniya a Turkiyya nan gaba.

“Mu (masana kimiyyar Turkiyya) a yanzu mun dauki babbam matakin cigaba da binciken karan-kanmu a samaniya. … Yana da kayatarwa cewa masana kimiyya a Turkiyya suna iya tallafa wa bincike a wannan fanni.”

TRT Afrika