Daga Coletta Wanjohi
Har yanzu Sudan na ci gaba da fama da mummunan tashin hankali sakamakon rikicin da ke tsakanin manyan janar-janar din soji biyu masu gaba da juna, duk kuwa da kokarin ganin an samar da yarjejeniyar tsagaita wuta.
Duk wasu yunkuri na ganin an kawo karshen zubar da jini a kasar na kara dusashewa la'akari da yadda dakarun sojin Sudan din ke kauracewa dut wata tattaunawa da dakarun soji ta RSF.
A ranar Laraba, rundunar sojin kasar ta ce ba za ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Amurka da Saudiyya ke son a yi ba, saboda kungiyar RSF ba ta mutunta yarjejeniyar ba, batun da ita ma RSF din ta zargi sojin kasar da yi.
Wannan sabon al'amari dai ya dada sanya fargaba ga zaman lafiya da ake fatan gani a Sudan.
Yakin, na neman mulki a kasa ta uku mafi girma a nahiyar Afirka, ya fara ne a ranar 15 ga Afrilu inda ya yi sanadin kashe mutum sama da 800, tare da raba sama da mutum miliyan 1.4 daga matsuguninsu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Ma'aikatar lafiya ta Sudan ta ce baya ga daruruwan mutane da suka mutu, kimanin mutum 5,500 ne suka jikkata a fadin kasar kawo yanzu.
Rikicin da ya haifar da mummunan yaki tsakanin dakarun sojin biyu a Sudan, ya kawo cikas ga shirin kasar na komawa mulkin farar hula da ake sa ran yi a shekarar 2024.
Yiwuwar samar da zaman lafiya zai yi wuya
Shugabannin Sojin Sudan da na RSF sun rike manyan mukamai a majalisar mulkin kasar tun bayan hambarar da tsohon Shugaba Omar al-Bashir daga karagar mulki bayan wani bore da aka yi a shekarar 2019.
Sun yi juyin mulki a shekarar 2021 a lokacin da ake shirin mika jagorancin majalisar ga farar hula, inda shugaban sojin Abdel Fatah al Burhan zai jagoranci gwamnatin, yayin da babban kwamandan RSF Mohammed Hamdan Dagalo a matsayin mataimakinsa.
Amma daga baya manyan Janar din sai suka bata, saboda kokarin mulkar soji da kum sake fasalin RSF don shigar da su cikin rundunar sojin Sudan, a karkashin shirin mika mulki; kuma bayan makonni na zaman dar-dar, sai yaki ya barke a watan Afrilu.
"Kashi 20 na sassan kula da lafiya ne suke aiki a Khartoum, wanda ke nuni da wargajewar bangaren da aka fi bukatarsa a yanzu haka," in ji Alfonso Verdu Perez, shugaban tawagar ICRC a Sudan.
Wadanda suka iya guduwa daga kasar na neman mafaka a kasashe makotan Sudan irin su Sudan ta Kudu da Chadi da Masar ko Ethiopia, saboda tsoron barkewar mummunan rikici a yankin. Dubban mutane ne gwanatocin kasashe suka kwashe daga Sudan.
Har yanzu Janaral Abdulfatah Al-Burhan da ke jagorantar sojojin Sudan da Janar Mohamed Hamdan Dagalo mai jagorantar mayakan RSF ba su dakatar da rikici ba, duk da yawan sanar da tsagaita wuta da suke yi.
Akalla an sanar da tsagaita wuta sau 10 tsakanin bangarorin biyu da ke rikici da juna da manufar bayar da damar kai kayan agaji ga mutane.
Ba a girmama dukkan wadannan yarjeniyoyi ba duk da sanya hannu da bangarorin suka yi.
Wadanda suka dinga kai ruwa rana don ganin an tsagaita wuta sun hada da Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka da Kungiyar Gabashin Afirka da kuma na baya-bayan nan Amurka da Saudiyya.
A ranar 16 ga Afrilu ne kwana guda bayan fara rikicin aka sanar da yunkurin tsagaita wuta na farko.
Babu masu tsayawa bangarorin
“Matukar manyan Janar na sojan biyu za su samu dama, to su ba abin da ya dame su ba ne su dakatar da yakin.”
Tsohon mataimakin Ministan Harkokin Wajen Amurka mai kula da harkokin Afirka Tibor Nagy ya fada wa TRT Afirka cewa "Kasashen duniya ba za su iya yin komai ba har sai mutanen biyu sun shirya.".
“Idan ana son tsagaita wutar da gaske, to dole a samu wadanda da za su tsaya kan wadanda suka sanya hannu tare a tabbatar da sun yi aiki da yarjejeniyar," in ji Dr. Edward Githua, kwararre kan harkokin kasa da kasa.
A ranar 20 ga Mayu, a birnin Jeddah, Saudiyya da Amurka sun jagoranci sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta ta gajeren lokaci tsakanin bangarorin da ke yaki da juna.
Wannan yarjejeniya ba kamar ta farko ba, tana da tsarin sanya idanu da bin diddigi, amma kuma yaki ya sake barkewa a kwanaki bakwai bayan sanya hannu a kai. Amma masu shiga tsakanin ba su gajiya ba.
A ranar 30 ga Mayu, an sanar da kara wa'adin yarjejeniyar tsagaita wutar ta kwana biyar. masu shiga tsakani sun tabbatar da an yi aiki da yarjejeniyar yadda ya kamata, amma kara wa'adin zai taimaka wajen kai taimakon jin kai."
Amma har yanzu ana samun labaran barkewar rikici, sojojin sun sanar da za su fita daga yarjejeniyar..
Haka zalika game da batun fita daga yarjejeniyar tsagaita wutar, Sojojin Sudan sun bukaci Wakiln Sakatare na Majalisar Dinkin Duniya Volker Perthes wanda ya taba jagorantar wani babban aikin MDD a Sudan.
Shugaban sojojin Janar Abdulfatah Al Burhan ya zargi wakilin na MDD da rura wutar rikicin, amma kuma Majalisar ta fito ta musanta wannan zargi.
Masu goyon baya daga waje?
Wasu masu nazari na cewa a lokacin da kasashen duniya ke kira da rokon a tsagaita wuta sai abun ya zama kamar kara zuga bangarorin ake yi, watakila daukar tsauraran matakai zai taimaka.
“Githua ya gaya wa TRT Afrika cewa "Takunkumi na daya daga hanyoyin da za su iya tankwara wadannan mutane su dakatar da rikicin, saboda idan ba ka nemi inda suke da rauni ka kassara su ta nan ba, to za su ci gaba da fadan ne", Githua ya shaida wa TRT Afirka.
Amma kuma Nibor Nagy na jin kamar takunkumin ma ba za ta yi tasiri ba, inda ya kara da cewa "matsalar ita ce za ka iya saka takunkumai da yawa, amma wanne tasiri hakan zai yi idan suna da kudadensu na dala da zinare."
Tarayyar Afirka ta matsa kan lallai 'yan Afirka ne za su jagoranci wanzar da zaman lafiya a Sudan, musamman ma jama'ar Sudan da kansu.
Kungiyar nahiyar ta yi watsi da duk wani yunkuri na tsoma hannu a rikicin daga kasashen waje. Mai nazari Edward Githua na da yakinin cewa akwai wasu 'manyan kasashe' da ke goyon bayan bangarorin daban-daban da ke rikici.
Githua ya ce "Idan za mu samu damar ganin wadannan masu goya baya na kasashen waje sun janye taimakon da suke bayarwa, watakila a samu damar samun tsagaita wutar".
Duk da kalubalen da ake fuskanta karara, ana ci gaba da kokarin neman mafita tare da Tarayyar Afirka, Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin yankin daban-daban.
Fuskoki da dama
Hukumar Tarayyar Afirka ta ce shugabanta Moussa Faki Mahamat zai aika da jakadu zuwa kasashen da ke makotaka da Sudan a wani bangare na kokarinsa wajen neman mafita ta bai daya a rikicin na Sudan mai fuskoki daban-daban.
Daukar matakin hada hannu waje guda na da muhimmanci, saboda yawaitar masu shiga tsakani ba zai fa'idantar da abubuwan da al'ummar Sudan suke so gaba daya ba" in ji Dr. Workeneh Gebeyehu, Sakataren Zartarwa na yankin kasashen IGAD.
Duba da yadda ba a hango kawo karshen rikicin Sudan, akwai tsoro da fargaba kan yadda al'amura ke kara rincabewa a kasar - wasu na cewa ya kamata a kawar da yiwuwar fadawa yakin basasa.
Makonni biyu kawai bayan fara rikicin, tsohon Firaministan kasar Abdallah Hamdok ya yi gargadin cewa "Allah Ya kiyaye kar Sudan ta fada yakin basasar da zai mamaye yankin baki daya...Ina tunanin hakan zai zama babban jafa'i ga duniya.”
Hamdok, da sojojin biyu da ke yakar juna suka sauke daga kan mulki ya ce ya kamata a dakatar da rikicin nan da nan, saboda ba shi da kachaniya da yawa.’’