Daga Firmain Eric Mbadinga
Manyan kwandunan ƙona shara da aka samar na ƙara yawa a dukkan yankunan Burkina Faso, inda ake da kalubalen raba muhallai da robobi.
An samar da wadannan kwanduna a lokacin da ake da buƙatar su - sun zo a lokacin da Ƙasashen Yammacin Afirka suke da ƙarancin manyan kwandunan ƙona shara don rabuwa da robobi da tarkacen kayan magunguna da aka tara a lokacin annobar Corona.
Amfani da takunkuman rufe fuska da yawa da sauran kayan kare kai ya janyo bayar da muhimmanci ga kwashe shara a kasar.
Wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar ya lura da cewa dattin sharar lokacin Covid-19 ya janyo kalubale ga kwashe hara a muhalli a duniya.
Rahoton ya kuma bayyana cewa sashen kula da lafiya a kasashen da ba su ci gaba ba da masu tasowa ba ya samun isassun kayayyakin da ake bukata don kawar da sharar da ake da ita.
Jean Pierre Salifou Dondassé ne ya kirkiri kwandunan "Wanbzanga" da "Gwaba", kuma tuni ma'aikatar lafiya ta amince da amfani da su wajen yaki da gurbacewar muhalli.
Ya ce bayan barkewar cutar Corona ne bukatar wadannan akwakuna ta karu a kasar.
Yadda aka fara samar da akwatunan
Asalin tun 2002 iyalin Dondasse suka nuna sha'awar samar da hanyar kwashe shara da raba ta da muhalli.
A wannan lokacin ne Jean Pierre Salifou ya zana akwatun farko tare da ba shi sunan "Gwaba" - ma'ana babbar wuta a yaren Joola.
An samar da shi da karfe, siminti, yumbu da sauran kayayyaki, inda ake da manufar sharar kayan magunguna da ta sauran kayayyakin amfanin yau da kullum.
Serge Dondasse, dan gidan JP Salifou Dondasse d aya rasu 'yan watannin baya, ya bayyana cewa "Da fari, abub babu sauki. Mun yi kokari da dama, a wasu lokutan mu karkare da rashin nasara, amma mun jure."
Bayan an kaddamar da manyan kwandunan kona sharar, sai suka fara samun yabo da karbuwa, suna samun nasarar lashe kambi da yawa.
An bawa kwandunan kambin Shugaban Kasar Burkina Faso a wajen Taron Binciken masana Kimiyya da Fasahar Kere-Kere (FRSIT), da kuma kambin kirkirar sabon abu a Afirka na Thomas Sankara, in ji Serge Dondasse yayin tattaunawa da TRT Afirka.
Nasarar wannan aiki ne ya ba su karfin gwiwar samar da kwandon shara na biyu a 2016 da aka baiwa sunan "Wanbzanga" - ma'ana mai cinye komai, a yaren Moore.
Ya fi girma, kuma yana da wurin zuba shara guda biyu, ba kamar na farko ba, hakan ya sanya shi zama mafi dacewa ga manyan cibiyoyin kula da lafiya.
"Babban abu ne da aka samar, madalla ga gudunmowar kwararru da kuma Kungiyar Masu Basira ta Afirka (OAPI).
Ana amfani da shi wajen kone sharar kayan magungunan Covid-19, inda muka ajje shi a cibiyar magance cutar," in ji JP Salifou Dondasse yayin tattaunawa da 'yan jaridu..
Ya kara da cewa "Muna kuma amfani da su wajen kone kayan kula da lafiya daga sauran bangarorin Bobo-Dioylasso. An samar da su da kayan cikin gida."
Kyaututtukan da suka lashe
A 2016 ne aka kaddamar da akwaku na byu, wanda shi ma ya lashe kambin Shugaban KAsar Burkina Faso a wajen Taron Binciken Masana Kimiyya da Fasahar Kere-Kere (FRSIT) da kuma kambin kirkirar sabon abu a Afirka na Thomas Sankara,
Ko a Ouagadougou, ko kuma Bobo-Dioulasso - babban birnin kasuwanci na kasar - wuraren kula da kiwon lafiya na dogara kan akwatunan kone shara don rabuwa da dattin kayan magunguna.
Serge Dondasse, da ke da shekaru talatin da wani abu, ya karbi ragamar wannan kasuwanci bayan rasuwar mahaifinsa. Yana kuma yin aikin kula da kwandunan bayan sayar da su.
Serge Dondasse ya bayyana cewa "Ba kamar kwandunan da ake shigo da su daga kasashen waje ba, namu ba sa daukar tsawon lokaci wajen gyara su bayan sun lalace, saboda muna nan, muna gyara su da kan mu.
"Kuma yadda aka samar da su daga kayan cikin gida, ba ma shan wahalar gyaran su."
Serge Dondassé ya ci gaba da cewa "Ya zuwa yau, 'Wanbzanga' da 'Gwaba' da ake tattarawa d akona shara a cikin su na nan a sassa da dama na kasar.
"Ga manyan cikinsu, mun jibge sama da 15, kananan kuma ana da sama da 300 a fadin kasar."